Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.

INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.


KAFIN NA FARA JAWABIN BAN YARDA A JUYA WANNAN SAKO TA KOWACCE HANYA BA, HAKA KUMA BAN YARDA A CIRE WANI ABU DAGA CIKI BA TARE DA CIKAKKEN IZININA BA KO WANI DAGA MUJJALAR DUNIYAN FASAHA KO KUMA SHAFIN HANYAN TSIRAH. A KIYAYE! WANDA KUMA YAYI MUN BARSA DA ALLAH. A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.

1.     ki tsayar da saurayi guda daya tak na kirki bisa la akarai da ayyukan sa da halayensa na zahiri.

2.     kitabbata kina sonsa sosai kuma shima yana sonki sosai.

3.     Kada ki yarda kidade da saurayi, ko kishaqu dashi ko ki nuna masa tsananin so batare da iyayensa sun gana da iyayenki ba. In yaqi turosu kirabu dashi tunkafin yagama sace zuciyarki.

4.     Kizama mebin shawarar iyayenki, da neman shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.

5.     Kada kiyarda a kawo miki gulmar saurayinki ke kuma kidauka koki kama zargin sa. A'a sai kinyi bincike na adalci ko kingani da idonki.

6.     Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki qarya kizama me fada masa gaskiya, da yimasa bayanin komai iya saninki.

7.     Kizama me yawaita addu'ah da bawa Allah zabi a dukkan lamarinki.

8.     kikiyaye zargi da binciken laifinsa matuqar ya sanar dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.

9.     kidauka dan adam tara yake bai cika goma ba, kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa afuwa.

10.kizama me kare mutuncin kanki, da kuma kulada matsayinki batare da girman kaiba ko jan aji ga masoyi... JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE HAIFARWA SAI NADAMA. idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu yabarki ko kin rasa wani abu da yake baki, kiyi haquri kada kijuya masa baya, kisa masa shakka a ransa yadinga tunanin anya kuwa kina son sa da gaske???

KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA TAKUNKI.

11.Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki fuska yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko dabi'u. kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki ,ko zai auna kaurinki dadai sauransu.

SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI ADUK SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE YA BATAKI. Wakilin shaytanne.

12.Kizama me yiwa saurayinki Al-qawarin nuna masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa biyayya dai dai gwargwadon iyawarki.

KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI MAKIRCI. Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo yabata miki lokaci. Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo wajenkibyayi tayi miki qarya batare dakin fargaba zai dasa miki ciwon so, YA KORAR MIKI SAMARIN KI NAKIRKI. Wani kuma kawai so yake yana zuwa wajen fati dake. Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana fira da ke zai fake da cewa SAI YAGAMA School KO SAI BAYAN YAGAMA KARATU ZAI TURO KUYI AURE.

Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi. Wani kuma soyake kawai yana taba jikinki yaji dadi koda bai kwanta dakeba, saboda haka zaita binki sauda qafa yana soyayya dake. Wani kuma so yake ya bataki. Irin wadannan samarin sunfi kowanne hatsari. Idan yaganki yana sonki yana fara karantar halayenki IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO ZAIYI SHIGAR USTAZAI HARDA LITTAFIN SA A HANNU, HAKA ZAITA KAFA MIKI TARKO HARSAI KIN FADA.

Idan yaga 'yar BOKOCE zai fito miki a dan boko. Idan yaga ke yar duniya ce toshima a hakan zai fita.

Irin wadannan samarin har kayan mungani munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna turowa daga qarshe daya kwanta dake shikenan yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki kwaya da zarar yaga baki da ciki yasan yayi free tunda yasami abinda yake nema, zai Qirqiri laifi yalaqamiki domin ku6ata a karbo kayan sa daga gidanku, koma yabar miki kayan...

Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran soyayya ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a gaban budurwa duk da sunan so amma yawanci domin ya raunana zuciyar kine. Yakan maqale miki har unguwa yana rakaki koda yaushe.

YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA WAYE YAFI SHAN WUYA DA TOZARTA ??? SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE KO BUDURWA AKEWA??? IDAN ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI ZAUNA A GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA DAN KUNYA NAMIJI KO MACE??? MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA BIYAR CIKI BATARE DA AURE BA AMMA INYAZO NEMAN AURE SAI ABASHI??? IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA DA KYAR TAKE AURUWA KOMA SAI TABAR GARIN??? MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA TSANARTA AKEYI, AMMA NAMIJI DAYA KAWO RAGO DA KUDIN ICE SHIKENAN??? MATA NAWANE SABODA CIKIN SHEGE SUKABAR GARINSU KO RAYUWARSU TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI KAMARMA BAIYI KOMAI BA??? KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN MAGANI DUK WATA??? KINTABA GANIN ANSA WUQA A WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI WACCE KAYIWA CIKIBA SAINA YANKAKA??? AMMA WA AKEWA HAKA???

'Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan kudin da saurayi zai baki kodan zai saki a gaban mota, kodan wasu yan riguna dazaina saya miki HAKAN TASA KIBASHI DAMA HAR YASANKI 'YAMACE WALLAHI KIN KADE.


IN HAKAN TAFARU TO KITUBA GA ALLAH (S.W.T) DOMIN SHI MAI GAFARANE. FATAN "HANYAN TSIRAH" ANAN SHINE, ALLAH YASHIGA TSAKANIN NAGARI DA MUGU. ALLAH YAHADA KOWACE YA MACE DA SAURAYI NAGARI DA ZATA KAISU GA AURE NAGARTACCE. MUMA MAZAN ALLAH YABAMU MATA NAGARI. BISSALAM
Share:

"ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"

"ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"

"ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA BY MUHAMMAD ABBA GANA"
Shafe-shafe yana da illoli masu tarin yawa musamman ga ’ya mace.

1.     Na farko yana canjawa mace launin fatarta. Fatar da ba a yiwa shafe-shafe, ita take bada kariya daga cututtuka da sauran kwayoyin da suke yiwa fata barazana. Fata ta asali tana ba mace garkuwa daga zafin rana.

Bayan mace tayi bilicin zata kasance cikin yawan laulayi, bazata iya yawo a rana ba domin zataji kamar ana kwara mata ruwan zafi, saboda tarasa fatarta ta asali datake bata garkuwa daga zafin rana.

2.     Abu na biyu shi ne, mai bilicin bazata sami kariya daga cutar daji ba wato (Cancer), wadda cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba kasafai aka fiya samun maganinta ba.

Cuta ce wadda take kama sassan jikin mutum, yawanci akan yanke gabobi ko wuraren data kama. Duk wannan yasamo asali ne a sakamakon bilicin.

3.     Mai bilicin za ta rasa kuzari, Idan kafin ta fara bilicin tana iya yin aiki na tsawon sa’a uku bata gaji ba, to yanzu ba lallai bane ta iya na sa’o’I biyu, hakan ya haifar mata da nakasu, maimakon a nemo kiba sai aka iske rama.

4.     Ba a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba, akwai illoli masu tarin yawa da kuma tsoratarwa. Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi sani da olsa (ulcer) wanda mafi yawanci akan dauketa a matsayin rashin cin abinci ke kawota. Daga ciki akwai kassara dukkan wasu sassan jikinki masu amfani walau wadanda ake gani a zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani, kamar irinsu:

·        Hanta.
·        Qoda.
·        Hunhu da sauransu.


Wadannan duk suna tagayyara ne sakamakon illar bilicin. Da fatan za'a kiyaye.
Share:

Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi

Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi

A halin yanzu, sanyi ya fara sallama a wajaje da dama. Da zarar an fara ganin hazo ko hunturo lallai wannan alama ce ta nuna cewa sanyi ya shigo. A wannan lokutan ne yakamata a fara takatsantsan wajen kulawa da fatar jiki. Idan ba’a kula da fatar ba, har sai da ta gama bushewa ko yin gautsi, hakan na daukan lokaci kafin a samu a magancesu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za’a magance matsalolin fata a lokacin sanyi.

1.==> Man kadanya: tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata.

2.==> Kaushin fata: idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin.

3.==> Fason kafa: yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar.

4.==> Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska.


5.==> Karyewar gashi: kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwakwa na hana gashin kai zubewa.
Share:

Kula da gashin kai a hunturu

Kula da gashin kai a hunturu

Assalamu Alaikum matan gidan nan tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Na dan tafi hutu ne amma da yardarr Allah na dawo lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a lokacin hunturu. Gashin kawunanmu na bukatar kulawa sosai saboda gashin ‘ya mace na cikin abin da yake kara mata kyau. Akwai abubuwa da dama wadda ya kamata ki yi amfani da su kamaru; man zaitun, zuma, man ‘castor’, ruwan lemun tsami, man kwakwa. Wadannan nau’ukan mai na da inganci sosai musamman ma wajen kare gashi daga tsinkewa da kuma sa shi karfi, santsi da sheki.

Man kasto: Man kastor (castor oil) na taimakawa wajen gyaran gashin kai a hunturu. A debo man kastor kamar cokali uku. Sai ki shafa a fatar kai sanan sai a taje a hankali. A tirara tawul har sai ya yi zafi. Sannan a daura tawul din mai zafi a kai na tsawon minti goma sha biyar. Bayan haka, sai ayi wanka. Yana hana gashi tsinkewa da hunturu.

Man zaitun da zuma: A hada cokali uku na man zaitun da cokali daya na zuma. A kwaba hadin har sai ya gaurayu sosai, sannan a shafa hadin a kan fatar kai. Bayan mintuna kadan, sai a wanke da ruwa da sabulun wanke gashi. Kwai, ‘binegar’ da man kwakwa A kada kwai daya, sai a sa man kwakwa cokali biyu da binegar. A hadin nan hadin waje daya. Sai a kwaba su. A sa hadin a fatar kai sannan sai a taje gashin kai. A bar hadin ya jima tsawon minti goma sha biyar. Sai a wanke da ruwan dumi.

Lemun tsami da man kwakwa: A hada cokali biyu na man kwakwa, cokali daya na ruwan lemun tsami. Sai a gauraya hadin har sai ya gaurayu sosai. Sannan a shafa a kan fatar kai. Wannan hadin na warkar da amosarin kai, da kuma hana gashi tsinkewa.

Man zaitun: Man zaitun na da matukar inganci musamman ma ga gashi mai gautsi. Fatar kai na saurin bushewa saboda hunturu. Idan ana da irin wannan kai, sai a dumama man zaitun a tukunya idan ya yi zafi, sai a shafa a fatar kai. A ci gaba da murza man a fatar kai har sai man ya shiga fatar sosai. Sanan sai barshi kamar tsawon minti goma sha biyar. Bayan haka sai a wanke.
Share:

Kula da fata a lokacin sanyi

Kula da fata a lokacin sanyi

Kula da fata a kowane lokaci yana da matukar muhimmanci, sai dai a lokacin sanyi fata tana bukatar kulawa ta musamman saboda yaushi ko yamutsewa da tsattsagewar da fatar kan yi sakamakon busawar iskar hunturu. Ga wasu hanyoyi wadanda za su taimaka wajen kare fata daga tsattsagewa a lokacin sanyi:­-

Kula da fata a lokacin sanyi


1.==> Shan ruwa mai yawa. Amfanin shan ruwa ga jikin dan adam yana da yawan gaske. Duk da cewa a lokacin sanyi mutane ba su fiye son shan ruwa ba, amma hakan babbar hanya ce wajen taimaka wa fatarsu ta kasance tana sheki tsawon lokacin hunturu. An so mutum ya sha ruwa kimanin lita biyu zuwa uku a rana. Sai dai wannan bai hada da shan shayi ba, a maimakon haka an so mutum ya yawaita shan lemo.

2.==> A yawaita shan kayan itatuwa da kuma ganyayyaki wannan zai sa fata shekki da walwali.

3.==> Idan an tashi wanka a yi da ruwan dumi. Duk da an san cewa a lokacin hunturu ana bukatar ruwa mai zafi musamman idan da safe za a yi wankan, sai dai ya zama wajibi anan a kaucewa yin amfani da ruwan zafi saboda yana haifar da yamutsewar fata da kuma kaikayi. An so mutum ya yi wanka da ruwa marar zafi sosai kuma wanka ya kasance na dan takaitaccen lokaci, ma’ana kada ya wuce tsawon mintuna biyar zuwa goma wajen wanka.

4.==> Ana so a rika yawaita goge jiki ‘scrubbing’ wannan shi zai sa duk wata matacciya da busasshiyar fata ta fita tare da ba wa sabuwar fata wuri don tofowa.
5.==> Shafa mai akan lokaci, mun san yadda jiki yake saurin bushewa saboda kadawar iska. A duk lokacin da aka yi wanka yana da kyau a shafa ma tun a bandaki lokacin da dan ragowar danshi a jikin fatar.

6.==> A zabi mai da ya dace da lokacin sanyi, ma’ana mai wanda ke da maiko wanda zai sa fata ta kasance cikin danshi na tsawon lokaci. Duk wani mai da zai zama ya sa fata tauri ba shi da amfani a wannan lokaci na sanyi. A wannan lokaci amfani da man kadanya ko man zaitun yana taimakawa fata kwarai da gaske.


7.==> Haka kuma akwai bukatar mutum kada ya manta da labbansa da kuma hannuwansa, kasancewar wadannan wurare suna da muhimmaci a jikin dan’adam kuma sanyi yakan yi musu illa don haka akwai bukatar koda yaushe mutum ya kasance yana tare da man lebe da kuma wani mai na hannu mai ruwa-­ruwa.
Share:

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger

A wasu sa’in mutum yakan so chanza kallar rubutunsa don ado ko kuma dan banbanta kalma tsakaninsa da suran. Ko ma dai me manufar mutum yake insha Allahu a wannan makon zamu tattauna ne game da yadda ake canza kallar rubutu a blogger wato wajen rubutun shafi a yanar gizo.

            A hakikanin gaskiya chanza kallar rubutu a shafin blogger ba wani abune mai matukar wahala ba ko kuwa yana bukatar wasu matakai masu tsauri ba. A’a sam bai da wani wahala face duk sa’in da mutum yake son canza kalar rubutu sai ya bi yan wasu matakai masu saukin gaske.

Matakai da ake bi wajen canza kallar rubutu a shafin Blogger  

1.==> Da fari mutum zai ziyarci wajen da ake posting ma’ana wajen da ake saka abunda aka rubuta wanda mukayi bayani dalla dalla a makon daya gabata Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger cikin sauki.

2.==> Yayin da mutum ya kammala rubuta abunda yake son sawa sai ya zabi kalaman dayake son chanza wa kallar ta hanyar yin highlighting nasu sannan ya danna mabullin Kalmar 'A' wadda yake dan sama ta bangaren hannunsa na dama sannan mutum ya zabi kallar da yake so.

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger


Za’a iya bin wannan matakan koda kuwa an sa kallar ana kuma son sauyawa.

Wannan shine takaitacciyar hanya da ake bi wajen chanza kalar rubutu a shafin blogger dafatan wannan ya taimaka matuka, a kasance tare da shafin Duniyan Fasaha dan samun sabin abubuwa da zasu amfaneku a yau da kullum. Naku a yau da kullum Jikan Marubuta Muhammad Abba Gana. Bissalam!! 
Share:

Yadda ake jus din gurji mai zobo

Yadda ake jus din gurji mai zobo

Yadda ake jus din gurji mai zobo


Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na girke girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha tare da fata ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau a san yadda ake yin nau’ukan girke girke da kuma mahadinsu. Ina nufin jus ke nan. Duk dadin abinci yana bukatar mahadi da zai dada wa girkin armashi. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake wata mahadar girki; jus din gurji.

Abubuwan da ake bukata

·              Gurji
·              Kankana
·              Ayaba
·              Lemu
·              Amfuna
·              Gwanda
·              Zobo
·              Flaba
·              Sakari
·              Citta
·              Kanumfari

Hadi

A sami gurji kamar goma sai a fere sannan a markadasu a na’urar markade a tatse ruwan a ajiye a gefe. A sami kankana a yayyanka kanana sosai a wata roba da ayaba da amfuna da gwanda duka a yayyankasu kanana sannan a ajiye a gefe.

A tafasa zobo da kayan kamshi kamar su citta da kanamfari da kuma bawon abarba. Sannan a tafasa sosai sannan a tace a ajiye ya huce sannan a zuba sukari da flaba sannan a sanya a gidan sanyi.


Bayan haka, a debo wannan ruwan gurjin a zuba a zobon sannan a zuba wadannan yankakken ’ya’yan itatuwan a zubasu a kofi sannan a zuba wannan jus din zobon. Ana sha ana tauna.
Share:

Yadda ake masa

Yadda ake masa

Yadda ake masa


Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi don yin masa. Yadda wata zata tsara na ta masar daban take da yadda wata uwargidan za ta sarrafa na ta. Akwai nau’ukan masa da dama kamar masar Gero da Dawa da Semo da kuma Shinkafa da dai makamantansu. A yau na kawo muku yadda ake masar Shinkafa a cikin hanya mai sauki ba tare da an bada ayi ko kuma a saya ba.

Ababen da ake bukata

·              Danyen shinkafa
·              Albasa
·              Man gyada
·              Yis da ‘baking powder’
·              Siga
·              Albasa

Hadi
A jika danyar shinkafa na tsawon awa daya sannan a wanke ta carak a zuba a cikin na’uran markade. Sannan a tafasa shinkafar kadan kafin ta nuna sosai sai a sauke a zuba a cikin wannan danyar shinkafar sannan a yayyanka albasa a kai sannan a markada har sai shinkafar ta yi laushi sosai sannan a zuba a cikin roba.

Bayan haka, sai a zuba yis a ruwan dumi kadan sannan a zuba a ciki. A sake dauko ‘baking powder’ a zuba a gauraya sosai sannan a rufe a sanya a rana har sai hadin ya tashi.

Sannan a dauko Tanda a daura a kan wuta. A zuba siga a roba da ruwa kadan yadda za ta narke sannan a zuba a kullun masar a sake gaurayawa . sannan a zuba man gyada kadan idan ya yi zafi sannan a debo kullun a zuba a ramukan tandar. Idan ya dan nuna sannan a sake juya masar zuwa dayan gefen domin ta nuna. Bayan ta nuna sannan a sauke a sanya a kwano.Za a iya cin wannan masar ko waina da yajin kuli ko miyar taushe ko kuma miyar Alayyahu. A ci dadi lafiya.
Share:

Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa

Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa 

Wani likita a fannin cututtukan mata a Nijeriya dakta Adewole Akintoyose ya yi kira ga mata da su jimirci cin kayayyakin itatuwa da na lambu domin kare kansu daga wata cuta mai hana haihuwa mai suna “endometriosis” a turance.

Adewole, wanda ma’aikaci ne a asibitin St Leo da ke unguwar Lekki a jahar Lagos ya ce wannan cuta ta fi yawaita a tsakanin mata ‘yan shekaru 25 zuwa 40.

A fadarsa, Cutar na yin lahani ne ga mahaifa da kuma kwayayen da ke jikin mace. Likitan ya ce alamomin cuta sun hada yawan ciwon mara, zafi a yayin saduwa, yawan gajiya, zafi yayin fitsari, da sauran su.

Sauran alamomin sun hada da rashin haihuwa da wuri, fara gani jinin haila da wuri, da daina haihuwa a lokacin da ya kamata.


Ya gargadi mata da su rage cin naman shanu, wanda ya ce ka iya haifar da cutar, ya kuma shawarci su da su kara yawan kayan itatuwa da na lambun da suke ci, wanda hakan na matukar taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cutar.
Share:

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa


Assalamu Alaikum! Ina yi mana gaisuwa wadda ta dace da al’umma. Allah Ya kara mana ni’imar rayuwa da zaman lafiya a kowane lokaci, Amin.

A wannan makon kuma, za mu duba muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwar dan Adam. Har kullum riba da nasara na nan ga mutumin da ya yi aiki tukuru a rayuwarsa. Domin kuwa komai ka gani a rayuwar nan, yana da sanadin faruwarsa, kamar kuma yadda babu yadda za a yi ka kama zomo ba tare da ka ci gudu ba. Duk wani abu mai kima da muhimmanci, ba a samunsa a haka nan, watau a bagas, kamar yadda masu iya magana kan ce.

Aiki tukuru ba yana nufin ka dawwama, tun daga fitowar rana zuwa faduwarta kan abu guda ba, a’a, ba haka ake nufi ba. Duk aikin da za ka yi, ka tabbatar ka ba shi isasshen lokacin da ya dace, kuma ka aiwatar da shi da gaske ba tare da kasala ba. Sannan ka tabbatar ka ware lokacin sararawa da lokacin cin abinci da lokacin yin ibada, sannan kuma da lokacin tashi daga aikin nan naka. Aiki tukuru na nufin ka yi adalci tsakaninka da aikin kansa da kuma yin adalci ga kai kanka da jikinka, sannan kuma ka yi wa wanda ya sanya ka aikin adalci. Da ikon Allah, za ka samu biyan bukata daidai gwargwado.

Gaskiya da rikon amana, abin dubawa ne wajen gudanar da aikinka ko sana’arka. Su ma wadannan sinadarai ne na sirrin samun nasarar aiki ko sana’a. Sai dai dole mutum sai ya dode kunnuwansa daga surutan mutane, domin a wannan zamani, duk wanda ya ce zai mayar da hankali kacokan ga aikinsa bisa gaskiya da adalci, zai zama wani bako a wurin aikin nasa, domin za a rika kiransa da wasu sunaye na shagube. Za ka ji ana cewa ‘ina ruwan agogo sarkin aiki!’ Ko kuma a rika ce masa ‘Gadu mai aikin banza!’ Ko kuma saboda tsare ka’idar lokaci da ba komai da kowa hakkinsa, sai ka ji ana ce masa ‘wane bai waye ba.’

Irin wadannan maganganu, kada ka yarda su karya maka gwiwa, kada ka amince su maido da kai baya. Duk abin da za ka yi, ka tabbatar kana da yakinin yinsa a zuciyarka, ka tabbatar bisa dokar aiki yake. Idan ka yi haka, komai daren dadewa, kai ne kan nasara, kuma za ka gane amfanin tsare aikin naka, za ka ga ranarsa, wata rana. Domin kuwa duk abin da ka bauta masa, sai ka ci gajiyarsa. Duk abin da ka sadaukar da lokacinka da karfinka da tunaninka wajen aiwatar da shi, to babu shakka ba zai fadi kasa a banza ba. Za ka samu sakamakonsa, komai tsawon lokaci.

Wannan al’amari, kamar yadda misalai suka gabata, mujarrabi ne. Idan ba ka amince ba sosai, tsaya tsaf da ranka ka natsu. Dubi tarihin wani magabaci da kake ganin ya ci nasarar rayuwa, ko kuma ya kai kololuwar nasarar aikinsa ko kasuwancisa. Yi masa tambaya cikin kwanciyar rai, ka ji irin surkukin dajin wahalar da ya ratsa kafin ya kai ga wannan matsayi. Na tabbata idan dai ya ba ka labarinsa tiryan-tiryan, za ka iske cewa ba haka nan ya samu nasarar ba. Ba yana zaune haka siddan aka ba shi nasarar ba. Don haka, raggo dai ba ya suna, kuma duk wanda bai tsaga ba, ba zai ga jini ba, wanda duk bai gina rijiya ba, ba zai samu ruwa ba.

Don haka, kai dai maida hankali ga aikinka, komai kankantarsa, komai rashin ingancinsa, ka yi amanna, sannan ka ci gabadaaiwatar da shi. Babban burinka da farin cikinka na nan tafe wata rana. Babu mamaki ba za ka zama gagarabadau ba a fagen naka, amma dai za ka iya kawo canji na alheri ta wanan aiki naka. Watakila ba za ka iya zama farin wata gama duniya ba, amma kana iya zama wata karamar tauraruwa mai haska ma wasu hanya, a rayuwarsu. Domin a rayuwar nan tamu, ba a taru aka zama daya ba. Zama ne na ’yan marina, kowa da inda ya sanya gabansa.


Babban darasinmu na yau shi ne, kada mu karaya, mu jajirce mu yi aiki tukuru, bisa amana da adalci da gaskiya. Allah Ya taimaka mana, amin. Sai kuma mako na gaba idan Allah Ya kai mu. Wassalam!
Share:

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


Email yakan bamu damar tura abubuwa da dama kama daga rubutaccen sako, sauti, hoto da kuma hoto mai mosti cikin sauki zuwaga abokan hulda ko kuma abokan arziki. A makon daya gabata nayi cikakkiyar bayani dalla dalla ma’anar sa da kuma yadda ake bude shi tare dashi gmail. A wannan karon kuma insha Allahu zan nuna muku hanyar da ake bi wajen shiga account na gmail din da aka bude.

Matakin Farko: Mutum zai ziyarchi addreshin gmail din wato www.gmail.com zai kaisa izuwa ga shafin nan wanda shine babban shafinsu na shi gmail.
A sama can bangaren hannun dama mutum zaiga inda aka rubuta “Sign in” wanda ma’anar sa a hausance shiga ciki. ba lallai bane mutum yaga wannan shafin mafi yawancin lokutan yana kai mutum ne izuwa ga mataki na biyu koda yake ya dan ganane da wani irin browser mutum yake aiki dashi ko kuma wani irin salula mutum ke aiki dashi a mafi akasarin lokutan yana nunawane wa masu aiki da chrome browser ko kuma masu aiki da kwanfuta.

Mataki na Biyu:  za’a umurci mutum yasaka email nasa a dan akwatin dake k’asan nan misali email namu na shafin nan shine duniyanfasaha@gmail.com sai na sanya shi a cikin akwatin tare da latsa ma bullin “Next” 

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


wanda zai bada damar zuwa mataki nagaba. Akwai wasu sa’in da zai rubuta wa mutum “Email not found” kodai maka mancin haka yana gayawa mutum cewar email daya sanyan nan ba dai dai bane wata kila an yi tuntuben kalma wajen rubutu dole mutum ya lura a lokacin da yake rubutawa dan gujewa kuskure.  

Mataki na Uku: Zai tambayi mutum ya sanya numbobin sirri wato wanda aka fi sani da password a turance, sai mutum ya sanya shi tare da latsa mabullin “Next” 
Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki

in dai mutum ya sanya numbobin sirrinsa daidai zai kaisa izuwa ga account nasa in kuma ba dai dai bane zai fito da wani rubuta mai kala ja dauke da “incorrect password” ko kuma “wrong password” koma wanne ya sanya maka daga ciki yana gaya maka cewar numbobin sirrin ba daidai bane sai ka goge su sannan ka canza zuwa wani wanda ka sanya a lokacin da kake budewa.


Wannan shine cikkakiyar hanya da ake bi wajen shigan email naka na gmail ku kasance tare da Duniyan Fasaha don samun sabbin ababe da zasu amfaneku a al’amuran yau da kullum.      
Share:

Yadda za a magance kodewar fata

Yadda za a magance kodewar fata

Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin neman halaliyarsa ko kuma don yini a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka. Wannan abu ya fi aukuwa ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da dan haske. Wannan abu ba a sanin lokacin da suke faruwa. Shi ya sa a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi don neman kariya daga wadannan kunar ranar ko kuma kodewar fata.

Ruwan dankalin turawa; a fere dankalin turawa sannan a wanke sai a kankare a matse ruwan sannan a rika shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. Yin haka na magance matsalar fatar sannan kuma yana kare sake aukuwar hakan.

Madara; a samu madara a sanya a gidan sanyi har sai ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul karami a rika tsomawa ana goge fuskar da shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma tana warkar da wannan kodewar fatar.

Ruwa; a yawaita shan ruwa sosai idan ana dauke da wannan matsalar sannan za a iya sanya ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa wannan kankarar a inda fatar ta kode.

Gurji; a samu gurji sannan a yanka sannan a sanya a gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.

Koren ganyen shayi; za a iya tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan sun tafasa sannan a bari hadin ya jiku kamar na tsawon sa’a daya sannan a sanya a gidan sanyi, sannan a wanke fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.

Ganyen ‘aloe bera’; a samu wannan ganyen sannan a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa a fuskar a kullum har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a fatar mu don haka yana da kyau a kowane gida a shuka.

Ruwan tuffa; za a iya samun wannan ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika shafawa a fuska har sai ya bushe. Haka za a rika yi a kullum.


Masu karatu kada su hada duka wannan hadin su ce za su yi shi a lokaci guda. Sai dai su zabi daya daga cikinsu. Hada wadannan ababen da na lissafo na iya haifar da wata cutar fatar fuska. Da fatan za a kiyaye.
Share:

Tuwo miyar kuka

Tuwo miyar kuka

Assalamu Alaikum Uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake tuwo miyar kuka. Lallai wannan irin girki ne wadda yara da dama basu cika so ba. Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa. Ko kun san cewa wannan miyar ba ta karamin gida bace idan har an san yadda za a sarrafa ta?
Wannan miya ce ba na hana yaro kuka ba, har ma da manya. Domin babu abin da ya kai ta sauki wajen hada ta musamman idan aka hada da tuwon masara ko dawa. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata

·           Kuka
·           Tafarnuwa
·           Banddar kifi
·           Kaza/nama
·           Citta
·           Attarugu
·           Albasa
·           Magi
·           Kori
·           Man shanu
·           Daddawa

Hadi

Da farko Uwar gida za ta wanke kazarta ko nama yadda ya kamata sannan ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da tafarnuwa da daddawa sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da magi da kuma kori.

Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo garin kuka a rika kadawa kadan-kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba. Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke.

A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.
Share:

TALLA

LOKACI

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *