Girkin koda
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da
fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka koda. Akwai hanyoyi da
dama wadanda mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin
daban yake. Don haka yana da kyau a kasance an karanta wannan shafin domin gano
sirrin girki da kuma canza salon girki a kodayaushe, domin yara su rage kwadayi
a makwafta.
Abubuwan da za a bukata
- koda
- Albasa
- Tumatir
- Garin
tafarnuwa
- Magi
- kori
- Garin
citta
- Attarugu
- Man gyada
- Koren
tattasai
Hadi
A wanke koda ta fita tas. Sannan a yayyankata
kanana, sai a sanyata a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a
rufe.
Idan ya fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki da zuba yankakken
tumatir da magi da garin tafarnuwa da kuma garin citta kadan sosai.
Sannan a
rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a cigaba da juyawa
har sai albasa da tumatar da kuma attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a
kwano.
Sai a yayyanka danyen albasa da koren tattasai a zuba a kan kodar domin
kawata girkin. Za a iya cin wannan girkin da dafadukar shinkafa ko kuma farar
shinkafa da jus din lemun zaki. A ci dadi lafiya.