Alhaji Muhammad Ibrahim wani ma’aikacin gwamnati ne da ya fada hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kagarko zuwa Jere da ke Jihar Kaduna, inda suka sako shi bayan kwana uku. A zantawarsa da Aminiya, ya bayyana irin halin da ya kasance tare da wadanda aka kama su tare
Aminiya: Kwanakin baya ka fada hannun masu garkuwa da mutane, ko za ka bayyana mana yadda lamarin ya kasance?
Muhammad: To, da farko dai sunana Muhammad Ibrahim kuma ina aiki ne a garin Abuja. Ni mutumin garin Kafanchan ne. Wata ranar Litinin na baro Kafanchan kamar yadda na saba idan na zo hutun karshen mako, na kama hanya da misalin karfe bakwai na safe don komawa Abuja ta hanyar Kagarko zuwa Jere zuwa Bwari ke nan. To, bayan na wuce Kagarko da misalin karfe takwas da minti goma kafin na iso Marabar Jere, ban ankara ba ina tafiya ni kadai a cikin mota sai wasu mutane biyu kawai suka fito kan titi da bindigoginsu; suka fara bude mani wuta har sun fasa mani mota da harsashi guda hudu. Da na ga suna neman kashe ni sai na tsaya cak, sai ga wasu karin mutum hudu sun fito daga dajin; kowannensu da bindiga a hanunsa, suka fara buguna. Suka ce sun san aikin da nake yi, don haka in ba su kudi kawai.
To, akwai kudi Naira dubu hamsin a jikkata da nake tafe da ita a lokacin, a bayan but din motata. Suka bude suka dauko, sannan suka amshe wayata. Ana tsakar haka sai ga wata mota nan ta fito daga Jere dauke da wasu ’yan makaranta su hudu; maza biyu da mace daya. Bayan sun umurce su da su fito, sai suka kora mu gaba daya mu biyar din cikin daji, muka bar motocin a wurin. Haka suka rika kada mu a cikin kungurmin daji, mu kurda nan mu kutsa can; suna tafiya suna harbe-harben bindigogi a cikin dajin nan. Sai da muka kwashe awa goma sha daya muna tafiya, kafin muka isa masaukinsu a kungurmin dajin.
Aminiya: Yaya masaukin nasu yake?
Muhammad: Babu komai a wajen da zai nuna maka cewa ko wajen kwana ne.
Aminiya: Sai me ya faru daga nan?
Muhammad: Daga nan sai suka ce mana muna da labarin wadanda ake kira masu garkuwa da mutane, muka ce musu e. Sai suka ce mana to su ne, don haka yanzu duk mai so ya koma wajen ’yan uwansa to sai ya biya kudin fansa.
Suka fara tambayata ko ina da kudi, na ce musu ina da su. Suka ce nawa zan ba su? Na ce sai dai su yi magana da ’yan uwana. To, a haka suka fara magana da su ta waya. Sauran kuwa da suka ce ba su da kudi don su ’yan makaranta ne, haka suka dinga jibgarsu. Duka na fitar hankali suka yi masu, domin sun tambaye su kudi sun ce babu saboda su ’yan makaranta ne. Haka muka zauna a dokar dajin nan har tsawon kwana uku suna ta ciniki da ’yan uwana har suka daidaita.
Aminiya: Kamar nawa suka bukata?
Ni ma ban san nawa suka yi ciniki da su ba. Sun ce ’yan uwana sun cika taurin kai da yawa. Ni ban sani ba ashe har sun yanke shawarar cewa washegari za su kashe ni saboda ba su samu abin da suke so wajen ’yan uwan nawa ba. Ni ban sani ba ashe daya daga cikinmu Bafulatani ne, yana jin abin da suke fada da Fulatanci. Shi ne yake shaida mani abin da ya ji suna fadi da yaren Fulatancin.
Aminiya: Me ka fahimta da mutanen?
Yara ne dai matasa, daga dan shekara ashirin zuwa ashirin da biyar. Wani lokaci za ka ji sun kira ’yan uwansu suna cewa a kula masu da dabbobinsu, domin sun yi tafiya, ba za su dawo ba sai bayan kwana biyu. Ka ga watakila ma danginsu ba su san suna wannan muguwar sana’a ba.
Aminiya: Yaya batun abinci da ibada?
Muhammad: Ibada? Lokacin da na ce masu ma ina so in yi Sallah, daka mani tsawa suka yi, suka ce idan na sake yi masu maganar Sallah a nan za su kashe ni. Amma fa abin mamaki, har wa’azi dayansu yake kunnawa a wayarsa yana sauraro.
Batun abinci kuwa, iya tsawon kwanakin nan da muka yi, ba abin da suke ba mu face kofin ruwa sau daya a rana. Su kuwa farar shinkafa suke dafawa, sai manja da albasa amma ko gishiri ban gan su da shi ba.
Aminiya: Yaya aka yi suka sake ka?
Muhammad: To, bayan sun daidaita da ’yan uwan nawa, sai suka fada wa wanda zai kawo kudin cewa kada ya ji komai, domin dajin nan nasu ne, ba abin da zai faru da shi.
Aminiya: Ko akwai abin da suka ce maku daga nan?
Muhammad: To, lokacin da zan tafi sai suka ce mani in roka masu Allah idan na koma gida, domin Ya yaye masu wannan aikin ta’asar da suke yi sannan ni ma in roka wa kaina Allah Ya kiyaye ni daga sharrin makiyana na fili da na boye, domin su makiyana ne na fili amma na boyen suna nan like a kusa da ni saboda sun karanta mani tarihina kakaf.
Aminiya: Ko akwai wani kira da za ka yi, musamman ga hukuma?
Muhammad: kwarai kuwa! Da farko dai ina so hukuma ta sani, wannan lamarin ba dan karami ba ne, don haka ta tashi tsaye haikan ta yi fada da mutanen nan; musamman a wannan babbar hanyar, wadda na samu labari zuwa yanzu bayan sako ni, sun tsare mutane da dama a hanyar. Domin in kana tunanin tafiyar dare ce matsala, to su da rana tsaka suke ta’asarsu. Don haka ina kira ga gwamnati, ta yi kokari ta dirkake mutanen nan kamar yadda ta yi wa ’yan ta’addan Boko Haram a dajin Sambisa, domin ana asarar dukiyoyi da rayuka kuma ana kashe hanyar.
.
No comments:
Post a Comment