Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Ana so uwar gida ta kula da gabanta musamman ga wacce tayi sabon haihuwa. Barin gaba (farji) ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen mai gida, uwar gida kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi. Masana ilimin kiwon lafia da jima'i sun ce duk lokacin da aka yi jima’i da mace farjin ta yana kara fadi shi kuma azzakarin mai gida yana rage girma. To kinga nasa na rage girma na ki kuma yana kara fadi, rashin kula da kuma neman mafita a hakan yasa maza da dama suke ganin matayensu a matsayin tsofaffi ta bangaren jima'i. Haka kuma kema uwar-gida rashin kula daga wajen maigidan naki takansa kema ba kya jin gamsuwa sosai a duk lokacin da kuka gabatar da ibadan aure (jima'i) Don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin ya za ma rago. Kuma ba kowane namiji ba ne zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba hakama ba kowace mata bace zata iya gayawa maigidanta ba rashin gamsuwar ta ba. Don haka uwargida da maigida sai mu kula.
Ga wannan hadi ga uwar gidan:-
·        Farar albasa
·        Kanunfari
·        Citta
·        Balmo
·        Barkono
·        Rihatul hulbi.

Sai ki hada su waje daya ki mayar da su kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum. Insha Allahu Uwargida da maigida zakusha mamaki, domin kuwa gabanki zai cike yayi cif-cif kuma zaki dawo tamkar sabuwar budurwa ga maigidanki.

Bayan haka ma, za ki iya samun zogale mai kyau sosai, amma danyen ganyen, ki wanke sosai, ki sa a Blender, ki markade shi, har sai ya yi laushi, har ki ga yana yauki, sannan ki tace shi sosai. Bayan kin tace ruwan, sai kuma ki nemo madarar gwangwani na ruwa, misali irin madarar PEAK (na ruwa), ki juye a ciki, ki dan saka zuma, haka za ki rika sha a kai a kai. a kai a kai.
Maigida ma za ki iya masa hadi:-
·        Muruci
·        Saiwar haukufa
·        Namijin goro
·        Hanno
·        Rihatul hubbi
Sai ki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau ana sha. Sannan ku nemi dabino a daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.
Insha Allah za a samu biyan bukata. Allah ya taimake mu amin.


Tura Zuwa:

Yanda ake gyara nono cikin sauki - Gyaran Nono

Yanda ake gyara nono cikin sauki - Gyaran Nono

Yanda ake gyara nono cikin sauki - Gyaran Nono                               
Assalamu Alaikum Yar’uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muka daga zauren nan na Duniyan Fasaha insha Allah yau zamu waiga ne izuwa gareku mata, nata samun sakonnin tambayoyi daga gareku masu sauraro akan cewa yaya ake gyaran nono wasu na tambayan cewa nono na yana yawan kwanciya yaya zanyi koma yaya tambayar take in dai ta shafi bangaren nono ne insha Allah yau na zo muku da amsar wannan tamabayar.  Nono babbar kadara ne kuma kyawunsu yana kara miki kyau da kima gurin miji idan sun lalace kuma ke da kanki baki son ganinsu balle mijinki saboda haka dole ki dinga kula dasu wannan hadin zaisa su ciko idan sun yamushe zasu tsaya su cika suyi bubul bubul suyi kyau ki samu waken soya ki cire dattin ki sa a wuta ki soya sama sama ammafa bada mai bahakanan zaki saka shi cikin tukunyar zakijiyana kanshi to saiki sauke idan yasha iska kidaka yayi gari saiki samu ridi ki soya sama sama shima ki daka yayi gari to yar’uwa kullum da safe ki diba wannan garin waken soya ki zuba a cikin ruwan zafi ki shanye sannan ki samu kunun aya mai kyau ki zuba garin ridi ki dinga sha sau 3 a rana,  wancan na waken soya sau daya kafin kici komai,na kunan aya kuma sau 3 saiki dinga shafa man ridi a nonon wannan hadin yana da kyau gaskiya dan zakiga canji domin wannan kayan dana lissafa sune abincin nono idan kina sha zakiga kamar taki ake zuba musu zasuyi kyau suyi bulbul kuma jikin ki ma zaiyi kyau har sai kin mun babban kyauta, Allah ya bada sa.a

Tura Zuwa:

Kwalliyar da amarya ya kamata ta yi kafin ranar biki -Gyaran Amare

Kwalliyar da amarya ya kamata ta yi kafin ranar biki -Gyaran Amare

Kwalliyar da amarya ya kamata ta yi kafin ranar biki -Gyaran Amare

Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa daku cikin sabon shirin namu wanda muke kawo muku a shafinnan na Duniyan Fasaha insha Allah yau hangenmu zai komane izuwa ga amare inda zamu tattauna game da gyaran da amarya ya kamata tayi kafin daurin aure, tare da wasu shawarwari wanda amarya ya kamata tabi wajen gyaran jiki,  hakika Kwalliyar da amarya ya kamata ta yi kafin ranar biki suna da yawa dan gudun dogon surutai zan zayyano wasu masu amfani daga cikinsu. ‘ya mace babbar rana ce a rayuwarta na jin dadi kuma a wannan ranar kowa yana son ya ga irin kwalliyar da za ta yi. Koda ’yan gidan amaryar ne suna son kare mata kallo a wannan ranar. Wasu amaren tsabagen son gyaran jiki har gyaran ya yi yawa ya feso musu da kuraje a fuska ko da ba su da wadannan kurajen ko kuma kaga wasun su saboda kwlliyar tayi yawan gaske sai ka kamanninsu ya juya wasun su har kama suke yi da dodo, Don haka ne a yau muka kawo muku yadda amaryar gobe za ta kimtsa kanta kafin ranar biki.

·        Amaryar gobe ta kasance tana yawan shan ruwa, sirrin hakan shi ne kar jikin ya yankwane. Kuma yana da kyau ta kasance mai shan kankana sosai, domin gyaran fatar jikinta da kuma cin su latus da ‘ya’yan itatuwa.

·        Ana son amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura watanni uku. Ta san irin mayukan da za ta shafa da kuma irin abincin da za ta ci.

·        Idan amaryar gobe ta wuce shekaru 20, yana da kyau tana kwaba fiya da zuma tana shafawa a fuskarta domin warkar da kananan kurajen fuska kafin ranar biki.

·        Idan shekarunta sun wuce 25, yana da kyau ta kasance cikin yin dilke, domin cire dattin fuska. Kuma hakan na rage mata shekaru a fuskanta.

·        Yana da kyau ta sayi magungunan turawa na gyaran jiki (supplement). Wadannan magungunan na dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma na omega3, wanda aka fi samu a man kifi. Wadann magungunan na sanya fata sulbi da laushi.

·        A samu mai mai kyau tsayayye, wanda za a rika shafawa na tsawon wadannan lokuta. Ana shafa wannan nau’ukan man a kalla sau biyu a rana.

·        Yana da kyau amaryar gobe ta samu lokacin yin bacci sosai, kuma ta rage shiga rana domin gyaran fata da kuma hutu.


·        Tana amfani da soson hoda mai tsafta ba mai datti ba, domin rage haifar da wasu kurajen fuskar.

·        Domin samun fata mai haske a samu kurkum da ruwan lemun tsami da kuma man zaitun kamar rabin cokali karami da madara sannan ta shafa a fuskanta na tsawon rabin awa, sannan ta wanke. A kullum za ta rinka yin hakan safe da yamma lallai za a ga canji.

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive