Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Kabeji mai nama

Kabeji mai nama

Kabeji mai nama

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya bamu ikon tarbiyantar da su yadda yakamata. A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama amma yawaita girka abinci iri daya na ginsan yara da kuma maigida. A kullum mutum yana son cin sabon abu. Don haka dole ne mata a dage wajen koyan nau’ukan girke-girke domin kayatar da abincin da ake dafawa a gida.

Abubuwan da ake bukata

·        Nikakken nama
·        Kabeji
·        Attarugu
·        Koren tattasai
·        Albasa
·        Magi
·        Karas
·        Kori
·        Citta
·        Tafarnuwa
·        Man gyada

Hadi

A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon mintuna biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe. A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken nama a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai ayi ta gaurayawa har sai naman ya soyu sannan a kwashe. A samu kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sannan a debo hadin nama a zuba a ciki sannan ayi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen. Sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe. Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abun karyawa.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive