Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yanda ake goge sakon da aka tura bisa kuskure a WHATSAPP koda ya isah

Yanda ake goge sakon da aka tura bisa kuskure a WHATSAPP koda ya isah


Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabo shirin namu wanda yake zuwa muka kai tsaye daga mujallar Duniyar Fasaha, Insha Allahu yau zamu koyi yanda ake goge sakon da ake tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wajen wanda aka tura wa.

Tura Zuwa:

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A zamanin namu na yanzu mutane da dama suna aiki da blog ne kawai da manufar samun kudi, ko hanyan samun kudi wasu kuma suna aiki dashi ne saboda hanya ce da zai taimaka sosai wajen kasuwanci. 

Haka kuma ma danfara sukan samu hanyar danfaran mutane saboda yanda mutane suka sha’afa da aiki dashi. Sau da dama mutane sukanyi korafin cewa basu samun mutane suna ziyartan shafinsu wanda sun bi duk wata kayatacciyar  hanya daya dace a abi dan ganin mutane suna da masaniya a kanta. 

Abu daya kamata mu sani shine yawan sa ran samun kudi ta hanyan yanar gizo yana daya daga cikin abubuwan dayake janyo rashin ziyartan mutane saboda bazaka sa ko kayi abunda ya dace ba kawai matsalar ka kaga dubban mutane suna ziyar tan shafinka wanda hakan ba karamin abu bane kuma ba abun gaggawa bane. 

Yana da kyau ka kasance na musamman in kana son cimma manufarka na zama daya daga cikin shahararrun masana kan yanar gizo ko kuma zama daya daga cikin hamshakan mutane da suke samun kudi ta hanyan yanar gizo. 

Maganar gaskiya, akwai dubban hanyoyi da ake bi wajen ganin shafi ya riske mutane da dama abu na farko ya kunshi abubuwa masu inganci, duk da cewar ba bangaren nan zan tabo ba yau zan mayar da hankali ne game da asalin shi shafin wato sarki da kansa wanda shine “abun dake ciki” ko yaya shafinka ya kasance misali gwani wajen sura (design) yawan sa a wajen mutane a karshen mako abinda ke cikin shafinka ne zai sanar da mutane manufanka,

Tura Zuwa:

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}  A hakikanin gaskiya suna da yawa amma ga kadan daga ciki 

RIKO


Riko shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba uwargida ta riki maigida a xuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita daga zuciyar miji duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sane ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi

Tura Zuwa:

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A wasu lokutan mukanji sunayen wasu abubuwa daga yan uwa da abokan arziki ko kuma daga yanar gizo wadda kan zamo mana sabo sabili bamu taba jinsa ba ko kuma wasu sa’an mukan ji mutane suna yawai ta ambatan sunayen, wadda a hakikanin gaskiya bamu sansu ba balle mu san yadda suke aiki. 

Tura Zuwa:

Yadda ake girka kazar Indiyawa

Yadda ake girka kazar Indiyawa
yadda ake girka kazar indiyawa

Yadda ake girka kazar Indiyawa


Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da su a kan abincin kasashe waje.

Abubuwan da za a bukata
·        Man zaitun
·        Albasa
·        Kori
·        Madara (nonon da aka tafasa)
·        Gishiri
·        Dakaken masoro
·        Heaby cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke girke)
·        Kaza daya
·        Timatir guda daya.
·        Ganyen kori.

Hadi

A wanke kaza sannan a silala ta da kayan kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya.

Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai sai a ci gaba da juyawa.


A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya!
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *