Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Hada Burodin Ayaba

Yadda Ake Hada Burodin Ayaba

Uwargida Barkanki da warhaka, tare da fatar kina cikin koshin lafiya. Allah yasa Ameen!. Kamar dai yadda muke fada a koda yaushe yana da kyau kina chanza girki lokaci zuwa lokaci domin tsotsa kunnuwan mai gida. 

Bamu yi kasa a gwiwa ba A yau Duniyan Fasaha ta kawo miki wata hanya mai sauki na yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa domin yi wa Manyan Gobe ko shimi mai gida a matsayin abin karyawa a duk safiya ko kuma yin sa domin sha’awar cinsa ko kai wa aminan arziki da yan uwa.

Abubuwan Da Zaki Bukata:

  • Fulawa
  • Kwai
  • Sukari
  • ‘Baking powder’
  • Ayaba
  • Madara
  • Bata

Yadda ake yin hadin cikin sauki:

Ki samu ayaba biyu ki kwaba su da cokali mai yatsu, sannan ki zuba fulawa a kwano sannan ki zuba ‘baking powder’ da sukari da madara, sannan sai ki kwaba.

Daga nan sai ki zuba BATA kamar cokali biyu sannan ki kwaba sosai. Sai ki fasa kwai biyu da kwababbiyar ayabar a cikin fulawar da kika yi mata hadin sukari da sauransu.

Sai ki gauraya su sosai su kwabu. Sannan sai ki dauko tukunyar gasa burodi ki zuba sannan  kisa a gidan gasa burodi. Bayan minti 45 ko hamsin sai ki cire.

Za a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za’a iya aika wa makwabta domin su dandani sabon salon burodi sai mayar da dogon kwadayi.

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *