Lura da lebba na kara wa kwalliyarki armashi, don haka ya kamata ki mayar da hankali wajen lura da lebbanki. Tsagewar lebba na kawo nakasu ga murmushinki ko kwalliyarki. Wani lokaci yanayi na haifar da tsagewa ko bushewar lebba, ko kuma kawo nakasu ga lebba. Don haka ne muka taho miki da hanyoyin da za ki bi wajen lura da lebbanki. Muna fata za ki bi bayanan sau da kafa, sannan kuma ki yi amfani da su. Goge Lebba
Hanya ta farko da za ki lura da lebbanki ita ce, ki rika goge lebbanki da dan karamin buroshin yara. Kafin ki fara goge lebbanki ana so ki tsoma buroshin a cikin ruwa mai tsafta, ana so ruwan ya kasance mai dumi ba mai sanyi ko zafi ba. Wanke lebba da man zaitun ko kuma ruwa da aka jika soda ko toka na kare lebba daga kwayoyin cuta. Man lebba
Bayan kin wanke lebbanki da man zaitun sai ki dauraye lebbanki da ruwa mai dumi, daga nan sai ki shafa man lebba wanda ake kira ‘Lip Balm’. Wadannan man lebba suna hana lebba bushewa. Wani abu da ke bada mamaki shi ne, ko da an shafa man lebba sai ka samu lebba suna saurin bushewa, hanyar da za ki magance wannan ita ce, ki samu man lebbe da ke kunshe da sinadarin ‘bee wad’. Wannan sinadari na bee wad yana kare lebba daga bushewa.
Guji lashe lebba da harshe
Yawancin mata sukan yi amfani da harshensu wajen sanya yawu a lebbansu, don magance bushewarsu, ko kuma su rika cizon lebbansu da hakora, yin hakan yana sanya lebba su yi tauri ko su rika tsagewa. Shafa jan-baki na hana cizon yatsa. Shafa man da ke sanya danshin lebba Yana kyau bayan ki gama goge lebbanki da karamin buroshin yara, ko kuma bayan kin gama wanke bakinki da man zaitun ko da ruwan soda ko na toka, sai ki shafa man da ke sanya laushi da danshin lebba. Shan ruwa mai tsafta a-kai-a-kai yana hana bushewar lebba.
No comments:
Post a Comment