Sana'ar talla tana da illoli masu ɗunbun yawa ga rayuwar mata musamman wanda sun munzalin yin aure.
A mafi akasin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla ba; a bakin kasuwa ko makaranta, tasha ko masana'anta, wureren leburori ko kan titi, gidajen kallon kwallo ko sinima, filin kwallo ko gidajen dambe.... babu dare babu rana.
Babban abunda zai baka mamaki
shine, yawancin abubuwan da suke sayarwa basa wuce abun Naira dubu daya ko dubu
biyar, amma yarinya zata bar gidan iyayenta tun da safe har zuwa dare da sunan
talla.
Mafi muni shine, wasunsu har lunguna suna shiga da katti da sunan talla. Illolin talla sun hada da:
- Talla tana kawo fiyade har ta kai ga taɓa mutuncin ƴa'ƴa mata,
- Talla tana hana ƴa'ƴa mata sallah a kan lokaci,
- Talla tana hana ƴa'ƴa mata karutu (na addini ko boko),
- Talla tana ɓata tarbiyyan ƴa'ƴa mata,
- Talla saka ƴa'ƴa mata suna kamuwa da cututtuka masu hatsarin gaske.
- Talla tana saka fitsara da rashin kunya ga ƴa'ƴa mata.
- Talla tana saka rashin kamun kai da rashin sanin ciwon kai ga ƴa'ƴa mata.
- Talla tana kaskantar da mace daga kima da daraja da aka san ƴa'ƴa mata suna da shi.
Allah ka shiriyar damu baki ɗaya.
No comments:
Post a Comment