Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Ya Kamata A Ba Mata Dama Su Taka Rawa A Harkokin Siyasa-Inji Aisha Yakubu Mai Jama’a

Allah ya albarkace ni da haihuwar ‘ya’ya dai dai har guda takwas kana Allah ya nufe ni da shiga makarantar gaba da sakandare domin karo karatu a cewar wata fitatticiyar ‘yar siyasa Aisha Yakubu Mai Jama’a.
Malamar ta bayyana cewa ta koma makaranta a shekarar ta 2009, inda ta karanci Public administration kuma a hallin yanzu take karatun HND wato kwatankwacin karatun digiri.
Ta ce a matsayinta na ‘yar siyasa, ta fahimci cewa a halin yanzu ba’a baiwa mata damar damawa da su a harkar siyasa inda ta ce mafi yawa maza basa son mata su shiga cikin siyasa sun mai da harkar kamar gado ko sana’a.
Aisha Mai Jama’a, ta ce zai yi wuya mace ta fito neman takara ba tare da delegate ko agent sun kawo mata cikas ba, daga karshe ta bayyana cewa abin kunya ne mace ta fito sa’annan ta gaza yiwa al’ummar ta hakan ne ya sa da zarar ta samu nasara babban muradinta a rayuwa shine ta cika alkwarin da ta daukar wa al'ummar ba.Ya Kamata A Ba Mata Dama Su Taka Rawa A Harkokin Siyasa- Inji Ai

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive