YADDA ZA A RAGE ZUBAN GASHIN KAI
Yadda za a rage zuban gashin kai...
Sallama a gare ku mata. A yau na kawo muku abubuwa da dama wadanda za a yi don rage zubar gashin kai, musamman ma a lokutan sanyi. Abincin gina jiki da sinadarin bitamin C da na B da yawan shan ruwa da rage shan kayan maye da sinadarin bitamin E na janyo gashi sosai, kuma yana rage zubarsa a ka. Don haka, cin abinci mai kyau na janyo gashi kuma na hana zubarsa. Akwai abubuwa da dama wadanda in ana amfani da su za a samu canji. Kada a manta abu daya kawai za a zaba a yi amfani da shi domin yawan sanya abubuwa da yawa a gashi na tsinka shi. A sha karatu lafiya.
· A samu albasa sai a yayyanka kanana, sannan a matse ruwan. A shafa a fatar ka a duk sa’adda aka zo wanke kai na tsawon mintuna 15 kafin a wanke da man wanke gashi.
· A samu man amfuna sannan a shafa a fatar kai, na tsawon mintuna 20 sannan a wanke da ruwan dumi da kuma man wanke gashi.
· A samu ruwan kwai a cire gwaid uwar cikin, sannan a zuba man zaitun da zuma a kwaba sosai a shafa a fatar gashi da kuma gashin. Sai a bari na tsawon mintuna 20 sannan a wanke da ruwan sanyi da kuma man wanke gashi domin hana karni.
· Ana amfani da man kwa-kwa idan anzo kitso, domin yana magance amosanin ka. Kuma yawan amosanin ka na zubar da gashi.
· Man zaitun na magance amosa nin ka da kuma sanya gashi laushi da sheki.
· Man fiya na hana zubar gashi, kuma yana ratsa fatan kai sosai yadda gashi zai yi tsayi da kuma laushi.
· Amfani da man ‘castor’ na da muhimmanci sosai, domin yana hana zubar gashi. Kuma yana sanya gashin da ya zube kara tsirowa ba tare da daukar tsawon lokaci ba.
No comments:
Post a Comment