Lokaci yayi da matasa zasu farga su nemi ilimin ko sana’ar hannu domin zama masu dogaro da kai don huce takaicin zaman duniya inji Malama Rayya Abba Fagge.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA a yau a Kano, inda ta bayyana cewa jajircewa da sadaukar da kai ne ya kai ta ga matsayin da take ciki a yanzu da goyon bayan ‘yan uwanta da mai gidan ta.
Malama Rayya, ta ce babban muhimmin abu dai a nemi ilimi inda ta ce a mafi yawan lokuta daga cikin wasu kwasa-kwasan da ake karantawa a yanzu ba zai lallai mutum yayi aiki a wannan fannin ba.
Malam Rayya ta bada misali da cewa ta karanci harshen Hausa amma a yanzu haka tana aiki a asibiti a fannin bada shawarwari ga masu dauke da cutar HIV dangane da shan magungunasu da sauransu.
Daga karshe ta ja hankalin matasa da su jure duk runtsi da kalubalen rayuwa a yayin da ake fafutukar nema, tare da tabbatar da an sami sana’ar hannu.
No comments:
Post a Comment