Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Iyaye a rage nuna wa ’ya’ya so

Iyaye a rage nuna wa ’ya’ya so

A yanzu iyaye mata wadanda aka fi sani da kawaici da kunya a kan ’ya’yansu suna kokari su yaye lullubin kunyar da ya lullube idanunsu ta yadda suke nuna son ’ya’yansu a fili. A zahirin gaskiya babu mutumin da ba ya son dansa, amma wane irin so? Shin son da zai sa yaron ya zama shagwababbe ko kuma wanda zai sa ya zama ba ya shakkar kowa?

A da makwabci yana da cikakken iko da damar hukunta dan makwabcinsa idan ya ga ya aikata wani abin Allah-wadai. Idan mahaifin yaron kuma ya zo ya ji labari babu abin da zai yi sai dai ya kara wa dan nasa wani sabon fadan ko kuma duka tare da yi wa makwabcin nasa godiya. Shin a yau haka abin yake?

A wannan zamani ta kai iyaye ba su so su ga wani ko da dan uwansu ne ya yi wa ’ya’yansu fada a kan wani abu da suke aikatawa na rashin daidai, ballantana kuma har ya kai hannunsa jikinsu. Idan suna jin kunya ne za su yi shiru sai dai shi mutumin ya gane kuskurensa ta wadansu hanyoyin, amma idan suka raina ajawalinsa to har gida cin mutunci zai iske shi.

Akwai iyayen da saboda tsabar son ’ya’yansu babu wanda yake iya fitowa fili ya gaya musu laifukan ’ya’yan, sai su nuna rashin amincewarsu a kai, har ma su nuna cewa mutumin yana so ne kawai ya yi wa ’ya’yan baki. Idan ba a yi sa’a ba kuma daga wannan lokaci sun daura gaba da wannan mutumin ke nan.

Wannan shi ya kara iza wutar lalacewar tarbiyyar yaya a wannan lokaci, kiri-kiri mutanen unguwa suna kallon yara suna aikata laifuka amma babu wani wanda zai fito ya tsawata musu, ballantana kuma ya gaya wa iyayensu halin da ake ciki, ba don kaomi ba sai don tsoron abin da zai biyo baya.

A wadansu lokutan za ka ga uwa ta san danta yana aikata wani abu da bai dace ba, maimakon ta yi gaggawar sanar da mahaifinsa don daukar matakin da ya dace, musamman ma da yake yara sun fi jin tsoron iyaye maza fiye da mata, sai dai ta rika boye masa, wai don kada ya yi wa yaran fada. Ba tare da sanin cewa kanta take cuta ba, domin Hausawa sun ce itace tun yana danye ake tankwara shi. Sai ka ga wannan uba ba zai tashi sanin abin da dansa ke ciki ba sai abu ya gama lalacewa ya kai matakin da sai dai addu’a.

Akwi matar da na sani kai ko da mijinta, wato mahaifin ’ya’yanta, ba shi da ikon ya yi musu fada a gabanta. Idan kuma har bacin rana ta sa ya yi hakan, to fa su sun samu lauya, domin ita za ta zama bakinsu ta kare su da dalilai irin nata. Kai wani lokacin ma sai ta gwaba wa mijin cewa wai shi wa ya san irin kuruciyar da ya yi? Ko kuma ta ce wai yara ne sai a hankali wata rana za su daina, da dai makamantan irin wadannan maganganu marasa tushe ballanatana makama. Idan kuma aka yi sa’a ba ta yi surutai ba, to fa mijin zai gane kurensa ta hanyar yin fushi da shi na tsawon lokaci.

Idan har ya kasance a matsayinki na uwa wacce ke ce a bangare marar karfi, domin kusan a ko’ina ’ya’ya sun fi raina uwa mace kasancewar ita ce a koyaushe ke tare da ’ya’ya, zai zama cewa kina nuna wa ’ya’yanki so a fili, ba ki son a fadi laifinsu, to kina cikin matsala babba. Ki sani ’ya’yan nan idan suka fahimci hakan za su iya aikata kowane irin abu a gabanki, sanin cewa babu abin da za ki iya aiwatarwa a kai.

Ban da ma haka, duk dan da ya san cewa idan har ya yi laifi aka zo aka fada a gidansu iyayensa ba su daukar wani kwakkwaran mataki na yi masa fada, to fa ya samu lasisin da gobe ma zai je ya aikata wata aikaaikar da ta fi ta baya muni.

Akwai wani yaro da a yanzu ya yi nisa a fagen shaye-shayen miyagun kwayoyi, wanda kuma iyayensa ba su kai ga sani ba sai da abu ya lalace. Amma da aka zo ana tattauna maganar sai wadansu a unguwar suka bayyana cewa su sun dade da sani, amma sun ki fadi ne gudun kada iyayen yaron su dauki maganar a wata manufa ta daban.

A ganina tarbiyya ba ta mutun daya ba ce, ma’ana ba a kan iyaye kadai take ba, abu ne da yake kan al’umma gaba daya, amma hakan ba zai yiwu ba sai da hadin kan iyaye. Kasancewar ba kowane lokaci ne iyaye ke tare da ’ya’yansu ba, ka ga akwai yiwuwar su iya aikata wadansu abubuwa ba a kan idanun iyayensu ba, ko kuma ma akwai yiwuwar su fita waje su aikata wani laifin da sun tabbatar ba za su iya aikatawa a gaban iyayensu ba, to ka ga a nan jama’ar gari za su iya taimaka muku wajen tsawata wa ’ya’yan.

Babu shakka a dabi’ar yaro yana son sakewa da walawa, ba ya son takurawa, don haka yana ganin duk wani wanda zai yi masa fada a matsayin mai takura masa. A matsayinki na uwa babu ruwanki da kallon fuskar da a lokacin da kike yi masa fada ko kuma kula cewa yana fushi ko kuma gudun kada dan ya dauke ki a matsayin wacce ba ta son sa da sauransu. Akwai lokacin da zai gane gaskiya ko ba dade ko ba jima.

Idan har muna so lamarin tarbiyyar ’ya’yanmu ya tafi yadda muke so, to dole sai mun hada karfi da karfe mun ba sauran abokan zama fuskar da za su fito su gaya mana halin da ’ya’yanmu suke ciki ko kuma mu ba su damar hukunta ’ya’yan namu kai tsaye a duk lokacin da suka ga suna aikata ba daidai ba, musamman ganin irin yadda yau ta zama yau.


Hausawa suna cewa, “ka ki naka duniya ta so shi. Haka kuma ka so shi duniya kuma ta ki shi.” Idan muka tsaya muka yi nazarin wannan Magana za mu gane cewa akwai hikima babba a cikinta. Akwai kuma kalubale a gabanmu. Dole ne sai mun bude wa ’ya’yanmu idanu mun dora su a kan hanya ta gaskiya ko da ba sa so, sannan ne za su zama cikakkun mutane wadanda za su iya shiga cikin sauran jama’a su kuma yi mu’amala mai kyau. Allah Ya sa mu dace, amin.
Tura Zuwa:

Makulashen Azumi – Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su

Makulashen Azumi – Kunun Buda Baki Kala 5 Da Yadda Ake Sarrafa Su

Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, Insha Allahu yau zamuyi jawabine akan kunun buda baki kala biyar da yadda ake yinsu. Kunu na daya daga cikin abubuwan da aka fisha a lokacin azumi musammam ma a lokacin bude baki, domin bukatar a dumama ciki a kuma warware kayan hanji. A yau muna tafe da kalolin kunu guda 5 kamar haka;

Kunun Madara

Kayan Hadi
1.      Madarar gari
2.      Danya ko busasshiyar citta
3.      Fulawa
4.      Lemon tsami
5.      Dafafiyar alkama ko shinkafa
6.      Sikari
7.      Masoro mai kwanso

Yadda ake sarrafawa

==> Ki dama madarar gari da ruwa sai ki zuba masoro da citta a ciki sai ki bari ya tafaso.
==> Idan ya tafasa sai ki kawo dafafiyar shinkafa ko alkama ki zuba a cikin madarar ki juya sannan ki kawo fulawa ki kwaba ta da ruwa ki na zuba wa a ciki kina juyawa a hankali har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
==> Sai ki sauke daga kan wuta ki bari ya dan sha iska kadan, sannan ki kawo lemon tsami ki matsa kadan a kai ko kuma iya yadda ya yi miki, sannan ki zuba sikari.

Kunun Gyada

Kayan Hadi
1.    Gyada
2.    Shinkafa
3.    Fulawa
4.    Lemon tsami
5.    Sikari
Yadda ake Sarrafawa

==> Ki jika gyada ta jiku sannan ki wanke ki cire bawon ta. Sai ki nika ki tace ta.
==> Sai ki zuba wannan tataccen ruwan a kan wuta ki zuba danyar shinkafa, amma idan kina sauri za ki iya zuba dafaffiyar shinkafa, ki na juyawa akai-akai saboda ruwan gyadar zai na kumfa yana tasowa.
==> Idan da danyar shinkafa ne sai ki bari har sai shinkafar ta dahu, amma idan da dafaffiyar shinkafa ce sai ki bari har sai kin ji babu gafin gyadar.
==> Ki dama fulawa da ruwa, ki daure kunun da ita. Za ki na zuba fulawar a hankali har sai kin ga kaurin ya yi miki. Sai ki sauke ki matsa lemon tsami idan ya dan huce, sannan ki zuba sikari.

Wannan hanya ce daya kawai da ake yin kunun gyada, akwai wasu hanyoyin daban.

Kunun Mardam

Kayan Hadi

1.    Garin kunu
2.    Citta
3.    Kaninfari
4.    Lemon tsami
5.    Nono
6.    ‘Ya’yan cumin

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki samu ruwa ki zuba a cikin tukunya ki saka citta da ‘ya’yan cumin ki dafa har sai sai kin ji sun fara kanshi.
==> A gefe daya kuma sai ki dama garin kunun, ki zuba nono a kai da dama sannan ki dan kara ruwa kadan, sai ki ringa zubawa a cikin ruwan cittar daya tafasa a hankali, ki rage wuta sosai ki barshi ya yi kamar minti hudu akan wuta.
==> Idan ya yi kauri da yawa kina iya kara ruwa dan kadan.
==> Sai ki sauke, idan ya dan huce sai ki saka lemon tsami. Idan kina so ki na iya saka sikari, ko kuma ki bar shi ki sha haka da gardinsa.

Cumin ana samunsa a wajen masu sayar da kayan kanshi a kasuwa ko kuma a kantinan sayar da kayan masarufi.

Kunun Alkama

Kayan Hadi

1.      Garin alkama da ‘ya’yan alkama
2.      Citta
3.      Kirfa
4.      Sikari
5.      Lemon tsamiKanunfari

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki dafa alkama har sai ta yi laushi sosai.
==> A gefe guda kuma ki dora ruwa a wuta ki saka kanunfari da kirfa a ciki.
==> Sai ki samu garin alkama ki kwaba shi da wani ruwan daban.
==> Ki juye wannan alkamar da kika dafa a cikin ruwan kanunfarin da ke kan wuta, sannan ki
fara zuba kwabin alkamar ita ma a cikin ruwan a hankali.
==> Ki bar shi ya yi kamar minti uku zuwa hudu akan wuta sannan ki sauke.
==> Idan ya huce sai ki zuba lemon tsami da sikari.

Kunun Tsamiya

Kayan Hadi

1.        Garin kunu
2.        Tsamiya
3.        Sikari
4.        Barkono
5.        Kayan kanshi

Yadda Ake Sarrafawa

==> Ki samu gero a sirfa miki sannan a bakace a fitar da dusar. Ki wanke shi sosai ki kuma rege domin gero baya rasa tsakuwa.
==> Sai ki baza shi akan tabarma ya bushe. Idan bushe sai ki zuba barkono da kayan kanshi sannan ki kai a nika.
==> Ki tankade nikan da rariya mai laushi.
==> Ki jika tsamiya, idan ta jiku sai ki tace ki zuba tsamiyar a cikin garin kunun ki kwaba amma ba da kauri ba.
==> Idan kina so kuma kina iya yin gaya, ki zuba ruwa da sikari a cikin garin kunu ki kwaba da kauri.
==> Ki dora ruwa daidai adadin kunun da ki ke so, idan ya tafaso sai ki saka gayan, ki rufe tukunyar har zuwa minti goma don gayan ya dahu.

==> Idan kin tabbatar gayan ya dahu sai ki kawo tafasashshen ruwan ki juye shi a cikin garin kunun da ki ka kwaba, sannan ki juya. Idan ya huce sai ki sa sikari ki sha ko kuma ki sha haka.
Tura Zuwa:

Mahimmancin amfani da lemun tsami a fata

Mahimmancin amfani da lemun tsami a fata

Ko kun kasance daga cikin wadanda kurajen fuska ke bata musu fuska? Shin kun kasance cikin wadanda garin shafeshafen na’ukan man kara hasken fata, kuraje na fesowa musu tare da barin tabo bakake? Ko kun san mene ne zai warkar da wadannan tabon da kuma kurajen da sanya fata haske? Lallai ba wani abu bane illa amfani da lemun tsami na tsawon wata uku ko fiye da hakan. Lemun tsami na dauke da sinadaren da ke magance kowace irin cutukar fata, amma idan an yi hakuri. Kasancewar ganin yadda wannan hadehaden lemun tsami ke taka rawar gani a wajen yaki da cututtukar fata ya sanya a yau na kawo muku mahimmancin amfani da shi a fata domin samin sauki a wadannan cutukan da kuma yadda za a yi amfani da su.

==> Amfani da shi a matsayin man shafawa: a sami man kwakwa sannan a zuba a cikin murta sai a sami lemun tsami kamar guda daya ko biyu sannan a matse ruwansa a cikin wannan man kwakwar sannan a kwabasu a rika shafawa a jiki a matsayin man shafawa. Yin wannan hadin na kare fatar jiki daga cututtuka da dama.

==> Haskaka gwiwar kafa da gwiwar hannu da kuma yatsar da ta yi baki sakamakon man kara haske: Idan gwiwar hannu da gwiwar kaka da kuma yatsun kafa da hannu sun yi baki sosai sakamakon yawan shafa na’ukan man kara haske. Sai a sami lemun tsami daya a yanka shi zuwa gida biyu sannan a rika shafawa a inda ya yi baki a jiki na tsawon minti ashirin safe da yamma a kullum, za a sha mamaki.

==> kurajen fata: A sami lemun tsami a yanka shi zuwa gida biyu sannan a rika matse ruwansa ana gogawa a kan kurajen ko kuma tabon fata. A sannu a hankali tabon zai fara haske har ya bata. Amma sai an yi hakuri. Ina so idan aka fara amfani da wannan hadin kada a rika matse kurajen.

==> Domin cire kwalliyar fuska: Idan ba a manta ba, a baya na taba fada muku cewa rashin goge kwalliya a fuska sannan a kwanta bacci na haifar da fesowar kuraje, don haka a sami lemun tsami sannan a hada da man dogon yaro a sami auduga a rika goge fuskar da hadin har sai kwalliyar ta fita tsaf kafin a kwanta bacci.

==> Samin farin hakura: A sami ‘baking soda’ sannan a kwaba shi da ruwan lemun tsami. A dauko magogin hakora sannan a rika lakutawa ana gogawa a hakora. Yin hakan na sanya hasken hakora sosai musamman ga masu hakoran da suka riga suka dafe kuma suka canza launi.


==> Hasken fata: lemun tsami na dauke da sinadarin bitamin C don haka yawan amfani da shi a fata na dada hasken fata. Amma ana son amfani da man SPF idan ana yawan amfani da lemun tsami a jiki ko fuska. Yawan amfani da shi na sanya rana ta rika dakar fuska amma idan an sami man SPF ana shafawa kafin a fita, hakan na hana rana yi wa fatar illa.
Tura Zuwa:

Yadda ake girkin ‘Chicken Curry’

Yadda ake girkin ‘Chicken Curry’

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani nau’in girki da idan aka yi tabbas za a samu canjin dandano a gida. Shin da mene ne ake cin farar shinkafa a gidanku? Inji dai ba da miyar dagedage ba ce kawai? In ko haka ne har yanzu da sauranku a girki, sai a matso kusa a dauki sabon darasi. Miyar ‘Chicken curry’ dai miya ce ta kasar Indiya wadda ake hadawa da shinkafa domin kara dadi da gardi da kuma dandano.

Abubuwan da za a bukata

1.          Kaza
2.          Kori
3.          Bata
4.          Nono
5.          Tafarnuwa
6.          Citta
7.          Albasa
8.          Karas
9.          ‘Peas’
10.      Koren wake
11.      Magi

Hadi
Idan Uwargida ta wanke naman kaza tsaf kamar yadda muka yi bayani a baya yadda ake cire karni, sai ta yayyanka kanana sosai yadda za ta raba fatar da kashi sannan ta ajiye a gefe.

Sai ta dora tukunyarta mara kama girki (nonstick) sannan ta zuba bata ko man zaitun isasshe sannan ta zuba naman kazar da ta riga ta yayyanka a ciki ta yi ta gaurayawa har sai hadin ya fara nuna sannan ta dauko kori mai kyau mai kuma kanshi ta zuba kamar cokali biyu sai ta ci gaba da gaurayawa.

Sannan ta dauko albasa kanana ta watsa tare da jajjagen attarugu da tafarnuwa da citta ta zuba sannan ta debo nono ko madara mara sukari ta zuba a ciki ta ci gaba da gaurayawa sannan ta zuba magi ta dan rufe na tsawon minti biyu sannan ta sake budewa.


A wannan karon za ta zuba yankakken karas da koren wake sannan ta gauraya ta rufe. Bayan minti daya sai ta zuba ‘Peas’ ta ci gaba da gaurayawa sannan ta sauke. Sai a zuba a kan farar shinkafa a ci.
Tura Zuwa:

Yadda Ake Gyaran fata da kankana

Yadda Ake Gyaran fata da kankana
Yadda Ake Gyaran fata da kankana

Kankana na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan dake dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin fata da kuma rage tsufar jiki domin tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a magudanar gumi a fata wanda yawanshi ke haifar da fesowar kuraje da dama. Don haka, amfani da kankana a jiki na da matukar mahimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin yin amfani da kankana domin samin fata mai laushi da kuma sheki a kodayaushe:

==> Kodewar fuska: markada kankana tare da gurji sannan a rika shafawa kamar sau biyu a rana na matukar magance wannan matsalar. Sannan za’a iya markada kankanar zalla sai a dauko auduga ana tsomawa ana shafwa a fuska sannan a barshi ya bushe na tsawon mintuna goma sha biyar. Za’a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode. Amma abu daya nake so a yi amfani dashi a cikin ababen da na lissafo.

==> Domin yankwanewar fata: A markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika shafawa a inda fatar ke yankwanewa sau biyu a rana. A samu kankana da ruwan lemun tsami da sukari sai a hadasu guri daya. Kafin sukarin ta narke sai a rika dirzawa a inda fatar ta yankwane domin mikar da fatar.

==> Rage shekaru: A samu kankana da man zaitun da kindirmo da kuma kwanduwar kwai sannan a kwaba a rika shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau mai inganci. Za’a iya markada kankana sannan a samu ayaba a kwaba sannan a hadasu guri daya sai a rika shafawa a fata. A samu markadaddiyar kankana da madara da kuma fiya sannan a kwaba a rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.

==> kurajen fuska: a sami kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a tafasa ruwa a zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi.


==> Gautsin fata: a markada kankana sannan a zuba mata man ridi da na kwakwa sai a shafa a fata a barshi ya kai tsawon mintuna ashirin sannan a wanke.
Tura Zuwa:

Girkin nadadden nama

Girkin nadadden nama
Girkin nadadden nama

Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatan alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka nadadden nama. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma iya sarrafa girki dabandaban. Don haka dole ne mace ta dage wajen taka rawar gani a harkar girki tare da koyon kowane irin salon girki. Nadadden nama dai ana iya cin sa a kowane lokaci walau da safe ko da rana ko kuma da dare.

Abubuwan da za a bukata:

·              Namar karamar dabba
·              Man zaitun
·              Garin tafarnuwa
·              Garin citta
·              Gurji
·              Garin masoro (black pepper)
·              Barkono
·              Kori
·              Latus
Hadi:

A samu danyen naman rago wanda bai cika maiko ba. Sannan a yayyanka da fadi sosai kamar tabarma. Sannan a samu kwano a zuba garin tafarnuwa a ciki sannan a zuba garin masoro da barkono da garin citta da kori sannan a zuba man zaitun sai a kwaba ssosai.


A yayyanka gurji salasala a ajiye a gefe. A samu cokali ana dibar hadin man zaitun ana shafawa a kan naman. A zuba hadin isasshe sannan a dauko salan gurji ko latus a shimfide shi a kai sannan a yi masa nadin tabarma. Sai a dauko tsinken sakace hakori ‘toothpick’ a soke naman da shi yadda nadin ba zai warware ba sannan a saka a na’urar gashi a gasa na tsawon minti 30 zuwa 35.
Tura Zuwa:

Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?

Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?
Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?

Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa daku cikin sabon cikin shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar duniyan fasaha, insha Allahu yau zamu tattauna game da yanda password naka yake da yanda ya kamata ya zama, Ya ka ke rubuta password dinka a akwatin Email din ka? Ko kuma na facebook ko kuma twitter da duk dai wani shafin internet da kake shiga. Idan har kai ma’abocin kokarin rubuta lambobi masu sauki ne kamar 123456, ko kuma 98654, ko kuma kana amfani da sanan suna ne wajen password din ka kamar salisu, Ibrahim, ko kuma kai mai son saka sunan masoyiyarka ne kamar Fatima, amrat, beebah ko Aisha, ko kuma kai ma’abocin rubutun kalmomin soyayya ne kamar iloveyou, ko kuma fatimamylove ko kuma thankyou, to ina tabbatar da cewar wannan password din naka zai zama mai sauki wajen ganowa ko bai zai yiwa hackers wahalar shiga ba domin sacewa ko kuma aika maka da virus cikin shafukanka ba.

Ga yadda ya kamata ka rubuta password dinka

·              Karanci harrufa goma (10)
·              Ya kunshi kananan harrufa da manya a cikin sa
·              Ya kunshi alamomin rubutun na musamman
·              Ya kasance akwai lambobi a cikin su
·              Kada ya kunshi sunan masoyi, ko mahaifa da makamantansu
·              Kada ka yi amfani da sanannun kalmomi, kamar iloveyou, ihateyou, ihateu, da makamantansu
·              Kada kayi amfani da lamban wayarka ko na wani
·              Kada kuma ka yi amfani da ranar haihuwarka kamar, oct1977.

Ga misali

Dun!yanfasafaAbbaGana@er6969 – Wannan password yayi karfi sosai.

To ka yi la’akari idan ka kirkiri password dinka da wannan hada hade ya kake gani?

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *