Talla
na daya daga cikin tsari mafi sauki da mutum kan iya bi wajen sanar da al’umma
yadda ingancin kayansa yake da kuma yadda zai taimaki mutane a ayyukansu na yau
da kullum.
Amma yawan tallata kaya guda na tsawon lokuta mai tsawo yakan
gunduri mutane har a wasu lokutan yakan sa wasu su tsani kayan saboda yadda ake
yawan tallatasa daga lokaci zuwa lokaci.
Wayar
salula ya kasance kusan wani bari na rayuwa a duniyar mu ta yau; ta yadda bamu
iya zama na yan wasu kankanin lokaci ba tare da duba cikinsa ba. Duk da cewar
yana da matukar amfani domin kuwa yana taimakawa ta bangarori bila adadin.
Mutane
da dama sukan fusata bisa yadda sabbin wayar salulan Andriod suke dauke da
tallan manhaja a menu wadda a koda yaushe suna chanza launi a duk lokacin da
ita wayar salulan ta shiga yanar gizo ko kuma ta sun-suni data.
Idan kana/kina
daya daga cikin wayanda basu bukatar ganin wannan tallar na manhaja insha
Allahu yau Duniyar Fasaha ta kawo muku hanya da za’a bi wajen magance wannan
matsalar cikin sauki ba tare da tuntuban kwararre ba haka zalika ba tare da
kashe ko sisi ba.
Har
Ila Yau Kuna Tare Da Jikan Marubuta Wato Muhammad Abba Gana Tare Da Alqalaminsa
Matakan
Da Za’a Bi Wajen Dakatar Da Tallar Manhaja A Wayar Salulan Andriod
Domin
dakatar da wannan tsarin ga wayanda basu bukata, wayar salula dole ya kasance a
kunne sannan kuma cikin koshin lafiya domin gujewa wani matsalar.
Mataki
Na Farko: Da fari za’a koma asalin fuskan wayar
salulan wadda aka fi sani da home page a turance.
Mataki
Na Biyu: Sai a latsa wajen da babu komai tare da
tsayawa (Press and hold) har sai wasu zabi sun fito. Abin Kula: Kada
a latsa waje mai dauke da manhaja. Wasu daga cikin abinda za’a gani sun hada da
“Wallpapers”, “Widgets”, “Arrange Desktop”, “Desktop Settings”.
Ba lallai ya
kasance irin daya ba saboda wayoyi sun sha ban-ban idan har mutum bai ga abinda
na lissafo ba sai ya tura jerin ababen da aka lissafo masa zuwa hannun hagu
wadda hakan zai basa damar ganin wasu zabin na daban.
Mataki
Na Uku: A cikin jerin ababen da aka lissafo mana
sai mu zabi “Desktop Settings” ta hanyar latsa hoton da ke kansa ko kuma ta
hanyar latsa sunnan.
Yin hakan zai bamu damar zuwa shafi na gaba.
Yin hakan zai bamu damar zuwa shafi na gaba.
Mataki
Na Hudu: A wannan shafin da muka shiga na “Desktop
Settings” akwai abubuwa da aka lissafo mana masu yawan gaske wadda ko
wanne daga cikinsu yana da matukar amfani wajen saita yadda fuskar waya zata
kasance. Abin
kula: kada a shiga abinda ba’a sani
ba domin yin hakan zai iya chanza surar ita wayan gaba daya wadda zai iya
kasancewa babbar matsala. A nan zamu dan sauka zuwa karshe ta hanyar tura jerin
ababen da aka lissafo mana zuwa sama.
Mataki
Na Biyar: Zamu ga wajen da aka rubuta “Other
Settings” sai mu latsa kai, yin hakan zai bamu damar shiga wani shafi
na daban.
Mataki Na Shida: Haka
zalika wannan shafin da muka shiga akwai jerin setuka daban-daban. Domin
dakatar da tallace-tallace da ake mana a home menu na wayar salulan mu dole mu
kashe wasu abubuwa guda uku. Da farko akwai “Application Recommendation”
na biyu kuma “Instant Apps” sannan na karshe kuma “Instant App Reminder”.
Za’a
kuma iya kashe sune ta hanyar latsa dan karamin mabullin da aka tanadar wadda
zai taimaka wajen chanza wa dan karamin “kwallon” alkibla.
Idan
har kalar akwatin ya nuna “blue” sannan kuma dan karamin kwallon yana fuskantan hannun dama to
hakan yana nufin cewar haryanzu a kunne yake. Haka zalika idan kuma kallar
akwatin ya koma baki sannan dan karamin kwallon ya koma fuskantan hannun hagu
to hakan yana nufin an kashe tsarin wadda kuma shi ake bukata.
Ba
lallai a samu dukka tsarin a kunne ba zai iya kasance wa daya daga cikinsu yana
kunne ko kuma biyu haka zalika zai iya kasancewa dukka a kunne a kowani hali
aka samu to fa lallai sai an tabbatar da an kashe dukka ukun domin cinma manufa.
Wannan shine cikakken bayani yadda ake
Dakatar da tallan manhaja da suke fitowa a menu na wayar salulan Android. Shin
akwai wata hanya mafi sauki da aka sani wadda zai taimaka matuka? Shin akwai wani
mataki da muka tsallaka yayin rubutu? Za’a iya turo mana ta hanyoyin sadarwanmu
na Facebook, Whatsapp da Kuma Twitter. Allah ya taimakemu dukka Ameen!
Please send me your whatsapp number
ReplyDeleteok... 09039016969
DeleteGaskiya naji dadin Wannan Rubutun Saboda Wannan tallar ta cimin data ban san iyakar Allah ya taimaka ya qara Basira muna beyeda da Kai sauda da qafa
ReplyDeleteGaskiya naji dadin Wannan Rubutun Saboda Wannan tallar ta cimin data ban san iyakar Allah ya taimaka ya qara Basira muna beyeda da Kai sauda da qafa
ReplyDeleteGaskiya naji dadin Wannan Rubutun Saboda Wannan tallar ta cimin data ban san iyakar Allah ya taimaka ya qara Basira muna beyeda da Kai sauda da qafa
ReplyDelete