Na fara sana’ar hannu ne kasancewar ban sami gurbin karatu ba a makarantar gaba da sakandare ba domin zama mai dogaro da kai inji Bilkisu Isah, matashiya mai sa’ar hannu.
Bilkisu ta bayyanawa DandalinVOA haka ne a yayin da take hira da wakiliyarmu Baraka Bashir, inda ta bayyana cewa jarabawarta bata yi kyau ba hakan ne ya sa ta fi maida hankali wajen zama mai dogaro da kai.
Da take ci gaba da bayani, matashiyar ta kara da cewa tun kafin ta kammala makarantar sakandire ta fara sayar da kayan yara, don karewa kanta takaicin zaman duniya, domin kaucewa fadawa yanayin rayuwa rayuwa.
Bilkisu, ta ce bayan sana’ar hannu tana koyon dinki a yayin da take dakon samun gurbin karatun boko.
Daga karshe ta ja hankalin ‘yan uwanta matasa da su mai da hankali wajen neman nasu na kansu sannan su maida hankali wajen karatun boko domin magance matsalolin yau da kullum.
No comments:
Post a Comment