Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YANDA ZAKAYI WUTA WA KWAMFUTANKA (how to create light for your pc free)


Assalamu Alaikum Barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu insha Allah yau zamu nuna muku yanda ake kirkiran hasken wuta saboda amfani dashi a kwanfuta a sha kallo lafiya:............
Tura Zuwa:

ABUBUWA DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN SIYAN WAYA KO ANDROID(SMARTPHONE)ABUBUWA DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN SIYAN WAYA KO ANDROID(SMARTPHONE)

ASSALAMA ALAIKUM……..Barkan mu da war haka insha Allah yau zamu tattauna a kan abubuwan da ya kamata muyi la’akari dasu kafin mu canza waya ko kuma mu siya sabo, Android waya ne da ta cika gari a wannan zamanin wacce zai yi wahala ka samu mutum uku wadanda suke rike da waya amma kuma ba a samu mai irinsa ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina a fadin duniya, ga shi kuma kamfanonin da suke sarrafasu kullum kara fito da sababbi suke yi cikin kasuwa. Kodayake a irin tunani namu na bakaken fata kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna cewar wannan wayar tana da matukar kyau da kuma lafiya, wani lokutan kuma neman iyawa da bajinta da nuna isa shi ke sa mu mallaki waya wacce take da tsadar tsiya ba yin la’akari da me ke cikin wannan wayar ba ko kuma me wannan wayar zata iya yi mana nan gaba ba.
Wani abu kuma da yake daurewa jama’a da dama shine suna son su siya sabuwar waya, idan na samu kudi wace irin waya ya kamata na rike, ko kuma mene ne abin yin la’akari da shi idan ina son canza waya ko kuma sake siyan sabuwa. Amsoshin wannan tambayar ya danganta da me kake son yi da wayar ko cimma manufar wayan, domin wani yana yin la’kari da karfin wayar wurin rike wuta wato caji, wani kuma yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka wato clean camera a turance, wani kuma yana yin la’akari da karfin network da take da shi wato high network capacity, wani kuma yana yin la’akari da girman fuskarta waro screen size, da dai makamantan irin su. A cikin wannan darasi zan kawo mana abubuwa da jama’a suke yin la’akari da su wurin siyan wayar wato taba ka latsa wanda akafi sani da android ko smartphone a turance.

1-     KAMARA DAUKANSAUTI (CAMERA AND AUDIO RECORD)

Sauti da kamara Hakika wadannan abubuwa guda biyu sun karawa wayoyin tafi da gidanka daraja sosai, kusan a yanzu mutane da dama suna yin amfani da kamarar jikin wayoyinsu domin daukar shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi, wasan kwaikwayo da sauran makamantansu. Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan lokacin suke kara yin tsada, duk da cewar mutane da dama basu cika kiyaye haka ba. Kusan a yanzu akwai wayoyin da ake da su wadanda saboda karfi da kyau Yanayin hotuna da suke dauka hatta mawaka suna amfani da su wurin shirya wakokinsu. Haka yan jarida a wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin nado sauti da zasu iya kai rahoto da shi. Duk da cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma waya da kamara da kayan daukan sautin da ke jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan tafi da gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba kowace waya bace ta ciki inganci a kan haka. Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na hoto ba to ba sai ka sayi waya mai tsada ba.

2-    KAURI DA NAUYI (OHONE WIEGHT)

Kauri da nauyin waya abu ne mai muhimmanci sosai a lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet a turance. Kauri dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci sirantaka a wurin kayan computer bai cika bayar kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda haka ya danganta gare ka idan kana son kyau fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar waya ko tablet abunka. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin karfe ne saboda haka tun kafin kabar wurin siya ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata tayi nauyi.

3-    MANHAJOJIN (Operating System) DA WAYA TAKE AMFANI DA
SU (INSTALLED OPERATING SYSTEM)

Babbar Manhajar wato os a turance da take sarrafa komai da ke jikin waya shi ake kira da Operating System, shi yake lura da hatta maballan da kake tabawa wurin kunnawa da kashewa, shi yake lura da sauti da kalan da yake fita a wayar bai tsaya nan ba kusan shine waya saboda komai yana karkashin ikon sane. To lallai wurin siyan waya yana da kyau ka duba da kyau domin ka san wane irin manhaja ce a cikin wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin mu suka sani cewar wayoyin da muke rikewa suna da banbanci wurin gininsu da kuma wani company nine ya buga Kunga dai wayoyi idan ya zo ga maganar Operating System akwai na Android, sannan ga iOS, sai Microsoft Phone 7, sai Blackberry ga kuma webOS da Symbian, akwai java dukkan wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu sun dauka cewar waya ce. A a kamfani da yake yin karfe da kyan da suke jikin waya daban sannan manhajar da ake saka mata da ba. Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane sun fi sabawa da su a matsayin waya maimakon Babbar Manhaja ce.

4-    GIRMAN FUSKAR WAYAR (SCREEN SIZE)

A wurin siyan waya ko tablet mutane suna yin la’akari da girman fuskar wayar wato (screen). Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa ko a aljihunsa, wani kuma baya son ganin haka. To shi dai maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda yayi maka ba dole ba ne yayi wa wani. Amma dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar waya da barin ta cikin haske sosai na taimakawa wurin sanye caji da wuri.

5-    GIRMAN WURIN ADANA BAYANAI (FILE STORAGE CAPACITY)


 Mafi yawan kanfanonin da suke yin wayoyi da tablet a wannan zamanin suna kokarin ganin sun yi mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda zai baka dama domin a jiyar hotuna da rubutu da sauti da hotuna masu motsi wato video. Kodayake wadansu saboda yanayin yadda suke tara abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin abubuwa a ciki. To a nan yana da kyau ka sani wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada ramin kara ma’ajiya wato Memory, saboda haka idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa na tarkce ne sai ka nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman mazubi a cikinsu.

6-    KANA NAN MANHAJOJI (APPLICATION CAPACITY STORE)

Daya daga cikin abin wasu mutane da dama suke yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri kaza shin dawe application ne zan iya aiki ma;ana zai iya daukawa, kusan a wannan lokaci da muke ciki kasancewar wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin koyan yadda ake kirkiran manhajojinsu, yasa mutane da dama suke son siyar wayar Android. Amma kuma idan aka zo ga zafafan Manhajoji to sai muce manhajojin da ake amfani da su a waya kirar Apple sun fi shahara da kwarjini. Misalia shagon Apple akwai manhajoji dubu dari uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu da hamsin na kyauta da kuma siyarwa. Suma sauran manhajoji irin su Blackberry da makamantansu suma suna da shagunan da ake samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple da Android yawa ba saboda yanda ake yawan amfani da su a wannan zamamin namu.


            7-    KARFIN SHIGA INTERNET (INTERNET SPEED)


Kusan dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna zuwa da tsarin sadarwa maras waya wato wireless a turnce wanda ya ke basu damar iya kulla alaka tsakaninsu da ko kamfanin layukansu ko kuma hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma ofis da dai makamantansu. Irin wadannan hanyar da ake amfani da ita domin samun sinadarin shiga intanet ba tare da amfani da layin waya ba shine ta hanyar amfani da Wai-Fai (Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda zai sayi waya a wannan lokaci ya san cewar yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third Generation) ta wurin shiga intanet, a’a a wannan kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka tsallaka karni na hudu 4G. Wayoyin da aka yi a baya sun fara ne da 1G sai kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan wayoyin ba sa ba mutum damar shiga intanet da sauri, koda kuwa a inda mutum ya ke akwai network mai kyau da karfi. Daga baya suka shigo da 3G wanda yake bamu damar har kallon hotuna masu motsi (video) muke yi ba
tare da yana tsayawa ba. Saboda haka yanzu mafi yawan wayoyin da ake yi suna baka damar amfani da karfin network na 3G da 4G, sai a kiyaye idan an je siya.


       8-    DADEWAR BATIRI (BATTERY CHARGE RETAIN)


Lallai ko ba a fada maka ba kasan cewar batir yana da matukar muhimmamci a jikin waya domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan har batirin wayar baya dadewa ya zama shiririta. Shi yasa mafi yawan kamfanonin da suke kirkirar waya suka fi mayar da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da irin kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin suna yi sai ka samu kamfani yayi waya kuma cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai kama da wuta, amma dai suna iya kokarin su. Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta batirinsu har kaga waya tana iya kwana uku tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan muka sayi waya bama karanta takardar da take zuwa da ita. Wannan shine abubuwan da zan iya kawo muku wadanda sune abubuwan da ya kamata mu rika yin la’kari da su wurin sayin waya sabo koh canzawa.


Tura Zuwa:

Yadda za ki gyara jikinki da gishiri

Amfani da gishiri wata hanya ce ta gyaran jiki, alokaci guda yana kawar da gajiya da kuma bada kuzari. Tarihi ya nuna tun shekara ta 3150 kafin zuwan Annabi Isa al’ummar kasar Masar suke amfani da ruwan teku mai dauke da gishiri wajen inganta lafiyar jikinsu. A shekara ta 400 kafin zuwan Annabi Isa kuma mutanen kasar Girka suka fara amfani da gishiri wajen gyaran jiki, al’amarin ya rika tafiya da zamani wanda har zuwa yau ake kara fito da sababbin hanyoyin amfani da gishiri wajen gyaran jiki.
A wannan makon mun taho miki da matakan da za ki wajen amfani da gishiri don gyaran jikinki.
Akwai bukatar ki samu gishirin da ake kira ‘sea salt’ ko ‘rock salt’, wannan gishiri yana kunshe da sinadarin ‘sodium’ da kuma ‘chloride’, sannan ki nemi gishirin da ake kira ‘Epsom salt’, wannan gishirin yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da kuma ‘sulfate’, haka za ki nemi gishirin da ake ‘dead sea salt’, wannan gishiri kuma yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da ‘sodium’ da ‘calcium’ da ‘potassium’ da ‘chloride’ da kuma ‘bromide’, sannan ki nemi bakar soda, mai kunshe da sinadarin ‘bicarbonate’, sai kuma man ‘essential oil’. Sau da dama mutane suna amfani da sinadarin Borad a matsayin kayan hadi lokacin da suke hada sinadaran da za su sanya a ruwan gishiri don gyaran jiki, to gaskiya amfani da sinadarin Borad yana haifar da matsala a jiki.
Kayan hadi:

Cikin kofin shan ruwa na gishirin ‘rock salt’ Cikin kofin sha ruwa daya na gishirin ‘epsom salt’ Cokali biyu na bakar soda
digo 15 na man essential, misali; Labender da Rose da Peppermint da Citrus. Sai dai a tabbata an narkar da man sosai a cikin ruwan da za a yi wankan da shi.
Matakai:

(a)    Ki samu babban kwano ko babbar roba, sai ki hada dukkan gishirin da na lissafa a sama, bayan nan sai ki zuba bakar soda, sannan ki gauraya sosai, daga nan sai ki zuba man essential, idan kin yi hakan sai ki sake gaurayawa sosai.

(b)    Gauraya rabin kofin sinadaran da kika hada a (1) cikin ruwan da za ki wanka da shi. Ba a so ki yi wanka da ruwa mai sanyi da yawa, haka ba a so ki yi amfani da mai zafi. Ki yi amfani da ruwa mai dumi. Idan kina da bandaki na zamani, wanda akwai kwanon wanka (Baths) za ki yi cika shi da ruwa sannan ki zuba sinadaran (1) da yawa. Idan kin yi hakan sai ki shiga ciki, a lokaci guda ki shafe kamar minti talatin ko awa daya a ciki, yin hakan zai kara wa fatarki haske da laushi da kuma taushi; zai kuma kara miki kuzari.
Tura Zuwa:

yanda zakayi screen shoot a wayaShin ka taba son ka dauki hoton wani abu a wayar salulanka wanda akafi sani da screenshot a turance? Wata kila sako daga abokin arziki koh dan uwa koh kuma wani abun ban sha’awa da kaga a facebook koh kuma kana da abu a waya kana so ka turama wani yanda zaiyi abu ko yanda abun yake?.
Yanda zaka dauki abu cikin sauki tare da wayanka na android-
Danna ka Rike wajen kunna wayar tare da wajen rage sauti a lokaci daya. zakaji karan daukan abu Hoton ya dauku yana cikin dakin nuna zane-zane wanda akafi sani da gallery a turance. Amma yana aikine gamasu wayoyi android 4-0 zuwa sama wanda nasa kasa da haka bazayyi aiki ba.

zaka iya gani kai tsaye yanda akeyi
Tura Zuwa:

yanda ake kara girman rubutu a wayaShin kana samun matsala wajen karanta abu a waya saboda kankantar rubutu? Karo girman rubutu na wayar salulanka zuwa yanda zaka gani kuma ka gane
          Yanda zaka canza grima rubutu a android-
Kaje zuwa ga setting na wayar ka, ka shiga general ka sauka kasa zuwa ga Display sai kaje zuwa ga front size zaka same sa a normal sai ka canza sa zuwa ga large wasu wayoyin zaka ga extra large wasu kuma medium duk wand aka gani a cikin wayannan sai ka zaba daga nan sai ka danna ok shikenan zaka ga rubutun wayar ka ya canza zuwa babba.

zaka iya gani kai tsaye yanda akeyi

Tura Zuwa:

yanda ake sa security a waya sa KALMAR SIRRI NA HAKIKA (USE A REAL PASSWORD)Yanda zaka saka Kalmar sirri a wayar ka na android-
Kaje zuwa ga setting ka sauka kasa zuwa’ security’ sai ka shiga ‘screen lock’ sai ka danna zai tambayeka wani iri kake son sawa, na farko akwai ‘pattern’ wanda shi zana wa akeyi akwai kuma ‘pin’ wanda shi numbobi ake sawa akwai kuma na ukkun shine ‘mixed password’ a wasu wayoyin ‘password’ duk abu daya ne shi wannan zaka iya sa harrufa koh kuma ka hada harufa da numbobi, in ka zabi daya  zai tambaye ka kasa lambar sirrin, ko ka zana son ra’ayinka inna zana wane abun kula!! Ka tabbar ka san abunda ka sa ko kake sawa ko kuma ka zana, sai ka danna ‘continue’ zai sake tambayarka ma’ana ka sake sa abunda ka sa abaya, in kayi hakan sai ka danna ‘confirm’ yanzu wayanka ya kullu duk lokacin da ka kunna ko ya dan zauna na dan wani lokaci ba tare da aiki ba zai tamabayeka kasa in ba daidai ba bazai taba budewa.

zaka iya gani kai tsaye yanda akeyi


Tura Zuwa:

YADDA AKE ƘIRƘIRAR FOLDER DA KUMA AMFANIN TA ITA A COMPUTER
Folder wanda a turance ma’anarsa wani fasaha ne da ke amfani dashi wajen sakaye kaya a cikin kwanfuta, wato shi folder waje ne da ake zuba, tattara ko kuma ajiyar kaya a cikin kwanfuta waɗanda aka fi sani da ‘data’ a turance. Ita folder ta na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a cikin kwanfuta, domin kusan da ita folder ake shirya dukkanin kaya wato document na kwanfuta a shirya su kamar yadda ake shirya kaya a file na ofis ninki ninki ko kuma yanda ake shirya kaya acikin akwati. Ita folder kamar yadda muka faɗa kamar ma zubi ne, saboda haka, kusan ita kanta Kwamfutar ana shirya komai ne bisa tsari a cikin foldoji daban-daban. Haka kuma folder ta na iya shiga cikin wata folder, wa ta ma a cikin wata ya dangana da yanda kake bukatar ajiye ko kuma adana kayanka.
Kusan dukkanin application da suke cikin kwanfuta duk suna cikin folder ne a shirye. Shi ya sa kake iya ganin kayan kwanfuta suna ba ka sha’awa domin suna killace ne. Ɗauki misalin ofis ne babu drawer da za a iya ajiyar takardu, duk takardar da ta shigo wannan ofishin sai dai a ajiye ta a ƙasa, ko’ina takardu sun yi kaca-kaca a ciki. Na san ba sai an faɗama mai karatu ba cewar wannan ofishin komai kyanshi ba kintsattse ba ne. To, da waɗanda suka ƙirƙiri kwanfuta ba su yi tsarin folder ba to da wanda zai yi amfani da ita da bai san inda zai fara ba. haka ma in mun dauki misali da akwati wato wajen jera kaya duk kayanda ka dinka koka goge in har suna ajiye a kasa bazasu taba kyau ba haka kuma zai iya bacewa.
A misalin mutumin da yake amfani da kwanfuta kuma shi mai ɗaukar hoto ne, to waɗanda su ka ƙirƙiri Operating System a turance sun tsara shi a kan ya yi amfani da ‘My Picture Folder’ a cikin ita wannan folder zai kuma iya ƙirƙirar wata folder ya kira ta da misalin sunan shi wato son ranka, sannan kuma zai iya ƙirƙirar wata folder a cikin ita folder ya saka ma ta sunan hoton da ya ɗauka a misalin ya kira folder da AUREN MALLAM MUSA, sannan ya zuba waɗannan hotuna a cikin ta. Yin haka ya tabbatar da cewar duk lokacin da ya zo neman hotunan da ya ɗauka a bikin auren mallam musa to zai je kai tsaye cikin my picture – folder mai sunansa – AUREN MALLAM MUSA. Haka wanda yake son ya zuwa karatu a cikin Kwamfutar shi, kamar yana son ya saka karatun tafsiri na Sheikh Abubakar Muktar da na Sheikh Abubakar Gumi da na Sheikh Abubakar gero to zai shiga cikin folder ‘my music’ daga nan sai ya ƙirƙiri wata folder ya saka ma ta suna Tafsir daga nan sai ya shiga cikin wannan folder daka bude a baya ya ƙara ƙirƙirar wata ya saka mata sunan malamin farko. Misali Sheikh Abubakar Muktar 2012 bayan ka gama sa ka sunan sai ka buɗe ta ka zuba karatun a ciki. To, duk lokacin da kake son ka ɗauko ko ka saurari karatun ɗaya daga cikin waɗancan malaman sai ka shiga my music – tafsir – Sheikh Abubakar Abubakar gero 2011. Haka rubuce-rubucen da mutane suke yi a cikin kwanfuta ko kuma abubuwan da ka ɗauko na karatu a intanet suma haka ake son ka shirya su daki-daki a cikin kowace folder ta na wakiltar document da suke cikin ta.

Yaya Ake Ƙirƙirar Folder Ana iya ƙirƙirar folder ta wurare da dama a kuma kowane wuri a cikin kwanfuta sai dai yana da kyau duk lokacin da kake son ka ƙirƙiri folder to ka tabbatar wurin ba shi da alaƙa da wurin da ba a son a ajiye wani abu ‘reserve place’ wato a turance. Waɗannan wurare ne da waɗanda su ka yi Operating System a turance ba sa son kowa ya saka wani abu domin saka wani abu a cikin wurin zai iya cin karo da wani tsari da zai hargitsa kwanfutan ka. Wanda yake son ya ƙirƙiri folder a fuskar kwanfutanka wato Desktop zai bi wannan hanyar >> danna hannun dama Right Click a jikin sararin fuskar kwanfuta wato Desktop >> sai ka danna New >> Sai ka latsa Folder. Za ka ga ya kawo maka folder amma wurin sunanta ya sa ka ma ka suna ‘New Folder’ nan take sai ka rubuta sunan da kake buƙata son ranka, kamar ‘beebah’s Files’. Sai ka danna ‘Enter Key’ da ke jikin ‘keyboard’ na kwanfutanka ko kuma ka latsa wani wuri a jikin Desktop ɗinka da ‘left click’. Wannan shi ne hanyar da ake bi a ƙirƙiri folder a cikin kwanfuta kuma da wannan hanyar ce a kowane wuri ka ke son ka yi folder haka za ka yi. Wanda kuma ya yi kuskuren sa ka suna kuma yana son ya gyara sunan, to, zai je kan ita folder daya bude ne ya yi right click a kanta sai ya taɓa rename wanda a rubuce sai ya gyara sunan sannan ya taɓba wani wuri na daban gafen folder ɗin. 
Tura Zuwa:

YADDA AKE AMFANI DA SIGA WAJEN GYARAN JIKIAssalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fsaha. Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya, So da yawa mutane kan dauki suga a matsayin abinci ne, kawai ba tare da tunanin ana iya amfani da ita wajen gyaran jiki ba. Tabbas an fi amfani da siga a matsayin abinci, amma idan aka tsaya a matsayin abinci sai na ce lallai har yanzu an bar wasu a baya. Siga tana da matukar amfani wajen kawata jiki, domin tana fitar da dattin jiki da ko kin yi amfani da sabulu ba zai fitar da wannan dattin jikin ba. So da yawa ana amfani ne da wannan hadin ga amare, daga nan sai a ki ci gaba da shi. A wannan mako mun taho muku da matakan da za ki bi wajen amfani da suga don gyaran jikinki. Muna fata za ki bi bayanin sau da kafa. A sha karatu lafiya:
Kayan hadi:
• Ruwan lemo guda biyu
• Babban cokali daya na zuma
• Siga kashi daya bisa hudun kofin da ake shan shayi (¼)
• Man banilla (don ya bayar da kamshi)
Yadda ake hadawa:

Ki hada kayan hadin da na lissafo a sama cikin kwano ko roba. Daga nan sai ki gauraya su. Sannan ki shafa a fuska da kuma sauran jikinki. Sai ki fara gogawa da soso mai kaushikaushi, za ki ga datti yana fita, idan dattin ya fita sosai, sai ki yi wanka da sabulu. Yin wanka da sabulun zai sanya fatarki ta yi yalki da santsi da kuma sheki. Kada ki manta ki
sanya sauran a na’urar firij. Za ki iya amfani da shi na tsawon wata uku, sai dai ki tabbata yana cikin firij. Ba kullum ake amfani da wannan hadin ba, za ki iya amfani da shi sau biyu a sati. Ana amfani da wannan hadin ne musamman ga fata mai gautsi. Wannan hadin yana magani

kyesbi da ciwon fata na ‘psoriasis’. Ki guji sanya wannan hadin a wajen da yake da ciwo. Kada ki bari ya shiga idanunki, hakan zai iya haifar miki da matsala. In kin samu wannan post din da muhimmanci ki taimaka ki turawa yan uwa su anfana.
Tura Zuwa:

Yanda ake yin formating a Computer


Assalamu Alaikum barkanmu da war haka bar kanmu da sake saduwa acikin sabon shirinmu daga Duniyan Fasaha wanda yau da izinin Allah zamu nuna muku yanda akeyin formatting na memory card daya samu matsala ta amfani da kwanfuta, sau da dama mu kan samu matsaloli a memory card namu ko kuma flash ko hard drive saboda masu dalilai na virus ko kuma baciwa sanadiyar sa a wani kwanfuta ko kuma waya. akwai kirkirarrun Applications da dama wadanda ake iya yin formating na kayan kwamfuta kamar Hard Disk, Memory, Pen Drive, Re-Writable CD ko DVD da dai makantansu, sannan da matakai mabanbanta da mutum zai bi domin ganin ya yi wannan formatting din cikin sauki amma kafin nan

MENE NE MA’ANARA FORMATING?

Formating shine goge dukkan abin da ke cikin abubuwan da ake iya yin ajiyar kayan kwamfuta. Misali Hard Disk, DISK, USB Flash, Memory da dai makamantansu, ta yadda za su kasance babu su a kwata-kwata a ciki.

MENE NE BANBANCI TSAKANIN SHI FORMATING DA KUMA DELETING?

Shi deleting ya na baka damar ka cire kaya wato file ko folder a cikin abu ne, shi kuwa formating yana kankare gabadayan kayan ka ne ta yadda koda akwai wani boyayyen abu kamar virus ko zai goge shi cikin sauki, sannan zai baka dama ka canza tsarin yadda shi drive din ya ke kallo files da suke shigowa cikinsa.


MATAKAN YIN FORMATTING MEMORY KO PEN DRIVE.

1. Bayan ka saka USB Flash ɗinka a cikin ramin USB na kwanfutanka 

sai ka shiga My Computer ko ta hanyar amfani da karamar hanya wato window + E


2. Bayan ka shiga My Computer sai ka zaba shi USB Flash ɗin zaka iya gane shi ne ta ganin ƙarin babban mazubi da aka masa, ko kuma ta amfani da harafin da kwamfutan ka ba shi dashi ko kuma sunan shi Flash ɗin. Sai ka latsa shi da maɓallin dama wato(Right Click ).
3. Zai fito maka da abubuwan zaɓi masu yawa sai ka taɓa Format. Zai buɗe maka ɗan ƙaramin Window da ake amfani da shi domin yin formating.4. Sai ka zaɓi NTFS a ramin File System.5. Ka zaɓi Quick Format domin yin kankarar cikin sauri.6. Sai ka taɓa maɓallin start zai tambayi amincewar kafin ya fara in ka tabbatar kana so kayi sai ka latsa mabullin ok ma’ana ka amince7. Zai fara yin formating ɗin ya danganci girman sa, amma baya jimawa. Abin kiyayewa shi ne, da zarar ka taɓa maɓallin formattting dole ka barshi ya kammala idan ba haka ba, ka cireshi ko kuma wata matsala ta faru na ɗaukewar kwamfutar ko mutuwa to zaka iya rasa USB Flash ko memory card naka ɗin gaba ɗaya. Dafatan mun sami wannan post din da muhimmanci, ku tayamu sharing ta whatsapp facebook twitter da kuma Instagram dan yan uwanku su amfana.

Tura Zuwa:

Farfesun gandaAssalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake hada farfesun ganda, walau gandar akuya ko ta shanu domin sanya kunnen maigida motsi a kodayaushe. Ina fatan kuma ana gwada wadannan girke-girke da muke kawo muku domin neman kwarewa a harkar girki. Abubuwan da za a bukata • Ganda •Attarugu •Albasa •Tumatiri • Nutmeg •Tafarnuwa •Maggi • kori • Kayan kamshi • Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker) Hadi Bayan uwargida ta wanke ganda da ruwan kanwa domin cire karni, sai ta zuba a tukunyar dafa ganda domin samun farfesu mai laushi . Sai ta yayyanka albasa da tumatiri. Ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa. Sai ta daka garin nutmeg ta zuba da maggi da kori da thyme. Sannan sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ya nuna na tsawon awa daya. Sannan ta sauke. Ana son cin wannan girkin da safe ko da dare. Wannan irin girki, shi ne, wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba. Domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba, illa a ci kawai don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wadansu cututtuka kamar su mura da sanyi da sauransu. Ana son a rika girka irin wannan girki ga maijego, domin samun ruwan nono da karin koshin lafiya. Da fatan wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.
Tura Zuwa:

Yadda ake hadin ‘Ardeb’ Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri. A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi. Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin. A sha karatu lafiya. Abubuwan da ake bukata •Tsamiya • Siga •Masoro • Kanamfari •Citta • Ruwa Hadi A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai. dayan hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace. A dora tukunya a wuta bayan tukunya tayi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Hadin ‘ardeb’ ya hadu. A sha lafiya.
Tura Zuwa:

Girkin gasashen kifiAssalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fasaha. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya Allay yasa. A yau na kawo muku yadda ake girka gasashen kifi. Nasan daga jin an ce gasashen kifi da yawa daga cikin mata za su dauka cewa za a gasa kifi ne kawai. To ba hakan take ba. Wannan irin gashin dai sai a gidan wane da wane ake yinsa, ko kuma a manyan wajen sayar da abinci. Idan an koyi wannan girkin, ba sai an wahala wajen kashe kudi da yawa domin samun irin wannan girkin ba. Girkin gida ya fi armashi da auki. A sha karatu lafiya. Abubuwan da za a bukata • Kifin karfasa/tarwada • Attarugu • Magi • Takaddar ‘foil’ • Tafarnuwa • Albasa • Man gyada • Kori Hadi A samu kifin tarwada sannan a wanke da ruwan kanwa, ta yadda karnin zai fita tsaf. Sannan a wanke da ruwa. A kunna mukubur (rishon garwashi) ya yi zafi sannan sai a dauki karfen gashi akai. A yayyyanka albasa da jajjaga attarugu sannan a zuba a daura kifi akan takardar ‘foil’ a daka magi sosai yadda zai ratsa cikin kifin a zuba. Sannan a zuba jajjagen attarugun tare da yankakkiyar albasa a ciki. a barbada garin tafarnuwa kadan a ciki da dan kori. A shafa man gyada kadan a takardar ‘foil’ din kafin a zuba sauran kayan hadin a ciki. sai a nada takardar kamar sau biyu zuwa uku. Sannan a dora akan wutar garwashi. A bari ya gasu na tsawon mintuna 15 sannan a sake juya dayan gefen shi ma ya gasu na tsawon mintuna 15. A kalla dai an samu mintuna 30 ke nan. Sannan a bude a ci dadi. Za a iya yi wa maigida irin wannan girkin ko don more rayuwa.
Tura Zuwa:

SIFFOFIN UWA TA GARI 2SIFFOFIN MACE TA GARI

Yar uwa mai karatu ga kadan daga cikin siffofin mace ta gari, idan kuwa baki da wadannan siffofin, to sai ki rungumi wannan su zamo dabi’unki. Allah yasa mu dace Ameen

1. Itace idan mijinta yayi mata umurni zatayi masa biyayya.

2. Itace idan mijinta ya kalleta zata farantamasa rai.

3. Itace idan mijinta yayi rantsuwa akanta zata barrantar dashi.

4. Itace idan mijinta yayi tafiya zata kiyaye kanta da dukiyarsa1. MACE TAGARI ITACE = WACCE IDAN MIJINTA YAYI MATA UMURNI ZATA YI MASA BIYAYYA: Yake yar’uwata ki sani duk irin umurnin da mijinki yayi miki to wajibine kiyi masa biyayya matukar bai sabawa Allah ba. Kuma acikin kowani hali kika samu kanki ba tare da yamutsa fuska ba. Balle jan aji, kuma yar’uwa ki sani jan aji haramunne idan mijinki yayi miki umurni, wajibine ki zamo mai bin umurninsa. Allah ya baki ikon bin umurninsa Ameen.

2. MACE TAGARI ITACE= IDAN MIJINTA YA KALLETA ZATA FARANTA MASA RAI: Ya yar’uwata mijinki ba zai taba kallonki har ki faranta masa rai ba, face kin dauwama a siffarki ta ya mace.

GA WASU DAGA CIKIN SIFFOFIN KAMAR HAKA KWALLIYA DA GAYE:

Yar’uwata ki sani yana daga cikin asalin hallitar mace akai shine kwalliya, don haka ba’a son mace cikin sahun mata idan batayin kwalliya, anan wajibine ki kasance zinariya a gidan mijinki ko wani lokaci da irin salon kwalliyan da zaki yiwa mijinki acikin lokuta guda hudu kamar haka:

i- LOKACIN SAFIYA:Yar’uwata bayan kinyi Sallah wajibine kiyi wanka kiyi kwalliya irin kwalliyar Amarci.

ii- BAYAN BREAK FAST: Idan kin gama wanke kwanukan da aka ci abinci kinyi shara sai kiyi wanka kiyi kwalliya, yar’uwata kar ki yarda mijinki ya dawo ya sameki a hargitse, kamar yadda wasu mata sukeyi, abin kunya wai suna da zanin zaman gida kuma suna da zanin fita anguwa, wallahi wannan mummunar dabiane a dena.

iii- BAYAN ABINCIN DARE: Yake yar’uwata anan ma ya zama dole ne kiyi masa kwalliya irinta zamani wadda zaki kayatar dashi.iv- LOKACIN BARCI: Yar’uwata anan kuma wajibine zaki yiwa mijin ki kwalliya da shara sharan kaya wadda zasu rikita mijinki.
Tura Zuwa:

ABUBUWAN DAYA KAMATA KA SANI KAFIN KA FARA RUBUTUN RA’AYIN KANKA A YANAR GIZO WATO BLOGGING A GIDA NIGERIA KO KASHASHE MAKUSA


Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa a cikin sabon shirinmu, insha Allah yau zamu tattauna a kan abubuwan daya kamata mu san dasu kafin mu fara rubutun ra’ayin kanmu ta hanyn yaran gizo wanda akafi sani da blogging a turance, abu na farko daya kamata mu sani shine yanar gizo a zamanin nan ya kasance abune da yake sawwake ayyuka ta bangare daban daban, sannan kasan da cewa kafin ka fara rubutun ra’ayinka ta Shafi wato blogging yana da kyau ka san da cewar kafin ka fara dubanni mutane sun fara ko kuma sunyi ta bangare daban daban, in dai kana so ka zama gwani kuma kwararre ta bangaren yanar gizo  to yana da kyau kazoo dana ka fasalin wand aba mai aiki dashi, sannan kuma dole sai ka ringa rubuta abubuwa sabbi ta bangaren daka zaba.  Na kasance a kan yanar gizo sama da shekaru takwas 8 amma na fara rubutu ta yanar gizo shekaru biyar da suka wuce a shekaru biyar na kasance ina wasu kurakurai wanda a yanzu na gane kuma na gyara, kamar yanda ake fada ‘rayuwa ta kasance karamar aba ce wanda yana da wuya kayi ba tare da kayi kuskure ba’. Ina son na zayyano wasu kurakuren wanda na koyo daga wasu wanda ba nawa ba.


MUTANE BASU SON ZIYARTAN SHASHINA (BLOG)


Ina son na kasance mai samun masu ziyartan shafina sama da dubu a ko wani rana amma a yanzu bana samun ya kai koda dari a rana guda shin menene dalilin da yasa mutane basu ziyartan shafina shin abu nake sawa mara kyau?? Ko dai laifi nayi musu?? Wannan za kayi la’akari da shin kane, shin mene ne nake rubutawa kuma menene ingancinsa a wurin mutane saisai yake da kyau in zaka fara rubutu a shafi ya kasance ka zayyano menene dalilin fara wanka kuma menene manufar ka ta bangaren rubutu kuma abu babba daya kamata muyi la’akari dashi shin wani ya fara?? Shin wani nayi?? Ko kuma shin wani ya taba yi?? Wannan ne abu mafi girma daya kamata mutane muyi la’akari dashi kafin bude shafi dan gudun fara abunda akayi ko kuma akeyi.  


KOMAI A RAYUWA WASU LOKUTAN YANA DAUKAN LOKACI MAI SAWO KAFIN YA BAYYANA

Samun mutane suna ziyartan shahinka samun shashinka ya bayyana a google search, samun mabiya a facebook da kuma twitter, samun kasancewar daya daga masu aiki da companing google adsense da duk sauran abunda ya kamata yana daukan sawon lokaci sosai domin komai a rayuwa ba’a masa hanzari.


WASU LOKUTAN INA JIN KIWIYAN RUBUTU A SHAHINA


Saboda wasu ayyuka ko dalilai bana samun damar yin rubutu a shashina saboda kasala ko kuma ayyuka. Wasu lokutan kuma uzurori sunmi yawa, yana da kyau ka dage wajen rubuta abu a shafinka koda sau uku ne a sati ko kuma ka sami wani mai ilimi abangaren abunda kake rubutawa dan ya tallafa wa shafinka masana suna fadan cewa kai biyu yafi daya, mutane zuna ziyartan shafinka ne saboda abubuwan da kake rubutawa a kowani lokaci, in mutum ya karanta sau da dama babu kari yakan fita kansa kuma yaji shiru daga gareka tsawon lokaci dole ya koma wani shafin inda zai ringa samun abunda yake bukata.


            SURAN SHAHINKA

Suran Shashi wanda aka fi sani da blog design wannan yana daya daga cikin abu mafi girma da ya kamata muyi la’akari dashi wajen bude sabon Shashi saboda mutane da dama sukan ziyarci Shashi saboda lalurori ko kuma aiki, sau da dama zaka samu idan mutum ya ziyarci shafinka sai ya koma baya ba tare da ya karanata ko ya mai da hankali ba saboda yanda ya gansa ba tsari haka a tunaninsa yake gaya masa abunda ke kunshe a wajen bashi da inganci, saboda haka wannan yana daya daga cikin manyan abubuwa da ya kamata ka tanadar wa shahinka saboda samun masu karatu da mabiya sosai.


SHAKKA ZAI IYA KASHE SHAFINKA


Wasu lokutan ban sami amfanin suran shafina dana siya ko kuma banga amfanin bude hanyar sadarwa ba irinsu twitter facebook da kuma whatsapp saboda babu masu ziyartan shafina, yanda kake tunani ba haka abun yake ba yana da kyau in zaka fara rubutu a shafi ya kasance kana da account a hanyar sadarwa saboda yana taimakawa matuka wajen samun masu ziyara a koda yaushe, ba lallai bane ya faru san ra’ayinka ko a lokaci guda.


Ina fatan zaka fita daga shakka ka fara aiki dukurun wajen mayar da shahinka daya daga cikin manyan shafuka a kasa ko duniya baki daya.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan


Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

ABUBUWAN DAYA KAMATA MUYI LA’AKARI DASU WAJEN SAYAN SABUWAR TAFI DA KAYAN KA WATO LAPTOP

Assalamu Alaikum barkan mu da warhaka barkanmu da sake saduwa acikin sabon shirinmu insha Allah yau zamu tattauna akan abubuwan daya kamata muyi la’akari dasu wajen sayan sabuwar kwanfuta, Wai shin, menene abubuwan da ya kamata ayi la’akari in a nason siyan sabuwar tafi da kayanka wato laptop a turance kuma wani wani campani yafi inganci a yanzu?  abu na farko da ya kamata muyi la’akari da shi a lokacin da zamu siya kwanfuta zai sayi kayan wuta ba ma dole sai kwanfuta ba, shine suna da inganci sosai? idan aka zo ga maganar kwanfutan tafi da kayanka wato laptop kusan gaskiya campanoni da dama a wannan lokaci suna matukar kokari wajen ganin sun wuce tsara, amma idan maganar wace irin tafi da kayanka laptop zaka ka siya saboda ingancinsa to ya danganta da aljihunka domin kare da kudin shi ai zai sha lahaula. Idan kuwa ka zo siya ka duba mene ne girman processor dinsa ma’na yanayin gudunsa, kuma mene ne girman RAM din su, mene ne kuma karfin batirin ta awa nawa yake yi, domin a wannan lokacin karanci ka samu sabuwar laptop tana kai awa hudu da rabi cikakke kafin ta dauke, daga baya sai ka duba girman HARD DISK dinta wato girman kwakwalwanta, sannan kuma ka duba girman ta domin wata ta fiye kankanta wata kuma tafi girman da yawa ka duba matsakaiciya wacce ba zata baka wahala wajen dauka ba kuma wajen aiki. sannan bayan ka biya ka lura da yi mata charging kafin ka fara amfani da ita domin rashin yi mata charging da farko yakan lalata batir, A yanzu campani da aka fi samun kayansa a kasuwa shine HP da kuma DEL yana da kyau mutum in zai siya ya takaita a cikin biyunnan domin wasu in sun samu matsala kafin a samu kayansu a kasuwa yana da matukar wahala, sannan kuma kada ka rinka saka mata program ko applications da ba zaka yi amfani da suba kuma ka guji saka games da video da baka san daga inda suke ba. Kuma tunda ka yi kokari ka sayi tafi da kayanka laptop da kudi mai yawa to ka daure ka siya sabon antivirus daga company kaspersky ko kuma norton domin duniya anyi ittifaki babu wanda ya fisu defination na virus wato fasahar virus amma bayansu akwai wasu da dama wanda suke taimakawa sosai kamar su smadav.
Tura Zuwa:

SIFFOFIN UWA TA GARI
ABUBUWAN DA SUKE CIKI


 Godiya
Gaisuwa
  Gabatarwa
Mace Tagari
Siffofin mace Tagari
Bayanin siffofin Mace Tagari
Bayani akan Lalle
Bayani akan ado
kisisina da kareraya
Damuwa da damuwarsa
Bayani akan girki

  §  Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

GODIYA
Dukkan godiya su tabbata ga Allah (S.W.T) Ubangijin Talikai bias ni’imominsa bayyanannu da boyayyu tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da dukkan wanda sukabi tafarkinsa. Har zuwa ranar Alkiyama Ameen.
GAISUWA
Dukkan gaisuwa ga yan uwa musulmai maza da mata Allah ya hada mu a Aljannah. Baran manta Da:
v Albudullahi ahmad
v Abubakar Garba
v Abubakar sadeeq (takai)
v Ahmad bello Hassan
v  Beebah Wadata
v Habeebullah yareema usman
v  Rabiatu Sk Mashi
v Zainab isa
v Zahra bb
v  Faty Afreen
v Asma’u umar babayi
GABATARWA
Ina gabatar da wannan littafi wanda ya kunshi takaitaccen bayani akan iyaye mata. Domin a hakikanin gaskiya iyaye mata sun bambanta wajen tarbiyar ya’yansu Allah yasa mu dace, Ameen a karshe ina mika godiya da fatan alkairi ga malamina Abdullahi Mustafa a bisa shawarwarin daya bani har littafin ya kamala. 15/10/2016. Bayan haka wannan wata fadakarwace ga yanuwa mata zalla, ko zasu fadaka daga gurbatattun dabi’unda sukeyi a gidan aurensu. Muna rokon Allah ya daidaitamu bisa bin hanya madaidaiciya kuma ya shiryemu ya sanya mu cikin bayinsa salihai Ameen.
AURE
Da farko yake yar’uwa ki sani aure bautanena ubangiji ne. To amma mai yasa ku mata kuke banbanta yanayin zaman aurenku bayan Annabinmu dayane, domin da yawa daga cikin yan uwa mata basu dauki aure a matsayin bautaba wallahi. Bayan aure itace babban hanyar shigarki Al-jannah idan kikayi hakan kuma kika yarda da hakan to kinci riban duniya da kuma lahira.Allah yasa haka Ameen. Sannan ki sani yar’uwa duk wata ibada tana tareda jarrabawa musamman ma aure, domin zamane da ya kunshi farin ciki da bakin ciki, dadi. da mara dadi, hakuri da rashin hakuri, da sauran wasu abubuwan da basai na ambacesu ba, Yake yar’uwa ki sani aure anayinsa saboda wasu abubuwa da dama amma babban su shine natsuwa. Kuma natsuwa baya samuwa sai idan mace ta zama tagari shiyasa da yawa daga cikin maza basuda natsuwa saboda matansu ba nagari bane. Manzon Allah (S.A.W) yace duniya abin jin dadi ne, amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine mace tagari, don haka ya yar’uwata idan harke ba mace tagari bace to ki sani baki da amfani a zaman gidan aurenki da mijinki idan kika sake baki gyara zamanki da mijinki ba, to wallahi zaki samu mummunana sakamako a wurin Allah. Allah ya karemu Ameen.
MACE TAGARI
 Mace ta gari za a same ta da:
    1.    KAMEWA: Daga duk wani abu da zai sosa wa maigidan ta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
    2.     GASKIYA: In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.
    3.    AMINCEWA: Duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.
    4.    TAWALU'U: Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)
     5.     NATSUWA: Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.
    6.     KUNYA: Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
    7.     KWANCIYAR HANKALI: Mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
    8.     GODIYA: Duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.
   9.    HAQURI: A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)   
   10.                       TSAYUWA QYAM: A wajen bauta da qarfafa mijin da 'yayan su.

    11.                       AMANA: Ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.‎
     12.                       CIKA ALQAWARI: Yana Daya daga adon mace da namiji.
     13.                        TSORON ALLAH: A duk abin da za ta yi.
     14.                       DANNE ZUCIYA: Yayin da aka baqanta mata rai.


Wadannan abubuwa guda 14 su suke nuna mace nagari, dan uwana kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma yar uwa ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba. Biyayya ga miji ba mai iya wa sai mace ta tagari,da yawa mata suna so a ce su ne wadan da Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar ce ta yi qaranci, ko za a yi sai dai a gabansa in ya matsa an watsar kenan.

           Mace ta gari takan yi qoqarin ta zama wa mijinta aljannarsa ce, ba ta son ta ga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki in taga murmushinsa, takan damu matuqa in ta ga fushinsa ko da ba da ita yake ba, ba ta jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa ba tare da almubazzaranci ba, ita ce amin taccen abokin shawararsa,mai iya riqe masa sirri, ba ta yarda wani ya sani ko waye kuwa, sannan ga taimako.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive