Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE KWALLIYA DA GANYEN ‘ALOE VERA’

YADDA AKE KWALLIYA DA GANYEN ‘ALOE VERA’

YADDA AKE KWALLIYA DA GANYEN ‘ALOE VERA’

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu kuraje. Wannan ganyen na dauke ne da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sanya fuska sheki da gyaran jiki da dai sauransu. Son haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai. Ina so masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda daya daga ciki nake so arika amfani dashi. Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar kuraje.


·              Kodewar fuska; yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baka ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rika shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.

·              Yankwashewar fata; wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a hada da ruwar ‘rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.

·              Domin fuska mai yawan gumi/maiko; a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a daura a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.

·              Domin gautsin fata; a markada dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe bera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.

·              Gyaran gashi; a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a hada da man zaitun a kwaba su kwabu sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . yin hakan na sanya bakin gashi da kuma dada ma gashin tsawo da karfi.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive