Mataimakin shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci garin Numan na jihar Adamawa bayan hare-hare da aka kai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Farfesa Osinbajo ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa ya ziyarci garin ne don jajantawa al'umma a madadin shugaba Muhammadu Buhari.
Mataimakin shugaban kasar ya ce a tattaunawar da ya yi da masu ruwa da tsaki a garin ranar Talata, ya jaddada musu cewa babban abun da jama'a ke so shi ne zaman lafiya da ci gaba.
A watan Nuwamban 2017 dai rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a yankin tsakanin kabilun Bacama da Fulani inda aka kashe mutane akalla 20.
Hare-hare na baya bayan nan shi ne wanda aka kai ranar Litini inda aka hallaka mutane da dama.
A halin yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a yankin bayan da kura ta lafa.
No comments:
Post a Comment