Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda ake shiga account wato login a blogger

Yadda ake shiga account wato login a blogger

Yadda ake shiga account wato login a blogger


Kasancewar kana da account a blogger yakan baka damar rubuta ko saka abubuwa da dama kama daga wanda zai amfani mutane, tallata haja kodai maka mancin hakan. Sau dayawa mutane sukanyi korafin cewa basu san yadda zasu k’oma account dinsu ba; wasun kuma suna cewa kamfanin google bata bada damar komawa account da aka bude ba.

Koma dai me ka dauka ko kuma kake I’krarin cewa gaskiyar maganar anan shine yadda zakayi login a account naka na blogger ya banbanta da yadda kake shiga account naka na facebook da kuma twitter domin kuwa su kamfanin google suna aiki ne bisa wani tsari domin ingan ta tsaro ta yadda ba wanda zai samu damar shiga account naka na blogger ko kuma lalata maka ita face yana da email addreshin ka sannan kuma yana da numbobin sirri na wannan email din.

Sabida indai kana so ka koma account naka na blogger dole sai ka fara shiga email addreshinka na gmail ka sanya number sirri sannan hakan zai baka damar shiga shafinka. abinda nake so a gane anan shine wannan ba lallai bane ko wani sa’in sai ka yinga login kafin ka shiga ba a’a shima yana da ma’adanar ajiye bayanai da ka sanya na email addreshinka da kuma number sirrin ka face dai ka canza wayar ko kuma ta samu matsala ka goge dukkan ma’adanar da suke ciki indai wani daga cikin hakan ya faru ko makamancin haka to dole ne sai ka sake login da abubuwan da ake bukata.   

Cikakkiyar hanya da za’a bi wajen shiga account na blooger

Abu na farko da za’a fara yi anan shine ziyartar shafin gmail wato www.gmail.com tare da sanya email addreshi da kuma number sirrin bayan an kammala haka sai a ziyarci addreshin blogger wato www.blogger.com ko kuma www.blogspot.com duk wanda aka sanya daga cikin biyun nan zai kai mutum izuwa waje guda ne da zarar na’urar ya karanci wayarka ya tabbar cewa an shiga gmail account to zai kaika izuwa shafi admin dashboard inda ake gudanar da ayyukan shafi.Hanya ta biyu 

Idan kuma ana so a shiga ta hanya mai sauki za’a iya ziyartar shafin blogger wato www.blogger.com ko kuma www.blogspot.com duk wanda mutum ya sanya daga cikin biyun nan zai kaisa izuwa waje guda ne a can sama wajen hannunka na dama za’a ga inda aka sanya “SIGN IN” a rubuce wanda ake nufin shiga sai a latsa kai muddin anyi hakan zai kai mutum izuwa ga shafin gmail inda za’a bukaci email addreshinsa sai a sanya tare da latsa kan “NEXT” daga bisani kuma zai sake tambayar number sirri sai a basa tare da latsa ma bullin “SIGN IN” mudding an sanya abubuwan da ake bukata daidai zai mutum izuwa ga shafin admin dashboard wato inda dai za’a gudanar da ayyukan shafin.

Yadda ake shiga account wato login a blogger


Sannan duk sain da ake son a dawo dashboard na admin inda ake gudanar da ayyukann shafin za’a je izuwa ga addreshin blogger ne wato www.blogger.com ba tare da sake bin matakan dana gabatar ba face an goge wayar, anyi sabon waya ko kuma ana son shiga da wata wayar shine ya zama dole a sake bin matakan.

Abun kula: Misali ina da email addreshi guda biyu [email protected] da kuma [email protected] sai na bude blogger da [email protected] duk sa’in da nake so na shiga shafina na blogger dole sai na shiga da email addreshin dana bude ba wai dan ina da guda biyu ko fiye da hakan na rudi kaina da cewar zan iya shiga da kowannene wannan ba gaskiya bace sam dole sai da shi wancan dana buden kawai zaiyi aiki saidai in kuma ina son na sake bude wani.


Wannan shine halaccecciyar hanya da ake bi wajen shiga account na blogger ku kasance tare da Duniyar Fasaha domin samun ingatacciyar dabaru daga bangare daban daban; naku a koda yaushe Jikan marubuta kuma sharifin zamani ‘Muhammad Abba Gana’.   

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito

Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito

Idan har an yi rajistar samun katin kasa na dan wasu tsawon lokuta sannan ba’a san ranar da za’a karba katin ba, ko kuma an sha zuwa offishinsu tambayar ko ya matsayin wannan kati yake amma kuma haka zalika ba’a ji sabon labari ba, wata kila kuma an gaji da ziyartar offishinsu har an cire tsanmani. hukumar NIMC a yanzu ta samar da shafin duba matsayin katin ta yanar gizo wanda zai bada damar sanin cewa ko katin ya fito ko dai har yanzu da saura. Ga cikakkaiyar hanyoyin da mutum zai bi ya duba matsayin katin sa na kasa a yanar gizo.

1.==> Abu na farko dai shine, mutum zai ziyarci shafin NIMC a yanar gizo a wannan addreshin: https://touch.nimc.gov.ng/

2.==> Idan an shiga sai a danna mabullin ‘proceed button’ wadda ma’anar sa karasa zuwa gaba3.==> Daga nan sai mutum ya cika wurin ababen da ake bukata na sunayen sa, wanda akwai wurin cika suna na farko kafin sunan karshen wato sunan uba, sai kuma ya saka lambobi na katin kasa da aka ba shi (yana jikin katin da aka bayar).4.==> Da mutum ya cike wadannan abubuwa da ake bukata sai ya danna mabullin ‘check now button’. Bayan an danna sai a jira na dan wasu daki kai, yana gama dubawa za’a nuna ma mutum matsayin katin sa. Ya fito ko kuma dai yana hanyar fitowa.


Allah yasa ayi sa’a

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Shaukin so

Shaukin so

Shaukin so

Yadda bege yake, to kusan haka shima shauki yake, sai dai kuma ba daya suke ba, kowanne yanada da nasa tsarin.

Shi shauki shine mutum ya dinga jin wani irin farin ciki da annushuwa, da wani yanayi mai faranta rai a duk lokacin da yaga, ko yaji muryar masoyinsa.
Shauki, wani nau’ine a cikin so da ke haifar da farin ciki ga masoya, wanda ke wanzuwa tamkar daddadan sanyin iskar yammaci a lokacin zafin rana. Idan so ya kai so, to dole a samu wadannan abubuwa kamar haka:

·        Kauna da soyayya
·        Aminci da yarda cikin soyayya
·        Yarda da wanka ake so a cikin zuciya
·        Mallakawa wanda ake so, so zalla
·        Gaskatawa da wadda kake so a rai
·        Tabbatarwa zuciyarka soyayya zalla
·        Begen masoyiya ko masoyi
·        Shauk’in soyayya a cikin zuciya

Don haka shi shauki, masoyi ko masoyiya zasu dinga jin wani tsantsar farin ciki da annushuwa na tare da walwala da duk lokacin da suka ga junansu.

Ko kuma a duk lokacin da masoya suka ji muryoyin junansu, koda kuwa a wayar salula ne, to sai ka ga fuskokinsu sun nuna alamar farin ciki da walwala a Zahiri. A lokacin da jikin mutum yayi zafi, ba zafin rashin lafiya ba.

Ya kasance ace ana zafine, mutum na gumi, to zaka ga mutum yana bukatar ya dan samu inuwa mai sanyi ya zauna a ciki, har ma yayi barci idan yaji dadinta. Ko kuma ace mutum ya samu ruwa mai sanyi ya watsa a jikinsa don ya gusar da wannan zafin da ya addabe shi.

To kamar haka ne ga masoyin da yaga masoyinsa yake ji a cikin ransa, wani dadi ya ratsa shi har yaji ya manta da duk wata damuwa, sai farin ciki ya mamaye zuciyarsa.

§  Shauki tamkar shakar daddadan kamshi turare ne a cikin hanci
§  Shauki tamkar shakar kamshin furen fulawa ne a yayin da iskar yammaci mai dauke da ni’imtaccen yanayi ba wanzuwa a sararin duniya.
§  Shauki, tamkar dandanon zazzakar tattaciyar zuma ne a baki.
§  Shauki, wani yanayi ne mai gusar da damuwa a zukatan masoya.
§  Shauki wani bangare ne dake samar da walwala a gurin masoya
§  Shauki, wani yanayi ne wanda kan haifar da tsatsar farin ciki ga masoya.

§  Shauki, wani irin abune mai kasancewa a yayin da so ya zamo tamkar jini a jikin masoyan da suke kaunar junansu. 
Tura Zuwa:

Yadda zaki Kula da farcenki

Yadda zaki Kula da farcenki

Yadda zaki Kula da farcenki


Farce yana da amfani kwarai da gaske ta fuskar ginuwar jiki. Sai dai hakan ba zai samu ba sai idan har mun ba su kulawa ta musamman. Lafiyayyu kuma kyawawan farata su ne wadanda suke sumulsumul babu wata  gargada ko karkacewa a jikinsu. Za ki samu cewa gaba dayansu sun
zama launi guda ba tare da wani dameji na rauni ko tabo a kai ba.

Ga wadansu hanyoyi da muke ganin matukar za mu kula da bin su dakidaki, to za mu samu biyan bukata na mallakar kyawawa kuma lafiyayyun farata:

1.==> Ki guji cire farce da hakori: Ko da ya zama cewa wani abu ya taba farcenki ya yi irin dagowar nan, kada ki sa hakori ki cizge shi, domin hakan zai sa ya fita ba bisa ka’aida ba ta yadda har zai sa a tsarin farcen ya zama wani iri daban. Wato sai ki ga wani bangaren na farcen ya fi wani tsawo. A maimakon haka ki sami reza ko kuma abin yankan farce da ake kira da nail cutter ki yanke farcen da shi.

2.==> Bayan kin kammala da yanke faratanki za ki iya samun man farce ki shafe su da shi, wanda hakan shi zai sanya faratanki su rika walkiya da sheki, ba lallai sai kin sanya jan farce ba.

3.==> Ki kula da farcenki ta hanyar zuwa salun akaiakai.

4.==> Ki guji tara farce ya yi tsayi mai yawan gaske, wato akwai bukatar su zama a yanke a koyaushe.

5.==> Kada ki bari farcenki ya zama a jike koda yaushe, domin hakan zai sa ya rika kakkaryewa tun kafin ma ki kai ga yankewa. Idan ya zama za ki yi aiki da ruwa, yana da kyau ki sami irin safar hannun nan ki sa, don ta kare miki faratanki daga lalacewa.

6.==> Kada ki yi amfani da alkamashi wajen yanke farcenki, ko da farcen ya kasance mai rauni ne, balle kuma ga wanda ba shi da wata matsala.


Idan har ke mai sha’awar tara farce ce to ki tabbata cewa kina kula da su ta hanyar fitar da duk wata dauda da ke shiga cikinsu ta zauna. Idan kika kula barin dauda ta zauna cikin farce ba shi da kyawun gani a ido ma, ballantana ga lafiyar jiki.
Tura Zuwa:

Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger

Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger

Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger


Assalamu Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, a makon daya gabata nayi jawabi filla filla matakan da za’abi wajen bude blog tare da blogger a wannan karnin kuma insha Allahu zanyi bayanine yadda ake saka rubutu (posting) a shi blogger wanda hakan yakan baiwa maziyarta shafinka damar karanta wannan rubutun.   

Abu na fari da mutum zai fara anan shine shiga account dinsa domin kuwa ba yadda za’a yi mutum yasa wani rubutu a shafinsa ba tare da ya shiga account dinsa ba a rubutun daya gabata nayi jawabi dalla dalla Yadda ake shiga account wato login a blogger, sannan kuma bazai iya sa wani abu ta hanyar ziyartan shafinsa ba misali in addreshin shafina duniyanfasaha.guidetricks.com shiga wannan addreshin kawai zai bani damar karanta abinda aka sanya ne; in har mutum yana so ya saka rubutu to dole sai yabi matakan da zan zayyano.
Idan mutum yana so yayi post a shafinsa na blogger a daidai hannunsa na hagu bayan yashiga wato login a account nasa sai ya latsa inda aka rubuta Post na fari zai kaisa izuwa nan.

Za’a tatar da karamin akwati na fari ana kiransa title a turance shine inda mutum zai rubuta suna ko silar abinda yake son rubutawa misali anan sunan wannan post din “yadda ake post a blogger” sai mutum ya sanya ta a daidai wajen.

Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger


Babbar nan kuma shine wajen da za’a saka duk jawaban da ake son nunawa karkashin suna da aka sa misali duk wannan dogon surutan nawan suna cikin wannan babbar akwatinne amma shi asalin suna silar wannan rubutun na Yadda ake post a blogger yana cikin akwatin na fari ne. haka zalika mutum zai iya cope abu daga wani dandalin sadarwa kamar su whatsapp ko kuma facebook sannan yayi pesting nasa kamar yadda akeyi a wajajen da aka copo abun (ta hanyar latsawa a tsaya nayan wasu dakikai sannan na danna ma bullin “paste”). Bayan mutum ya kammala sai ya latsa ma bullin “publish” wanda ke rubuce a sama a daidai hanunsa na dama domin fitar abinda ya rubuta a shafinsa.

Yana da kyau mutum ya kula da wayannan madannan guda hudu wanda suke sama a hannun dama wato “publish”, “Save”, “Preview” da kuma “Close” akwai banbanci sosai tsakanin wayannan madannan. 

Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger


Abu na fari wato publish amfaninsa shine duk sa’in da ka latsa wannan mabullin to duk abinda ka rubuta zai fito a shafinka wanda duk ya ziyarci shafinka zai gani sannan kuma zai iya karantawa. Abu na biyu kuma a jerin madannan shine “save” amfanin wannan mabullin shine misali ina rubutu yanzu sai wani matsala ya taso wanda ya zamana dole ne na bar abinda nakeyi na je izuwa ga shi to mutum sai ya latsa wannan mabullin wanda duk sa’in da ya dawo zai sami abinda ya rubuta yadda yake sai dai akwai banbanci tsakanin sa da wanda nayi bayani a baya wato publish shi save in ka latsa sa ba zai fito a shafinka ba ma’ana ko mutum ya ziyarci shafinka bazai gani ba amma kuma kai ko wani sa’in ka dawo admin dashboard naka zaka tarar da abinda kayi saving nasa yana nan daram sai dai in ka goge (wato kai daya ne zaka iya ganin yayin da kayi saving).

Na uku kuma shine “preview” wannan mabullin amfaninsa shine zai baka damar ganin yadda abinda ka rubuta zai fito a shafinka kama daga surar rubutun da kuma tsari. Abu na karshe kuma a jerin mabullan shine “close” amfanin sa shine cirewa ko kuma koma wa baya ba tare da ya adana ba amma wasu sai’in yakan iya adanashi wato auto saving a turance sabida duk lokacin da kake rubuta wani abu a wajen abar rubutun yana adanashi sabida gugewa wata matsala irinsu daukewar wuta ko kuma daukewar layin sadawar wanda koda hakan ya faru zaka samesu yadda suke ba tare da ka sake wani sabon aiki ba.


Wannan shine takaitacciyar bayani yadda ake saka rubuta a shafin blogger. Ku kasance tare da Duniyan Fasaha domin samun ingattaciyar abubuwa wanda zasu taimakeku a harkokin yau da kullum naku a koda yaushe Jikan marubuta kuma sharifin zamani ‘Muhammad Abba Gana’.            

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Jirgin masoyane

Jirgin masoyane

Jirgin masoyane

Tare da

Muhammad Abba Gana

So yakan zamo tamkar tsiro a cikin zuciya, yayin da a gefe guda kuma yakan zamo ♥❤

So tamkar mayafin rufe ne, shi yasa ma wasu kan yi wa so lak’abi da suna marurun zuciya.

Bege shine mutum koda yaushe ya dinga tunanin wanda ransa ke so, ba wai ana nufin ya zauna koda yaushe bashi da aiki sai tunani ba. Abinda ake nufi shine, babu dai yadda za’ayi a dau lokaci ba a yi tunanin masoyiya ko masoyi ba.

Kuma akwai wasu misalai da dama wadanda suke nuna mutum yana bege, ko ya shiga cikin begen masoyinsa.

Wadannan abubuwa kuma idan mai karatu yayi Nazari akan su, zai tabbatar da hakanne, kamar yadda kila ta taba faruwa a kanshi.

Da yawa wasu kan shiga cikin soyayya su kuma samu kansu a yanayin zazzafan begen so, wanda ke haifar da yawan tunanin wanda ake so din.

Kuma a irin wannan yanayin, mutum kan shiga cikin wata yar damuwa ya zamo tamkar mara lafiya, ko wani maraya wanda yayi rashin iyaye, ko makamanciyar haka.


To a kowanne irin hali dai mutum samu kansa a cikin yanayin bege, ana so ya dinga jurewa saboda so shu’umi ne. 
Tura Zuwa:

Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’

Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’

Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’


Barkanmu da warhaka Uwargida. Kamar yadda na saba fadi cewa idan ana girka abincin Najeriya, yana da kyau a taba na wasu kasashe ba don komai ba illa wayar da kan uwargida kan sanin nau’ukan girke girke ko da Allah zai sa a ziyarci wadancan kasashe ba za a yi mamakin irin girkegirkensu. Sanin girkin wadansu akwai fa’ida na ilimantar da al’umma. Wajibi ne Uwargida ta koya wa ’ya’yanta musamman mata girki domin idan suka kware za su iya bude wata makaranta ta koya wadannan girke girken kuma hakan zai iya zamo musu sana’a a irin wannan yanayin da muka. shiga na rashin aiki a kasar nan. A yau na kawo muku girkin Turawa mai suna “sweet and sour shrimps’.

Abubuwan da za a bukata

·           ‘Shrimps’ (Ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kaji ko kifi)
·           ‘Dark soy sauce (shi ma ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kayan abinci).
·           Sukari
·           Citta
·           Cokali daya na garin tafarnuwa danya
·           Rabin kofin ruwan abarba
·           Man zaitun
·           Karas
·           Attarugu
·           ‘Peas’ (za a iya samu a kasuwa inda ake sayar da su karas)

Hadi

Bayan ‘shrimps’ din ya narke sai a tsoma a cikin ruwan ‘dark soy sauce’ sannan a saka a cikin gidan sanyi na tsawon awa uku. Bayan haka, sai a tsame daga cikin ruwan sannan a zuba sukari da garin citta da tafarnuwa da ruwan abarbar.

A dora tukunya a wuta sannan a rage wuta, sai a dora tukunya wadda ba ta cika kama girki ba (nonstick) sannan a zuba man zaitun a cikin tukunyar daga nan sai a zuba wannan ‘shrimps’ din da aka tsame a cikin man zaitun mai zafi sai a ci gaba da juyawa. Sai a dauko yankakken karas a zuba a ciki a ci gaba da juyawa har sai hadin ya nuna sannan a sauke a zuba a kwano.


Wannan irin girki ya dace da wadanda ke sha’awar rage jiki domin ba ya kara kiba.
Tura Zuwa:

Amfanin Rake Guda 9 A Jikin Dan Adam

Amfanin Rake Guda 9 A Jikin Dan Adam

Amfanin Rake Guda 9 A Jikin Dan Adam


Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu na shawarwari wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fssaha insha Allahu yau zamu dan yi jawa bine game da amfanonin rake a jiin dan Adam. A hakikanin gaskiya rake na da matukar amfani a rayuwar dan adam sosai, sannan yakan kare jiki daga cututtuka da dama, sannan yakan kare garkuwar jikin mutum daga cututtuka Zuwa yanzu dai binciken masana ya inganta amfanin rake ga rayuwar dan Adam kamar haka:

1.==> Yana kare mutum daga kamuwa da mura da ciwon daji da na sanyi.
2.==> Yana kara ma garkuwar jiki karfi.
3.==> Yana kara ruwan jiki musamman ga masu aikin karfi.
4.==> Yana taimakawa koda wajen sarrafa fitari.
5.==> Yana kara la_yar idanu, ciki, hanta da zuciya.
6.==> Yana gyara fata saboda sinadarin Glycolic Acid da ke cikinsa.
7.==> Yana kara ma hakora lafiya amman yana da kyau a kuskure baki yayin da aka gama shansa saboda cikinbaki akwai bacteria wadanda za su iya amfani da wannan zakin su haifar wa da mutum wata cutar misali (caris) ma’ana tsutsar hakori.
8.==> Baya da illa ga masu ciwon suga amman kada me zazzabin typhod da ciwon suga ya yawai ta shansa.
9.==> Rake na maganin yunwa da dai sauran muhimman abubuwa


Toh yan uwa kun dai ji abubuwan dashi rake ke karawa a lafiyar jiki sai mu kara adadin shan rake dan samun ingantacciyar lafiya. A huta lafiya.  
Tura Zuwa:

Cikakken bayani game da Google ADSENSE

Cikakken bayani game da Google ADSENSE

Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zamu tattauna ne game da abinda ake kira Google AdSense, yanda ake aiki dashi da kuma yanda ake samun kudi dashi a shafukan yanar gizo.

          Google Adsense wani shirine da babba kuma sanannen kamfanin nan na fasaha wato Google ta kirkira kuma yake karkashin kulawarta, mutum zai iya shiga wannan shirin ta hanyar yin register a shafinsu wanda zamuyi bayani dalla dalla a mako mai zuwa yadda akeyi in mai dukka ya kaimu wanda yin hakan yakan bawa mutum damar saka talla a shafinsa na yanar gizo kama daga hoto, sauti ko kuma hoto masu motsi wanda aka fi sani da video a turance. Mutum zai sami kudi a duk lokacin da wani ya danna wannan tallar ko kuma ya sami mutane da dama suka ziyarci shafinsa na yanar gizo.

Wannan shirin yana daya daga cikin manyan shafuka dake bawa mutum damar samun kudi a shafinsu na rubutun ra’ayin kai a yanar gizo a kowace kasa a fadin duniyar nan. Abun mamaki dake tattare da wannan shirin anan itace yana daga cikin hanyoyi masu sauki da mutum zai bi wajen samun makudan kudi a yanar gizo ta hanayar amfani da shafinsa. Shi wannan tallar yana zuwa ne a girma daban daban da kuma sura daban daban abinda kake bukata kawai shine zabar iya san ranka sannan sai ka cope wani dan code wanda zaka saka a shafinka dan watsa tallace tallace su cikin lumana.

Shi dai wanna shirin an yisa ne kawai wa masu rubutun ra’ayin kai a yanar gizo sannan duk wata tallace tallace tana zuwa ne daga wata shiri wanda ake masa lak’ani da Google AdWords wanda itama wata shirine da mutum zai biya kudi sannan ya saka hajarsa dan tallatawa.

Shin Yaushe kuma ya ya za’a biyani?

Indai wannan ne tambayar dake cikin ranka na tanadar maka da cikakkiyar amsa. Dan nasan ka da bala’in son kudi afuwan ba kai kadai ba kowa ma hake yake a jininsa. Google AdSense dai yana aiki ne da dalar amurka, sabida tushensu a can kasar amurka yake sannan duk lokacin da adadin kudin da ka samu ya kai koya zarce dala dari wato $100 kamfanin google zata tura maka kudin a sabon wata mai makawa misali a dadin kudina ya cika dala dari da ashirin da biyar $125 a kwanan wata shabiyar a watan satomba to bazan sami kudina ba a wannan watar sai wata mai kamawa wato daya ga watan October zasu tura min kudina zuwa cikin banki na basai lallai nan gida Nigeria ba kowace kasa kake in dai a duniyar nan take zasu turawa maka a barka; amma wasu bankuna zasu juya maka ita zuwa kudin kasar ka kamar anan Nigeria in an tura maka kudin zuwa banki ita bankin da kanta zata canza zuwa kudin kasar mu wato naira amma wannan bai zama wajibunba ya dai dan ganane da yanda ka bude account din in dai wa kasa Nigeria kawai ne to sai kudin kasar kawai zai shiga amma kuma in na duniya gaba daya yadda wasu masu kudir suke ka bude to akwai yakinin cewa kudin zata zauna a matsayinta na dala zaka kuma iya zara kowace lokaci a kuma ko ina.        

Ingantattun hanyoyi da Google AdSense ke tura kudi

1.==> Cheque: kamfanin google zasu juya kudin ka daga dallar amurka zuwa kudin kasar ka wanda zasu turo maka da cheque har cikin gida koda kuma a kauye kake sai de wannan hayar tana amfanine a kasashe arba’in 40 kawai a fadin duniyar gaba daya.

Amma kuma wannan hanyar tana da yan wasu matsaloli a tattare da ita wasu daga cikinsu sun kunshi za’a iya tura maka cheque kafin bankin ka su samar maka da kudinka zai dauki lokaci mai tsawo kuma maganar gaskiya zaka ji da jiki dan kullum ka ringa zirga zirga kenan kaine daga nan zuwa can daga sama zuwa kasa ba wai fa can samar iska nake nufi ba dan t’sanin ta karye jiya yan sama sama dai nake nufi.

Amma kuma in ka kasance dan mai son a sani ne irin abokina (wai so shi yake duk yan unguwarsu su san cewar shi fa ba karamin mutum bane dan har yan kasar waje har ita ma kamfanin google ta san da zamar shi) to wannan hanyar ita ta dace da kai amma bari na gaya muku wani abu Allah yasa kar yajini wannan abokin nawan ya ta yawo a banki dan ayi masa aikin kudin amma ina ya gaza karshe ya gaji ya bari, amma dai yata cewa mutane yayi nasarar samu bayan yace na rufa masa asiri.

2.==> Electronic Transfer: wannan dayar hanyar ce kuma ingattaciya wanda su kamfanin google zasu turo maka da kudinka ta hanyar transfer zuwa cikin bankinka ba tare da ka sha wata wahala tsiya ba ko kuma ka takura kanka kuma a ko ina a cikin fadin duniyar nan.


A wasu makonni masu zuwa insha Allahu zanyi cikkakiyar jawabin yadda ake register da yadda ake sa shi code din a shafi na blogger ko wordpress. Kada ku mata kuyi sharing na wannan post din zuwa ga yan uwanku dan su amfana.    
Tura Zuwa:

Kayan kwalliyar da ta dace da fata

Kayan kwalliyar da ta dace da fata 

Ya kamata mata su san irin kayan kwalliyar da ta dace da fatarsu saboda amfani da kayan kwalliya ko man shafawa wanda bai dace da fatar ba na kawo illa ga fatar. A yau na kawo mana shawarwari game da masu gaustin fata ko fata mai maiko da kuma mara gausti. Za a iya samun wadannan nau’ukan man a shagunan da ake sayar da kayan kwalliyar zamani.

Fata mai gautsi:

1.==> A nema ‘doubleduty’ fandesho idan za a sanya fandesho, domin maikon da ke cikin fandesho na taimakawa gautsin fata sosai.

2.==> Kada a rika sayan man da aka yi su da kayan maye domin hakan na bata fata.

3.==> Ya kamata a rika yawaita shafa man jiki akai akai.

Fata mai maiko: hakan na faruwane saboda yawan kiba ko gumi da ke jiki.

1.==> A sami ‘cleanser’ wanda ke tafiyar da datti da maikon fuska wanda kuma zai iya kashe ‘ya’yan cuta da ke haifar da kurarragen fuska.

2.==> Kada a rika amfani da man da zai canza kalar fata a kan fata mai maiko domin yin hakan na dada maikon fuska.

3.==> A sayi fandesho da hoda wanda zai tsayar da maikon fuska.

4.==> A rage yawan shafa fuska da rana saboda tafin hannunmu na dauke da na ta maikon, idan anyi hakan, kara maiko yake yi a fuska. Kuma na yawaita canza gidan filo don tsabta.

Fata mara maiko da mara gautsi: irin wannan fatar bata da gautsi da kuma maiko. Za a ganta babu kurarraji, kuma irin wannan fatar na canzawa saboda yanayin wuri;ko damina ko rani ko kuma hunturu.

1.==> Ana sayan fandesho da ake rubuta ‘normal skin’ a kanshi kamar man ‘TRUblend’da sauransu.

2.==> Za a iya shafa nau’ukan da zasu sa maiko a kan irin wannan fata da hunturu.


3.==> Kuma a zama ana tare da hoda kowani lokaci saboda idan zafi yazo za a iya shafawa domin fatar na canzawa ne saboda yanayi.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *