A ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotu dake Abuja, ta daga sauraron shari’ar Uwar Maryam Sanda, Maimuna Salihu da ake tuhuma da yin sama da fadi da kudaden bankin Aso Sabings and Loan a lokacin da take rike da mukamin Babbar Daraktar bankin har zuwa ranar 5 ga Watan Disamba.
Muhitin Alkalin ne ya shaidawa lauyoyi da manema labarai haka yana mai cewa alkalin yana halartar wani kwas ne wadda hakan ya tilasta dage zaman sauraren karar a wannan ranar. Koda shike wakilinmu ya ruwaito cewa Maimuna ba ta halarci kotun ba.
Tun da farko Hukumar ICPC ce ta gabatar da Maimuna Salihu a gaban katun bisa zargin karkatar da wadansu kudade mallakar bankin da take shugabanta. Kakakin hukumar ta ICPC, Rasheedat Okoduwa ta bayyana cewa “Mun shigar da wannan kara ne a gaban Alkalin babban kutun tarayya dake Jabi a Abuja, Mai Shari’a M.A Nasir, inda ake tuhumar ta da sayar da wasu filaye har uku a Gundumar Jahi masu lambobin 2432; da 2433; 2434 akan kudi naira miliyan 57 a madadin Bankin Aso, amma sai ta ki maida kudin. Haka kuma ana zarginta da rubuta kalaman karya da jami’an hukumar ICPC,” in ji ta.
Maimuna Salihu dai ita mahaifiyar Maryam Sanda, wacce ake zargi da halaka mijinta har lahira, sakamakon wadansu sakonni da ta gani a wayarsa kwanakin baya, wacce ita ma wannan kotun ta bada umarnin tsare ta a kurkukun Suleja har zuwa ranar 7 ga Watan Disamba mai zuwa don ci gaba da sauraron karar.
No comments:
Post a Comment