Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Mahimmancin Kankana Ga Lafiyar Jiki

Mahimmancin Kankana Ga Lafiyar Jiki
Mahimmancin Kankana Ga Lafiyar Jiki

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zamu tattaunane akan muhimmancin kankana ga lafiyar jiki. Kankana kusan dukkanta ruwa ne don gwargwadon ruwan dake cikinta masana sun qiyasta ya kai 90%-99% bisa dari, sukarin da ke cikinta kuwa zai kai 8%, sannan ana samun vitamin C da vitamin B a cikinta, kamar yadda ta tattara sinadarin Sulphur, Calories, Phosphor da kuma Potassium, wani kuskure da wasu suke yi shi ne suna cire ‘ya’yan kankanan a lokacin da suke sha, ba su san cewa kamata ya yi su tauna ba, ‘ya’yan ba su da daci sai dandanon mai dadi ga Fat 43%, Sugar 16%, sai Protein 27.

==> KODA: Kankana ta kan taimaka wa koda matuka, domin ruwan da ke cikinta, kamar dai yadda aka sani takan saukake wa taruwar fitsari da fitarsa, wannan saboda tana da sinadarin Potassium wanda ya ke taimakawa wajen korar gurbataccen sinadari daga jukkunammu, sannan sinadarin yana rage yawan sinadarin Hyperuricemia a cikin jini.

==> FATAR DAN ADAM: Dangane da fatar dan adam, sananne ne cewa kankana tana da sinadarin da ya ke kare jikin dan adam daga Oxidation, don haka ne ma take iya fatattakar tsattsakar fata, da lalacewarta, takan ba wa fata kariya daga hasken rana mai cutarwa, masamman yadda take dauke da sinadarin Lycopene da Crotin wadanda suke taimakawa wajen kare jikin dan adam daga kunar ranar da take sanya cutar fata ko kuma cancer wace take samun fatar.

==> HAWAN JINI: Sai kuma mutane masu fama da mummunar bugawar jini, kankana takan taimaka musu saboda tana kunshe da sinadarai kamar su Manganese da Potassium masu aiki wajen tsara bugawar jinin, matuqar kankana ta qumshi wadannan sinadaran kenan ta dace da mutum mai fama da hawan jini ya riqe ta a matsayin qari cikin abincin da yake iya ci a kullum.

==> CIWON SUGAR: Kamar dai yadda muka fadi ne a baya cewa kankana ta qumshi sinadarin Potassium da Magnesium wadanda aikinsu shi ne taimaka wa jiki wajen tatso sinadarin Insulin wanda yake tsara wa sukari yadda zai yi aiki a cikin jini, qarancin wannan sinadari shi yake hana iya sarrafa sinadarin Glucose da mutum ya samu a jikinsa ta hanyar wasu abinci masu masifar zaqi, ko wurin wasu ‘ya’yayen bishiyar, a nan cin kankanan zai taimaka wa mai cutar ko ta ba wa wanda bai da ita wata kariya.

==> KUZARIN JIKI: Ana aiki da kankana a matsayin wata madogara ta dabi’a wace take maye makwafin wasu magunguna masu kara wa mutum kuzari a jiki da qarfi da lafiya, wadanda galibin ‘yan wasan motsa jiki su suke amfani da su, domin kankana tana da dauke da Potassium da Magnesium da kuma Vitamin B da nau’o’insa wanda shi kuma yake qara kuzarin jiki.


==> MATSALOLIN IDO: Kankana takan taimaka wa ido wajen kare ganin mutum, don tana dauke da Vitamin A wanda yake da mahimci ga idon mutum, wani bincike ya gano cewa in dai mutum zai sanya kankana a gaba kullum zai ci na kimanin yankar N100 a yau, to ba ko shakka kankana za ta taimaka masa wajen kyautata ganinsa masamman domin wadan da ganinsu yake raguwa a dalilin aiki da na’urorin zamani kamar su talabijin, wayoyi da kwafyuta, ko kuma don tsufa.
Tura Zuwa:

Yadda ake Hada Lemun Abarba A Sawwake

Yadda ake Hada Lemun Abarba A Sawwake
Yadda ake Hada Lemun Abarba A Sawwake

Assalumu Alaikum yan uwa fatan alkairi a gareku da fatan an wuni lafiya insha Allahu yau zamuyi bayana nine akan yanda ake hada lemun abarba cikin sauki, abubuwan da kike bukata bai taka kara ya karya ba, saidai ga dadi ga kuma sauki:

KAYAN HADI: -  
==> Abarba
==> Suga
==> Ruwa
==> Fulebun abarba


YADDA AKE YI, da farko zaki wake kafin a bareta sai ki nika a cikin blender (na’uran markade) a tace, bayan an tafasa sugan, bayan ya huce, sai a hada su guri daya a sa fulebo, sai a motsa sosai, sai a saka a freezer yayi sanyi.
Tura Zuwa:

Bari ba Shegiya ba ce! Facebook ta amsa kiran ‘Yan Afirka

Bari ba Shegiya ba ce! Facebook ta amsa kiran ‘Yan Afirka
Bari ba Shegiya ba ce! Facebook ta amsa kiran ‘Yan Afirka
Bayan da aka akai harin kunar bakin wake a kasar Faransa a ranar Juma’a 13/Nuwamba/2015 munate da dama basu ji dadin yadda babban shafin sada zumunicin nan mai suna Facebook ya fito da wani tsari na canza hoton da ke wakiltar mutum zuwa tutar kasar Faransa.
Mutane daga kowane bangare na Duniya sun nuna bakin cikinsu dangane da wannan mummunan hari na ranar Juma’a sai dai a wani bangare kuma an samu korafe-korafen jama’a kasancewar kamfanin Facebook ya nema jama’ar duniya da su yiwa kamar faransar Addu’o’in zaman lafiya.
Wannan kira da kuma neman jama’a su can hotunan su ya bakantawa mutane da dama rai musamman mutaken yankin Larabawa da kuma nahiyar Afirka, musamman saboda ganin irin zubar da jini da ake yi ba dare babu rana a yankunan amma kuma daidai da nuna wani abu yana faruwa wannan kamfani bai taba nuna wa ba.
Hakan ya san wani shararren marubu ci mai kishin kasa Jafar Jafar ya rubuta zungureriyar wasika zuwa ga Mark Zuckerberg wanda shi ne shugaban wannan kamfani yana mai nuna damuwar sa da ko in kula da bai nuna wa ga jana’ar Afirka musamman idan aka dubi cewar mutane kusan sama da dubu goma sha takwas sun rasa rayukansu a hare-haren da Kungiyar Boko Haram take kaiwa a Arewacin Najeriya.
Ba ma Jafar da ya yi wannan rubutun ba kusan mutane sun yi amfani da wannan kiran da shi Mark Zuckerberg ya yi suna canza hotunan su zuwa hotunan kasarsu, kuma suka rika yin amfani da kalmar bai daya (Harsh Tag) suna cewar ayi wa duniya baki dayanta addu’ar neman zaman lafiya.

SAFETY CHECK


Wannan shi ne tsarin da kamfanin facebook suka fito da shi a Labara 18/Nuwamba/2015 bayan da aka kai harin da ya hallaka mutane a kalla talatin a garin Adamawa.
Wannan tsari ne da yaka baiwa duk wanda ya ke kusa da inda abin ya faru ya sanar da al’umma irin halin da yake ciki na yin makin cewar yana lafiya ko kuma shi babu abin da ya shame shi.
Wannan ba karamin ci gaba bane idan muka yi la’akari da irin korafe-korafen da jama’a suke yi na cewar ana nuna musu launin fata.
Duk da haka, wasu jama’a suna ganin cewar wannan fito da wannan tsari ba wani abin a zo a gani ba ne, domin har zuwa yanzu kamfanin bai dawo da tsarin da zai baka damar ka canza hotonka zuwa ga tutar Najeriya ba. A na su ra’ayin jama’a suna ganin idan dai ba nuna wariyar launin fata ba ya kamata a ce shi ma wancan tsarin na canza hoto ya kamata a ce yana aiki, kuma suna ganin kamar yadda yayi magana a cikin shafinsa na a nemawa Faransa zaman lafiya, ba wai dawo da tsarin fadin yanayin da mutum ya ke ciki za su ba, magana zai yi.
Sai dai muce Allah Ya kyauta kuma ya gafartawa suka riga mu da imani amin.
Tura Zuwa:

Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace

Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
 
Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, kuna tare ne da Muhammad Abba Gana insha Allahu yau zamnyi bayani ne akan amfanin lalle gaya mace, hakika Lalle na cikin wani sinadarin da ke dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da mata yin lalle akwai sirrika acikin sa mai griman gaske. Menene Amfanin Lallai?

In nace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai. toh a hakikanin gaskiya lalle yana da amfani diyewa ga rayuwan ya mace amma ga manyan daga cikinsu:

1.==> lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.

2.==> Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana kula da dumin mace, bi maana yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba.
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
3.==> Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu in Allah ya yarda zata warke.

4.==> Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.

5.==> Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.

Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace


6.==> A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan.ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum na mintuna talatin (30) kafin wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu.
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
7.==> Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun za kiga canji.
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
8.==> Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.

9.==> Sannan gamai son kamshin fata, Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu

10.==> Sannan ga Amare Kafin kiyi dilke na aurenki ki kwaba lalle mai kyau tare da turare mai maiko, turaren gargajiya mai mai, ki jika kamar bucket daya kada yayi ruwa ruwa sosai kamar dai kunu, kullum sai ki shafa a dukkan jikinki sai ki zo ki saka turaren wuta akasko ku burner ki rufu akai ki turara jikinki har sai hayakin turaren nan ya shiga jikinki sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki,za kiga canji a fatar ki rapid canji kuwa. Fata za tayi laushi, haske da kuma santsi. Wata biyu kafin bikin ki zaki iya wannan kedakanki kuma zakiji dadin hakan.
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace
11.==> Lalle nasa cikan gashi, ba yasa gashin kan mace ya zube, yana da matukan amfani wajen gyara gashin mace, inda wasu ke tura (steaming) gashin su dashi ma’ana.
Amfanoni sha biyu (12) da Lalle keyi Ga ‘Ya Mace


12.==> A karshe mata na yin ado da lalle wajen kara kyaun kwalliyar su. wanda su ke zanawa a jikin su.
Tura Zuwa:

Jus don sanyaya rai a lokacin zafi

Jus don sanyaya rai a lokacin zafi
Jus don sanyaya rai a lokacin zafi
 
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa damu a wannan filin namu na girke-girke uwargida wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. A yau na kawo muku jus din markadaddun ’ya’yan itace ne don sanyaya ran maigida domin zafin da aka shiga na kwanan nan. Abubuwan da za ki bukata ba ma su yawa ba ne. Ga arha, ga kuma biyan bukata.

Abubuwan da za a bukata

·              Abarba
·              Lemun zaki
·              Gwaiba
·              Flaba (wasu na kiransa da felebo)
·              Kanka na
·              Blanda (nau’ra na markada yayan itatuwa)
·              Abin matse lemu (orange skueeze/press)

Hadi

Idan uwargida ta sayo abubuwan da na lissafo za ta ga lallai ba wani abu mai tsada ba ne duka bai fi ta kashe Naira 300 ba. Ta bare abarba da gwaba da kuma kankana ta ajiyesu a gefe. Sannan sai ta samo lemun zakinta ta yanka shi rabi da wuka kamin ta daura a abin matse lemun zaki (orange press) idan ta samu ruwan lemu da dan dama, sai ta zuba ruwan a cikin blanda da yankakkiyar abarba da kwaba da kuma kankana duk a cikin blanda sai ta markadasu. Uwargida ba dole sai kinyi amfani da kayan zamani ba in har kina da wata dabara ta yanda zaki iya markadawa ba tare da yayi yaji ba ko matse ruwan lemun ba tare da wani dauda ba zaki iya yi.


Bayan ki markada, sai ki tace sannan ki zuba flaba, domin dada wa jus din kamshi. Idan uwargida mai son sukari ce, sai ta zuba siga. Amma babu sukari ya fi dadi. Sai a sanya a firiji domin ya yi sanyi kafin a zuba wa maigida a kofin gilashi domin sanyaya masa zuciya!
Tura Zuwa:

ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE

ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE
ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE
 
Idan aka ce smartphone ana magana ne da wayar da ta cika gari a wannan lokacin wacce zai yi wahala ka samu mutum biyu wadanda suke rike da waya amma kuma ba a samu mai ita ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina, ga shi kuma kamfanonin da suke yin su kullum kara fito da sababbi suke yi kasuwa.

Kodayake a irin tunani namu na bakaken fata kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna cewar wannan wayar tana da kyau, wani lokaci kuma neman iyawa da bajinta da nuna isa shi ke sa mu mallaki waya wacce take da tsada ba yin la’akari da me ke cikin wannan wayar ba ko kuma me wannan wayar zata iya yi mana.

Wani abu kuma da yake daurewa masu son su siya sabuwar waya shine, idan na samu kudi wace irin waya ya kamata in siya, ko kuma mene ne abin yin la’akari da shi idan ina son canza waya ko kuma sake sabuwa. Amsoshin wannan tambayar ya danganta da me kake son yi da wayar, domin wani yana yin la’kari da karfin wayar wurin rike wuta ko caji, wani kuma yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka, wani kuma yana yin la’akari da karfin network da take da shi, wani kuma yana yin la’akari da girman fuskarta, da dai makamantan wadannan.


1. ==> GIRMAN FUSKAR WAYAR

A wurin siyan waya ko tablet mutane suna yin la’akari da girman fuskar wayar wato (screen). Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa, wani kuma baya son ganin haka. To shi dai maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda yayi maka ba dole ba ne yayi wa wani. Amma dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar waya da barin ta cikin haske sosai na taimakawa wurin cinye caji.

2. ==> KAURI DA NAUYI

Kauri da nauyin waya abu ne mai muhimmanci a lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet. Kauri dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci sirantaka a wurin kayan computer bai cika bayar kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda haka ya danganta gare ka idan kana son kyau fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar waya ko tablet. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin karfe ne saboda haka tun kafin kabar wurin siya ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata tayi nauyi.

3. ==> MANHAJOJIN (Operating System) DA WAYA TAKE AMFANI DA SU

Babbar Manhajar da take sarrafa komai da ke jikin waya shi ake kira da Operating System, shi yake lura da hatta maballan da kake tabawa wurin kunnawa da kashewa, shi yake lura da sauti da kalan da yake fita a wayar. To lallai wurin siyan waya yana da kyau ka duba da kyau domin ka san wane irin manhaja ce a cikin wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin mu suka sani cewar wayoyin da muke rikewa suna da banbanci wurin gininsu da kuma wane ne yayi su? Kunga dai wayoyi idan ya zo ga maganar Operating System akwai na Android, sannan ga iOS, sai Microsoft Phone 7, sai Blackberry ga kuma web OS da Symbian, dukkan wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu sun dauka cewar waya ce. A a kamfani da yake yin karfe da kyan da suke jikin waya daban sannan manhajar da ake saka mata da ba. Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane sun fi sabawa da su a matsayin waya maimakon Babbar Manhaja ce.

4. ==> WURIN ADANA BAYANAI

Mafi yawan kanfanonin da suke yin wayoyi da tablet a wannan lokaci suna kokarin ganin sun yi mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda zai baka dama domin a jiyar hotuna da rubutu da sauti da hotuna masu motsi. Kodayake wadansu saboda yanayin yadda suke tara abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin abubuwa a ciki. To a nan yana da kyau ka sani wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada ramin kara ma’ajiya wato Memory, saboda haka idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa ne sai ka nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman mazubi.

5. ==> KARFIN SHIGA INTERNET

Kusan dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna zuwa da tsarin sadarwa maras waya (wireless) wanda ya ke basu damar iya kulla alaka tsakaninsu da ko kamfanin layukansu ko kuma hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma ofis da dai makamantansu. Irin wadannan hanyar da ake amfani da ita domin samun sinadarin shiga intanet ba tare da amfani da layin waya ba shine ta hanyar amfani da Wai-Fai (Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda zai sayi waya a wannan lokaci ya san cewar yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third Generation) ta wurin shiga intanet, a’a a wannan kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka tsallaka karni na hudu 4G.

Wayoyin da aka yi a baya sun fara ne da 1G sai kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan wayoyin ba sa ba msutum damar shiga intanet da sauri, koda kuwa a inda mutum ya ke akwai network mai kyau da karfi. Daga baya suka shigo da 3G wanda yake bamu damar har kallon hotuna masu motsi (video) muke yi ba tare da yana tsayawa ba. Saboda haka yanzu mafi yawan wayoyin da ake yi suna baka damar amfani da karfin network na 3G da 4G, sai a kiyaye idan an je siya.

6. ==> KANA NAN MANHAJOJI

Daya daga cikin abin da mutane da dama suke yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri kaza shin dawe application ne zan iya aiki, kusan a wannan lokaci da muke ciki kasancewar wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin koyan yadda ake kirkiran manhajojinsu, yasa mutane da dama suke son siyar wayar Android. Amma kuma idan aka zo ga zafafan Manhajoji to sai muce manhajojin da ake amfani da su a waya kirar Apple sun fi shahara da kwarjini.

Misalia shagon Apple akwai manhajoji dubu dari uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu da hamsin na kyauta da kuma siyarwa. Suma sauran manhajoji irin su Blackberry da makamantansu suma suna da shagunan da ake samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple da Android yawa ba.

7. ==> Kamara da Nado Sauti'

Hakika wadannan abubuwa guda biyu sun karawa wayoyin tafi da gidanka daraja, kusan a yanzu mutane da dama suna yin amfani da kamarar jikin wayoyinsu domin daukar shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi, wasan kwaikwayo da dai makamantansu. Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan lokacin suke kara yin tsada, duk da cewar mutane da dama basu cika kiyaye haka ba.

Kusan a yanzu akwai wayoyin da ake da su wadanda saboda karfi da kyau yanayin hotuna da suke dauka hatta mawaka suna amfani da su wurin shirya wakokinsu. Haka yan jarida a wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin nado sauti da zasu iya kai rahoto da shi. Duk da cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma waya da kamara da kayan daukan sautin da ke jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan tafi da gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba kowace waya bace ta ciki inganci a kan haka. Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na hoto ba to ba sai ka sayi waya mai tsada ba.

8. ==> DADEWAR BATIRI

Lallai ko ba a fada maka ba kasan cewar batir yana da matukar muhimmamci a jikin waya domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan har batirin wayar baya dadewa abin ya zamo da shirme ke nan. Shi yasa kuwan mafi yawan kamfanonin da suke kirkirar waya suka fi mayar da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da irin kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin suna yi sai ka samu kamfani yayi waya kuma cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai kama da wuta, amma dai suna kokari.

 Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta batirinsu har kaga waya tana iya kwana uku tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan muka sayi waya bama karanta takardar da take zuwa da ita.


Wannan shine abubuwan da zan iya kawo muku wadanda sune abubuwan da ya kamata mu rika yin la’kari da su wurin sayin waya.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *