Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Fasahar E-Naira: Ma’ana, Fa’idoji Da Tsarin Gudanuwarsa

Fasahar E-Naira: Ma’ana, Fa’idoji Da Tsarin Gudanuwarsa

A ranar Jumma’a, daya (1) ga watan Oktoban 2021 ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya so kaddamar da sabon nau’in kudin zamani mai suna: e-Naira, a tsarin gwaji.

Sai dai CBN ya dage kaddamar da sabon nau’in kudin saboda wasu dalilai da ya alakanta da al’amuran da za a gudanar a kasar na bikin cikarta shekara 61 da samun ’yancin kai.

Haka kuma wannan jinkiri ya zo na kwana guda bayan da wani kamfani mai suna ENaira Payment Solutions Limited ya shigar da karar Babban Bankin Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya kan amfani da sunan ENaira.

Tura Zuwa:

Shugaban Twitter ya yi murabus saboda matsin lamba

 

Shugaban Twitter ya yi murabus saboda matsin lamba

Shugaban kamfanin sada zumuntar intanet na Twitter, Jack Dorsey ya sauka daga mukaminsa, sama da shekara daya da tsallake rijiya da baya da ya yi, bayan da wani dan gwagwarmaya mai hannun jari a kamfanin ya jagoranci yunkurin tsige shi.

Dorsey, wanda shi ne shugaban kamfanin hada-hadar kudade na Square ya shiga cikin matsin lamba a shekarar 2020 daga hukmumomin kamfanin Elliott, wadanda suka bayyana damuwar cewa ya mamaye ko ina, kuma ayyuka na yi masa yawa ta wajen tafiyar da kamfanoni 2.

Tura Zuwa:

Za'a Samar Da Fasahar Intanet A Duniyar Wata

Za'a Samar Da Fasahar Intanet A Duniyar Wata

Shekaru kusan 50 kenan da dan Adam ya fara taka kafarsa a duniyar wata, sa’ar da mahaya Kumbon Apollo 11 suka ziyarci duniyar.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu dai an samu ci gaba a fannin kimiyyar sararin samaniya sosai.

Wannan ya sa a halin yanzu Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasar Amurka (NASA), ta kudiri aniyar sake komawa duniyar wata a shekarar 2024.

Sai dai a wannan karon ziyarar za ta sha bamban da ziyarar farko. A karon farko mace za ta kasance cikin ayarin. 

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *