Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Illoli Goma(10) Da Rashin Shan Isasshen Ruwa Ke Haifarwa Ga Lafiyar Jiki

Illoli Goma(10) Da Rashin Shan Isasshen Ruwa Ke Haifarwa Ga Lafiyar Jiki

Duk da cewar muna sane da muhimmancin da ruwa ke takawa wajen tabbatar da kasancewar mu cikin koshin lafiya, kwanciyar hankali da kuma walwala. Sai dai kuma da yawa daga cikin mutane ba su san adadin ruwan da ya kamata su na sha ba a lokaci zuwa lokaci. Wannan yasa yau Mujallar Duniyan Fasaha ta taho muku da wasu daga cikin illoli guda goma(10) da rashin shan isasshen ruwa ke haifarwa ga lafiyar jikinmu.

Tura Zuwa:

Yadda Shan Ruwan Zafi Ke Magance Cututtuka Guda Sha Uku 13

Yadda Shan Ruwan Zafi Ke Magance Cututtuka Guda Sha Uku 13

Shan ruwa dayawa nada matukar muhimmanci ga lafiyar jikinmu, sai de ta dayan bangaren kuma yawan shan ruwan sanyi yakan iya zama babbar matsala, domin kuwa a duk lokacin da muka sha ruwan sanyi bayan chin abinci yakan je kai tsaye ya toshe magudanar jinin jiki wadda hakan kan janyo cututtuka bila adadin kamar irinsu ciwon sugar wadda aka fi sani da Diabetes a turance, ciwon daji wato cancer da dai makamantansu. Haka zalika ruwan sanyi yakan zama tamkar guba a cikin jikinmu mussamman ga wayenda basu iya rayuwa ba tare dashi ba. Ruwan sanyi na tattare da illoli masu yawan gaske wadda zamuyi bayani a wasu makonni masu zuwa. 

Tura Zuwa:

Wasu Abubuwa Da Mukeyi Wadda Ke Bude Kofofin Satar Account Namu Na Facebook

Wasu Abubuwa Da Mukeyi Wadda Ke Bude Kofofin Satar Account Namu Na Facebook

Satar account a facebook wadda aka fi sani da hacking a turance ya zama tamkar ruwan dare domin kuwa yana da matukar wiya ayi kwana biyu ba tare da ganin wasu alamun sacewar account ba, idan ba’a yi wa mutum ba za’ayi ma dan uwansa ko kuma wani daga cikin abokai da ake dasu a facebook. Sau da dama mutane su kanyi korafin wannan matsalar wasu kuma su kanyi tambaya shin kamfanin facebook na sane kuwa da wannan matsalar da ake fama da ita?

Tura Zuwa:

Abubuwa Goma (10) Da Ke Haifar Mana Da Ciwon Koda

Abubuwa Goma (10) Da Ke Haifar Mana Da Ciwon Koda

Tare Da Muhammad Abba Gana (Jikan Marubuta)

Ciwo daga Allah ne haka zalika magani daga Allah ne, Allah yakan daura wa mutum da yaso ciwo ba wai dan baya kaunarsa ba, fa che dan ya jarraba imaninsa da kuma hakurinsa. Haka kuwa ta dayan bangaren domin Allah bai daura maka komai ba hakan baya nufin cewar yafi sonka fiye da kowa ko kuma kai na musamman ne a garesa.

Tura Zuwa:

Yadda Za’a Cire Tallar Manhaja Da Suke Fitowa A Menu Na Salulan Android

Yadda Za’a Cire Tallar Manhaja Da Suke Fitowa A Menu Na Salulan Android


Talla na daya daga cikin tsari mafi sauki da mutum kan iya bi wajen sanar da al’umma yadda ingancin kayansa yake da kuma yadda zai taimaki mutane a ayyukansu na yau da kullum. 
Tura Zuwa:

Yadda Za’a Fita Daga Duk Wani Tsari Na Mtn Da Suke Cire Kudi

Yadda Za’a Fita Daga Duk Wani Tsari Na Mtn Da Suke Cire KudiTare da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}

Duk da cewar layukan sadarwa da muke aiki da su a wasu lokutan sukan mana zanba ta hanyar cire mana kudade ba tare da kwakkwaran dalili ba haka zalika a wasu lokutan mukan kuma iya taimaka musu kwarai da gaske ta hanyar shiga wani tsari ba tare da sanin ingancinsa ba balle sanin rashin ingancin. 

Tura Zuwa:

Yanda ake goge sakon da aka tura bisa kuskure a WHATSAPP koda ya isah

Yanda ake goge sakon da aka tura bisa kuskure a WHATSAPP koda ya isah


Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabo shirin namu wanda yake zuwa muka kai tsaye daga mujallar Duniyar Fasaha, Insha Allahu yau zamu koyi yanda ake goge sakon da ake tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wajen wanda aka tura wa.

Tura Zuwa:

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A zamanin namu na yanzu mutane da dama suna aiki da blog ne kawai da manufar samun kudi, ko hanyan samun kudi wasu kuma suna aiki dashi ne saboda hanya ce da zai taimaka sosai wajen kasuwanci. 

Haka kuma ma danfara sukan samu hanyar danfaran mutane saboda yanda mutane suka sha’afa da aiki dashi. Sau da dama mutane sukanyi korafin cewa basu samun mutane suna ziyartan shafinsu wanda sun bi duk wata kayatacciyar  hanya daya dace a abi dan ganin mutane suna da masaniya a kanta. 

Abu daya kamata mu sani shine yawan sa ran samun kudi ta hanyan yanar gizo yana daya daga cikin abubuwan dayake janyo rashin ziyartan mutane saboda bazaka sa ko kayi abunda ya dace ba kawai matsalar ka kaga dubban mutane suna ziyar tan shafinka wanda hakan ba karamin abu bane kuma ba abun gaggawa bane. 

Yana da kyau ka kasance na musamman in kana son cimma manufarka na zama daya daga cikin shahararrun masana kan yanar gizo ko kuma zama daya daga cikin hamshakan mutane da suke samun kudi ta hanyan yanar gizo. 

Maganar gaskiya, akwai dubban hanyoyi da ake bi wajen ganin shafi ya riske mutane da dama abu na farko ya kunshi abubuwa masu inganci, duk da cewar ba bangaren nan zan tabo ba yau zan mayar da hankali ne game da asalin shi shafin wato sarki da kansa wanda shine “abun dake ciki” ko yaya shafinka ya kasance misali gwani wajen sura (design) yawan sa a wajen mutane a karshen mako abinda ke cikin shafinka ne zai sanar da mutane manufanka,

Tura Zuwa:

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}  A hakikanin gaskiya suna da yawa amma ga kadan daga ciki 

RIKO


Riko shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba uwargida ta riki maigida a xuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita daga zuciyar miji duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sane ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi

Tura Zuwa:

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A wasu lokutan mukanji sunayen wasu abubuwa daga yan uwa da abokan arziki ko kuma daga yanar gizo wadda kan zamo mana sabo sabili bamu taba jinsa ba ko kuma wasu sa’an mukan ji mutane suna yawai ta ambatan sunayen, wadda a hakikanin gaskiya bamu sansu ba balle mu san yadda suke aiki. 

Tura Zuwa:

Yadda ake girka kazar Indiyawa

Yadda ake girka kazar Indiyawa
yadda ake girka kazar indiyawa

Yadda ake girka kazar Indiyawa


Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da su a kan abincin kasashe waje.

Abubuwan da za a bukata
·        Man zaitun
·        Albasa
·        Kori
·        Madara (nonon da aka tafasa)
·        Gishiri
·        Dakaken masoro
·        Heaby cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke girke)
·        Kaza daya
·        Timatir guda daya.
·        Ganyen kori.

Hadi

A wanke kaza sannan a silala ta da kayan kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya.

Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai sai a ci gaba da juyawa.


A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya!
Tura Zuwa:

Alamar Insufficient Memory a Wayar Android: Meke haddasawa da kuma Yadda Za’a Magance Matsalar Cikin Sauki

Alamar Insufficient Memory a Wayar Android: Meke haddasawa da kuma Yadda Za’a Magance Matsalar Cikin Sauki


Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Insha Allahu yau zamu tattauna ne game da yar matsala wadda mutane da dama sukan fuskanta a wayoyin salulansu na Android daga lokaci zuwa lokaci wato sakon “Insufficient Space on Device” ma’ana babu isanshen waje a cikin waya wadda a mafi yawancin lokuta yana hana mutum tura abu ko saukarwa daga yanar gizo. 

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive