Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Tare Da 

Muhammad Abba Gana

A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.

Mafi yawancin wadannan mune wato matasa yan uwana, mukan bata kusan dukkan lokutanmu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo, neman yan mata, karanta littatafan hausa na soyayya ko yaki, neman saurayi, karatun boko, kallon videon kwallo, wakar hausa ko misic da dai makamantansu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mu har ma ya sanya bamu kula da wasu manyan damammaki da zasu iya amfanemu domin samawa kanmu wasu ‘yan kudade na a kasha, wasu lokutan ma har yakan shagaltar damu wajen yin ibada.

A zamanin da muke ciki yanzu mutane sunfi sha’awar aikin gwamnati mutum yana so aji ana cewa ya tafi office ko kuma yana da hadadden office mai dauke da kayan sanyi na zamani sannan kuma a karshen wata yana da wani kayataccen albashi mai tsoka da wannan ake rudan wasu sannan a cusa musu sha’awar shigarta ta ko wacce hanya.

Idan kuma muka maida duba izuwa ga sana’ar hannu zamu ga cewar akwai wasu sana’oi da dama da mutum zayyi wanda zai iya tashi da dubu 5 koma fiye da haka wadda in an kwatanta za’a ga cewa abinda mutum zai samu a karshen wata zai nikka albashir mai aikin gwamnati har sau biyu ko fiye da hakan.

Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yi wani sana’a  kafin ya iya samun kudin da zai siya Data, amma kuma bai san ta yaya zai iya samin kudin a saman yanar gizo (Internet).ta hanyar amfani da datar daya siya. Insha Allahu a wannan makon, Duniyan Fasaha zata kawo muku wadansu cikakkun hanyoyin da za’a iya bi domin neman na kashewa a saman yanar gizo (Internet).

1.==> HADA SHAFUKAN YANAR GIZO: Shafukan yanar gizo abune mai matukar amfani sabili da yana taimakawa wajen bada cikakkiyar bayani game da kasuwanci cikin sauki, A hakikanin gaskiya adadin shafuka a yanar gizo yana ninkuwa a kowace waye war gari, haka kuma adadin masu bukata yana kara bunkasa.

Masana kimiyya sun nuna cewar duk wata kasuwanci da bata hadayya da yanar gizo to hakika ta na rasa wasu damammaki da zata iya samu wajen tafiyar da kasuwancin, haka zalika alamomi sun nuna cewar duk wani kasuwanci da bai da shafi na mussanman a yanar gizo nan da wasu shekaru masu zuwa dole sai ya samo.

            Hada shafin yanar gizo ba kowa zai iya yinta ba sai wadda yake da ilimi sannan kuma yake da basiran yin hakan, akwai mutane da dama wadda suka gwanance wanje suranta shafukan yanar gizo sannan kuma sun dauke ta a matsayin sana’a.

Hada shafi a yanar gizo ba wani abu mai matukar wahala bane sai dai ya zamana dole mutum ya koyi wasu yaruka wadda aka fi sani da ‘programming language’ a turance wadda ita kwanfuta ke fahimta; misali: php, python, JavaScript, ajax, java, Asp.net da dai sauransu.  ko kuma mutum ya koyi yadda ake amfani da wordpress, wix (wadda zanyi jawabin su a wasu makonin masu zuwa) ko kuma blogger wadda nayi jawabinsa a wasu makonni da suka gabata. Koyon daya daga ciki ababen da na lissafo zai bada damar samun makudan kudi a yanar gizo.  

2.==> JAGORA: Wannan wata halattacciyar hanyace da ake samun kudi da ita ta hanyar jawo wani yayi rajista bayan anyi sannan kuma an tabbatar da ingancinsa. A mafi yawanci sa’oi wannan damar yana aiki ne ga manya ko kuma sabobbin shafuka dan samun mabiya da zasu taimaka musu wajen gudanar da kasuwancinsu.

Yadda abun yake anan shine: Bayan anyi ragista da ita kamfani a mafi yawancin lokutan sukan saka wani adadin kudi da mutun zai samu yayin da ya gayyato wani yayi ragista dan taimaka musu wanjen tallar hajarsu. Sukan bawa kowa addireshi na musamman da zaiyi amfani dashi wajen gayyato mutune.

Duk sa’an da wani yayi rajista da wannan addireshin wadda ya basa zai samu ‘yan wasu changi. Inji bahaushe Iya kudinka iya shagalinka haka zalika ‘Yawan mutanen da ka jawo yawan kudin da zaka iya samu’. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada da Konga.com, alibabab.com, Jumia.com.ng, Be With Me Technology, EntireWeb, Renkutten, Yllix, dadai sauransu.

3.==> HADA MANHAJAR WAYA: Adadin mutane dake amfani da wayar salula ya zarce yadda ake tsanmani, sannan adadin yana ninkuwa a kowace wayewar gari.  Wayar salula yakan taimaka matuka wajen sa da zumunta ta hanyoyi daban daban haka zalika adadin mahajar da ake kirkira yana kara ninkuwa a kowace safiya bisa la’akari da yadda mutane ke sa’awar amfani da ita musamman android.

Mutum zai iya hada mahajar waya sannan ya siyar ko kuma za’a iya biyansa ya hada hajar sai dai wannan yana tafiyane hannu riga dana fari dole sai mutum ya koyi wasu yarukan kwanfuta dana ambata a baya kafin cin ma manufa. Amma Alhamdullilahi a yanzu akwai wasu shafukan yanar gizo dake bada damar hada mahajar ba tare da koyon daya daga cikin yarunkan dana ambata a baya ba irin su Androidmob da kuma Appgeyser. Sai dai matsalar wayan nan shafukan basu bada cikkakiyar damar amfani da ita sai an biya wasu kudade.

Lallai ba shakka mutum zai iya samun kudi na hakika da mahajar da ya kirkira ta hanyar saka tallace tallace a ciki, duk sa’ar da wani ya danna wannan tallan zai samu yan wasu changi haka zalika za’a iya biyan mutum makudan kudade dan tallata wata haja kamar yadda zamuyi bayani a gaba.       

4.==> SAKA HOTUNA MAI MOSTI (VIDEO) A YOUTUBE:  Wata hanya da ba kowa ne ya san da ita ba ko kuma yasan amfaninta ba a cikin mutanenmu shine yadda za’a iya samin kude daga YouTube.

Wannan hanya ce mai matukar sauki. Kawai abin da kake bukata shine ka mallaki google account (gmail). Za ran ka mallaki gmail zaka iya zuwa YouTube domin da bude channel.

A cikin wadannan channel din ne zaka rika dora bidiyoyinka. Domin samin kudi a duk lokacin da wani ya kalli wannan bidiyo sai ka tabbatar ka shiga wajen settings kayi checking ko kuma ka zabi monetize, wannan zaya baka damar da zaka sami kudi a duk lokacin da YouTube suka sanya talla a cikin bidiyonka.

5.==> TALLA: Shima wannan wata hanya ce da ake samun kudi a internet ta hanyar yin talla, Duk wani wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu. Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla.

Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafinn. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar da ya kamata.

Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.


Wadanna sune wasu daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su wajen samun kudi a internet, shin ka/ki na da wata hanya da ka/kika sani wanda ban ambata a cikin wannan kasidar ba? Za’a iya turo mana dan dad’awa wanda zai taimaka wa masu ziyara nan gaba. 
Tura Zuwa:

Cikkakkun Hanyoyi shabiyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki Cikin Sauki

Cikkakkun Hanyoyi shabiyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki Cikin Sauki

Tare Da

Muhammad Abba Gana

Shin yaya zaki lura da fata cikinkin sauki? Babu shakka ba wata haifaffiyar ya mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki, yalki da kuma kyan gani; babu kuma macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankali. Amma kuma wace matakai za’a bi wajen lura da fatar cikin sauki yakan zama matsala.

Hakan ya sanya mata da yawa ke kashe makudan kudade wajen lura da fatar jikinsu ko ta fuska ta hanyar amfani da magunguna asibiti. Da yawa daga cikin mata kuma sun fada tasku sakamakon amfanin da mayukan da suke da sinadarai, wanda a maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu sai su buge da da-na-sani. Wannan dalilin ya sanya Duniyan Fasaha ta taho miki da Cikkakun hanyoyin sha biyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki ba tare da tararradin ko fatarki za ta gamu da wata matsala ba. Ga hanyoyin kamar haka:

Cikkakkun Hanyoyi shabiyar (15) da za ki bi wajen lura da fatarki Cikin Sauki


1.==> Ki samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun. Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi. Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata.

2.==> Shan ruwa mai yawa. Amfanin shan ruwa ga jikin dan adam yana da yawan gaske. Duk da cewa a lokacin sanyi mutane ba su fiye son shan ruwa ba, amma hakan babbar hanya ce wajen taimaka wa fatarsu ta kasance tana sheki tsawon lokacin hunturu. An so mutum ya sha ruwa kimanin lita biyu zuwa uku a rana. Sai dai wannan bai hada da shan shayi ba, a maimakon haka an so mutum ya yawaita shan lemo.

3.==> Ki samu karas sai ki markada, daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki. Bayan awa biyu sai ki wanke da ruwa mai dumi. Yin hakan zai sanya jikinki ya rika haske da kuma daukar hankalin duk wanda ya kalle ki.

4.==> Man kadanya: tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata.

5.==> Ana so a rika yawaita goge jiki ‘scrubbing’ wannan shi zai sa duk wata matacciya da busasshiyar fata ta fita tare da ba wa sabuwar fata wuri don tofowa.

6.==> Ki samu lemon zaki sai ki yayyanka, daga nan sai ki markada. Bayan nan sai ki shafa a fuska ko a jikinki. Wannan zai sanya miki laushin fata.

7.==> Shafa mai akan lokaci, mun san yadda jiki yake saurin bushewa saboda kadawar iska. A duk lokacin da aka yi wanka yana da kyau a shafa ma tun a bandaki lokacin da dan ragowar danshi a jikin fatar.

8.==> A zabi mai da ya dace da lokacin sanyi, ma’ana mai wanda ke da maiko wanda zai sa fata ta kasance cikin danshi na tsawon lokaci. Duk wani mai da zai zama ya sa fata tauri ba shi da amfani a wannan lokaci na sanyi. A wannan lokaci amfani da man kadanya ko man zaitun yana taimakawa fata kwarai da gaske.

9.==> ki gauraya ruwan Rose Water da kuma ruwan lemon tsami. Ki shafa a fuskarki ko jikinki. Yin hakan zai cire tabon da yake fata ko fuska, sannan yin hakan zai sanya fata ta yi laushi da danshi.

10.==> Kaushin fata: idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin.


11.==> ki samu madarar shanu wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri da kuma cokali biyu na ruwan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami, sannan ki gauraya sosai. Bayan nan sai ki samu auduga ko tsumma mai tsabta sannan ki rika dongala kina gogawa a jikinki ko a fuskarki. Bayan nan, sai ki wanke jikinki ko fuskarki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire miki dukkan dattin da ke makale a kofofin fatarki.

12.==> Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska.

13.==> Ki samu kukumba sai ki yayyanka ta, daga nan sai ki nika ta, sannan ki ajiye ta gefe guda. Hada ruwan Rose Water da ruwan lemon tsami ko jus din lemon tsami. Bayan nan sai ki hada su waje guda da kukumbar, sai gauraya sosai. Bayan kin yi haka sai ki shafa a fuskarki ko sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta har zuwa wayewar gari. A lokacin da kika zo wankewa, sai ki samu ruwa mai dumi. Hakan zai kara wa fatarki lafiya da kuma sheki.

14.==> Fason kafa: yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar.

15.==> Karyewar gashi: kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwakwa na hana gashin kai zubewa.


Shin kina da wasu hanyoyi da kike ganin zai taimaka wajen kula da jiki da ban zayyano a cikin wannan rubutun ba? Taimaka mana ta hanyar rubutawa a comment box dake kasa. Ko kuma ta hanyar tuntubanmu dan bada gudumawa. 
 

 
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *