Fatima ta kasance mace guda ‘yar asalin garin Hadejia wacce ta samu gurbin aiki a hukumar yaki da fasa kwauri a lokacin da aka dauke su aiki a lokacin, wannan yasa abokan aikin nata suka fara kiran ta da Iron lady, wato mace da kamar maza, inji Fatima Mustapha.
Matashiya Fatima ta ce a lokacin da ta yi karatu ta so ta karanta harkar kasuwanci ne domin a cewarta burinta a wancan lokaci bai wuce ta ga kanta tana hadahadar kasuwanci ba.
Amma ta ce hakar ta bata cimma ruwa ba domin sai Allah ya sauya mata da wani aikin, ta zama mace tilo ‘yar arewa da ta jurewa haraswar aikin kwastam. Ta kara da cewa bayan kammala jami’arta ne wata rana tana karanta jarida ta ga tallar aikin kwastam, kuma a matsayinta na ‘yar arewa bata yi kasa a gwiwa ba wajan gwada sa’arta.
Fatima ta kara da cewar aikin lallai yana tattare da kalubale da dama, mussaman ma yadda ta yi tunani ba haka ta gani ba, kama da horon da aka basu , wanda sojoji ke horas da su, aiki ne da dole sai an sanya kayan sarki na tattare da matsaloli da dama.
No comments:
Post a Comment