Hafsat Bello Danmaisoro,’yar asalalin jihar Kano, tayi makarantar firamari a makarantar ‘Yandutse Firamari School dake kwaryar Kano, daga nan ta zarce makarantar “Crescent International School” inda ta samu kammala karatun sakandire, daga bisani ta halarci Jami'ar Bayero, inda ta samu digirin farko a fanin karatun aikin jarida.
Daga nan ne kuma ta wuce kasar Amurka, inda ta kammala digirin ta na biyu, a fanin aikin jarida na sadarwar zamani "Masters in Professional Communication and Digital Media" a makarantar “Texas Southern University” dake garin Houston. Babban abunda yasa tazo kasar Amurka karatu, bai wuce kwadayin samun kwarewa a fanin aikin jarida ba, da samun damar taba kowanne irin kayan aiki na zamani ba tare da wani nakasu ba. Bude ido kuma da sanin abinda duniya ke ciki shima wani dalili ne babba.
Babban abinda ya bata sha’awar aikin jarida shine, ganin yadda mata basa yin wannan aikin, sunfi ganewa aikin likita ko lauya, kuma ina ganin a kowane aiki ya kamata ace akwai mata wadanda zasu wakilci sauran mata, musamman inda akayi la’akari da yadda rayuwa take a Arewacin Najeriya. Tunda ba ko ina ne maza suke shiga ba.
Na biyu kuma mahaifina ma dan jarida ne, nakan sa ido akan yadda yake gudanar da ayyukan shi, abubuwan da ya keyi kuma yana bani sha’awa kwarai hakan yasa naga cewar nima zan iya yin wannan aikin na jarida.
A iya ganin na, Ina ganin ya kamata ace iyaye su farga, su san cewa yanzu zamani ya canza, al’ummah bata bukatar marasa ilimi a cikin ta, don haka su bawa yaran su mata goyon baya, wajen samun ilimin boko domin taimakawa alumma baki daya.
idan aka duba za’a ga matsaloli da yawa rashin ilimi ke kawosu, musamman a kasa irin Najeriya da ma sauran kasashe a duniya. Idan kuwa akace mutane nada ilimi, za’a ga komai yazo cikin sauki. Kuma ya kamata ace kowace mace tanada gudunmawar da zata bayar a gidanta da alumma. Banda wannan akwai halin rayuwa, akwai cuta, akwai mutuwa, idan mace bata da ilimi, babu shakka bazata iya taimaka ma ‘ya’yata ko mijinta ba, ballae ayi maganar al'ummah baki daya.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment