Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za a magance tabo koh kurajen fuska

Yadda za a magance tabo koh kurajen fuska cikin sauki




Assalamu Alaikum

Matsalar kuraje da tabon fuska sun  shafi bangaren matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar.magance.kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa. Rashin bacewar tabo a fuska na bata. kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon. Da yawan mutane sun gwada.mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.

 daga Duniyar fasaha A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a.san cewa daya za.a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.

1- A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.

2- Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan yana.hana su sake fitowa.

3- A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

4- a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

5- A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.






Insha Allah za,a dace

in kasamu wannan post da ban sha,awa taimaka ka turawa yan uwa da abokan arziki dan su karu.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

4 comments:

  1. Masha Allah. Allah ya kara tamaikawa Abbagana zan gwada na gani

    ReplyDelete
  2. Godiya ta tabbata ga Allah tsira da amincin allah su kara haihawa ga annabin mu muhammad s a w ,kuma kai ina ma addu,a allah yakara basira da budi al,amuranka na taimakawa al,umma musulmai

    ReplyDelete

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive