Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Shan Lemuna Masu Sikari Na Haifar Da Cutar Rudewa A Lokacin Tsufa

Shan Lemuna Masu Sikari Na Haifar Da Cutar Rudewa A Lokacin Tsufa

Shan Lemuna Masu Sikari Na Haifar Da Cutar Rudewa A Lokacin Tsufa


Masana sun gano cewa akwai alaka mai karfi tsakanin shan lemunan da ke dauke da sikari da cututtukan da suka shafi kwakwalwa musamman kamar cutar rudewa da cutar mantuwa.

Wadannan cututtukai dai sunfi kama mutane a lokacin tsufa

A baya dama binciken kimiyya ya alakanta shan irin wadannan lemuna da cututtuka kamar su ciwon zuciya, rubewar hakori, shanyewar jiki, kiba da ciwon sikari.


A yan kwanaki da suka shudene aka wallafa rahotan binciken guda biyu da ke alakanta shan lemuna da cututtukan mantuwa da rudewa (Alzheimer’s and Dementia) a kundin ilimin likitanci biyu masu suna ‘Medical Stroke Journal’ da ‘Alzheimer’s and Dementia’ Wadanda suka gudanar da binciken masana ne a jami’ar koyar ilimin likitanci da ke garin Boston a kasar Amurka.
Tura Zuwa:

Yadda ake hada ’Yar tsala

Yadda ake hada ’Yar tsala


Assalamu Alikum barkan mu da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha, Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatan alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake hada yar tsala. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma iya sarrafa girki dabandaban da kayan marmari. Don haka dole ne mace ta dage wajen taka rawar gani a harkar girki tare da koyon kowane irin salon girki.

Kayan hadi:

==> Gero
==> Mangyada
==> Yis
==> Gishiri
==> Dakakken yaji mai kulikuli

Yadda ake yi:

Za a surfa gero sannan a bushe a wanke sai a shanya, idan ya bushe sai a kai a niko a tankade shi, sai kuma a jika yis da ruwan zafi. Sai a dauki ruwan yis din a kwaba garin geron da shi bayan an sanya masa gishiri.

Idan an gama kwabawa sai a bar shi ya dade kamar misalin sa’a biyu zuwa uku, ya danganta da yanayin gari, ma’ana idan lokacin zafi ne ba sai ya dade sosai ba. Idan kullin ya kumbura ko ya tashi sai a dan kara ruwa a juya ana son kwabin ya zama da dan ruwaruwa.

Idan aka gama hadawa sai a asa cokali a rika diba ana soyawa a cikin mangyada. Idan ’yar tsalar ta soyu sai a kwashe. Ana ci da yaji wanda ya ji kulikuli sosai.
Tura Zuwa:

Yadda za ki lura da hakorinki


Yadda za ki lura da hakorinki


Hakora na daya daga cikin abubuwa da ke fitar da kyawun mace. Don haka ya kamata a ba su kyakkyawar kulawa. Wadansu matan sukan shiga halin tasku, inda ko an yi abin dariya sai su rufe bakinsu da hannu kafin su yi dariya, saboda halin da hakoransu suka samu kansu a ciki. A wannan makon mun taho miki da hanyoyin da za ki yi amfani da su wajen lura da hakoranki.

Ga abubuwan da ya kamata ki yi da kuma wadanda za ki gujewa don samun lafiyayyen hakori.

Abin da za ki yi don samun lafiyayyen hakori

==> Za ki iya amfani da jus din lemon tsami ko kuma ruwan lemon tsami wajen cire dabbaredabbaren rawaya da ke hakora. Idan lemon tsami ne sai ki yanka, sannan ki matse ruwan, daga nan sai ki kurbi ruwan, sannan ki kuskure bakinki. Za ki iya amfani da hannunki wajen cuccudawa.

==> Idan kina so hakoranki su yi fari, kuma abin sha’awa, sai ki samu ‘ya’yan itacen Strawberries, sai ki yayyanka, daga nan sai ki yi buroshi da su.

==> Idan kika goge hakoranki da ruwan lemon zaki ma yana sanya hakora su yi haske.

==> Idan akwai datti ko dabbare-dabbare a hakoranki, sai ki samu gishiri, ki kuskure bakinki da shi. Ki dangwali gishiri da yatsanki, sannan ki cuccuda hakoranki.

==> Cin ‘ya’yan itatuwa da alayyahu na cire dabbare-dabbare a hakori.

==> Ki samu buroshin goge baki, sai ki dangwali sinadarin hydrogen perodide, sannan ki goge hakoranki da shi.

==> Idan kin ci abinci sai ki goge bakinki, hakan zai sanya hakoranki su yi kyau da kuma sheki.

Abin da ya kamata ki gujewa;

==> Ki guji yawan shan abubuwan da ke dauke da sinadarin carbon (Carbonated drinks), wadannan abubuwan shan suna dauke da sinadarin acid din da ke kashe hakora, sannan ya sanya su samu dabbare-dabbaren rawaya.

==> Ki guji yawan shan kofi (Coffee) ko Nescafe,domin suna sanya hakora su yi duhu.

==> Ki guji yawan cin goro ko shan sigari, domin suna dauke da sinadarin nicotine da ke kashe hakora da kuma sanya hakora su yi duhu.


==> Ki guji yawan sha zobo domin yana sanya hakora su yi duhu.
Tura Zuwa:

Ababen da ke magance matsalar qurajen fuska da fata

Ababen da ke magance matsalar qurajen fuska da fata

Ababen da ke magance matsalar qurajen fuska da fata


Assalamu alaikum masu karatu tare da fatan ana lafiya? Bari in yi muku wata tambaya. Shin mene ne wadannan abubuwan da ke magance matsalolin fata?

Lallai wadannan abubuwa ne, wanda a kullum mukan yi amfani da su a dakin girki ko kuma amfani da su a abinci. Idan aka koyi yadda ake amfani da su a fata, domin magance matsalolin fata, lallai ba sai an kashe kudi da dama ba wajen sayen magani.

Ina son in gargadi masu karatu da su gane cewa a cikin abubuwan da zan lissafo, daya kawai ake so a riqa amfani da shi wanda ta dace da fatar mutum. Amfani da su gaba daya na qara haifar da wata matsalar fata. Yana da kyau a gwada amfani da su tsawon watanni biyu zuwa uku.

==> Domin magance matsalar fata mai yawan saba ko masu samun barewar fata daga fuskarsu ko wata bangare a fatar jiki, sai a samu suga mai launin qasa da zuma da madara kadan yadda sugan ba zai narke ba, sai a shiga dirzawa a fuska ko wani bangaren da matsalar ta shafa.

==> Qarin haske: idan fuska ta kasance tana yin baqi a sakamakon yawan fita rana ko kuma canjin yanayi, yana da kyau a kwaba ayaba, sannan a hada da zuma da kuma lemun tsami sai a riqa shafawa a qalla sau biyu a rana na tsawon mintuna ashirin kafin a kwanta barci.

==> Sheqin fata: samin fatar fuska mai sheqi, sai an dage da cin kankana da kuma kwabata da cokali sannan a riqa shafawa a fuska ko jiki na tsawon mintuna talatin a qalla sau biyu a rana sannan a wanke.

==> Tsagewar lebe: Iidan lebe na yawan tsagewa ko kuma bushewa, sai a samu man kwakwa da siga sai a dan diga man kwakwa da sukari kadan, sannan a shiga dirza sukari a lebe na tsawon mintuna biyu zuwa uku, sannan a wanke. A kasance yawan shafa man kwakwa a leben.

==> Gautsin fata: gautsin fata na hana fata sheqi. Don haka, yana da kyau a kasance amfani da fiya da ruwan lemun zaqi. A kwabasu waje daya sannan a riqa shafawa a waje mai gautsin domin magance matsalar.


==> Fesowar quraje: a kasance ana amfani da ruwan qwai ban da gunduwar sannan a riqa shafawa a fatar fuska a kullum na tsawon mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin a wanke sau biyu a rana domin samun biyan buqata.
Tura Zuwa:

Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba

Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba

Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba


Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku daga mujallar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zanyi jawabine bisa yan wasu sakonni dana samu daga gareku ma’abota karatun shafinnan tambayar anyi ta kusan guda takwas amma duk alkibla daya suka dosa tambayar tana nan kamar haka; indan madannan wayar mutum na android wato guda ukunnan da aka tanadar sun daina aiki shin akwai wata hanya da mutum zai bi wajen aiki da abinsa kafin Allah ya hore masa kaiwa gyara koh siyan wata sabuwa? 

Bisa la’a kari madannin wayar android wanda aka fi sani da sensor a turance wata fasaha ce da aka tanadar wanda yake taimaka wa wajen aiki da ita wayar salulan, saidai bisa yanda aka hada abun bai cika jure wata wahala ba, misali idan wayar ka ta android ta samu subucewa daga hannunka kodai ya zamo daga samar wani abu zuwa kasa in Allah ya sa faduwan ba,ayi a sa’a ba za’a ga wannan madannin ya daina aiki gaba daya ko kuma wayannan madannan sukan daina aiki wasu lokutan ma ba lallai sai ya fadi ba yakan iya daina aiki idan ruwa ya shigesa ko ma dai haka kawai in lokacinsa yayi.

Toh a hakikakin gaskiya akwai hanyoyi da dama wanda mutum zai bi wajen aiki da wayar salulansa na android ba tare da wayannan madannin ba amma insha Allahu yau dai zan nuna muku daya daga cikin hanyan mafi sauki a cikinsu.
Wannan hanyar zaka iya amfanin da wayar salulan ka ba tare da ka damu da canza madannin (sensor) ba ko kuma siyan wata sabuwar wayan ba wannan hanyar mun tabbatar yana aiki a koda yaushe ga kuma yanda akeyi.

Matakai

Abu nafari da zamu fara yi anan shine saukar da wata manhaja (application) daga Google Playstore mai suna “Soft keys – HomeBack Button” za’a iya saukarwa ta hanyar latsa nan. Hakikanin gaskiya Za’a iya raina wannan application amma yana aiki kuma yana taimaka matuka. Bayan ka saukar ka fitar dashi zuwa gidan wayar ka (install application).

Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba


Bayan ka kammala installing na application din sai ka bude zai kai ka izuwa ga pagin san na farko a yanzu zaka iya gyara wasu tsari zaka kuma iya canza wasu tsari daya zo dashi amma kafin mu ci gaba akwai wani saitin da ya kamata ayi domin bai wa application din damar cika aiki wanda zai sanar da kwakalwar wayar ga abinda yake son aikatawa. Yanzu zaka je izuwa ga saitin waya wato (settings) sai kaje izuwa ga>> (All settings) sai kuma ka shiga >> Accessibility zaka ga sunan application din da mukayi installing a baya mai dauke da “soft keys – Home Back Button” sai ka latsa kai.

Yanzu anan akwai dan wani seti da zamuyi masa domin basa damar ciki aiki. a saman fuskar wayarka ta dama zaka ga dan wani mabulli inda akan iya kashewa akan kuma iya budewa sai ka latsa kai ma’ana ka kunna shi.       

Zaka kuma iya kunnashi ta hanyar danna “settings – Accessibility” wanda yake rubuce a cikin application yayin ziyaranka na farko ciki zai kaika izuwa wajen da setting wayarka yake zaka ga sunan application din da mukayi installing a baya mai dauke da “soft keys – Home Back Button” sai ka latsa kai. A saman fuskar wayarka ta dama zaka ga dan wani mabulli inda akan iya kashewa akan kuma iya budewa sai ka latsa kai ma’ana ka kunna shi.      

Toh yanzu ka baiwa application naka damar aiki a cikin wayar salulanka na android saidai haryanzu akwai wasu seti da ya kamata mu yi domin zama yanda ya kamata a cikin wayarka na salula. Yanzu zamu koma cikin hajarmu (application) da mukayi installing a baya.

Abu na fari wanda yake cikin hajar(application) din bayan ka bude shine “Navigation bar location:” wannan shine wajen da zaka saita madannai uku wanda zasu fito a cikin wayar salulanka shin ta sama kake so su zauna ko kasa ko ta hannun dama ko kuma ta hannun hagu wannan ya dangana ne da yanda kake so kamar ni nafi so yayi zaman sa a kasa shine na zabi down in kaima kana bukatan hakan sai ka zabi ‘down’ ma’anar sa a hausance kasa.

Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba

Abu na biyu a jerin ababen shine “new icons” wannan wata damace wanda yake taimakawa in kanaso kayi amfani da suran madannai uku wanda wayan zamani suke zuwa dashi zaka iya latsa wannan mabulin domin tabbatarwa.

Abu na uku a jerin ababen da muke gani a cikin hajar(application) din shine “back button on the left” wannan aikin sa shine taimakawa wajen canza mazaunin ‘koma baya’ wanda aka fi sani da back button a turance in kana bukatar mai da shi izuwa ga hagu sai ka canza zuwa left In kuma kana so ya koma izuwa dama sai ka zabi right.

Abu na kusa da karshe cikin jerin ababen da suke dauke a cikin hajar(application) din shine ‘size’ ma’anarsa a hausance shine girma in kana bukatan madannan su zama manya zaka iya ja daga hannunka na hagu zuwa dama in kuma kana bukatar ka rage girman sa zaka iya ja daga hannunka na dama zuwa hagu nan dai shima ya danganane da yanda kake son girmansa.

Abu na karshe a jerin abubuwan da suke kunshe a cikin hajar(application) shine ‘Transparency’ wannan yana taimakawa ne idan kana son ka kara hasken baya na madannan wanda suka fito a fuskar wayanka ko kuma kana so ka rage hasken bayan sa zaka iya gyarawa anan.


Alhamdullilah wannan shine wasu matakai da zaka bi wajen aiki da madannai uku na wayar salulanka na Android idan sun samu damuwa ko kuma suna wahalar dannuwa dafatan wannan rubutun ya taimaka sosai.  
Tura Zuwa:

A rayuwa, ko ka san inda ka sa gaba kuwa?

A rayuwa, ko ka san inda ka sa gaba kuwa?

A rayuwa, ko ka san inda ka sa gaba kuwa?


Ga masu bibiyar wannan shafi na Duniyan Fasaha, ina yi maku sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu Alaikum. Bayan haka, a wannan makon kuma, za mu yi ninkaya ne a cikin sabon maudu’i, kamar yadda muka nuna a sama.

Kafin mu shiga tsokacin namu kai tsaye, mu fara da wani takaitaccen labari, wanda shi ne zai share mana hanya, domin fahimtar jigon madu’in namu.

Wani manomi ne da ya mallaki wani kare mai karsashi da kazar-kazar. Karen nan ba ya zama ko’ina sai bakin titi kuma halinsa ne a duk lokacin da mota ta zo wucewa a hanyar, sai ya rika bin bayanta da gudun tsiya da nufin sai ya wuce ta. Haka yake yi a kowane lokaci, tare da haushi mai karar tsiya.

Kan haka ne sai makwabcin manomin nan ya yi masa tambaya: “Malam, wai shi karen nan naka, kana ganin akwai ranar da zai iya cin ma mota a wurin gudu kuwa?”

Jin haka sai manomin nan ya amsa masa da cewa: “Ni ba ma abin da ke damuna ba ke nan. Ni abin da nake tunani kuma yake damuna shi ne, idan ma har ya yi nasarar cin mata, to me zai yi kuma? Me zai samu da zai amfane shi, idan ya kamo motar da yake bi ko kuma idan ya tsere mata?” Wannan shi ne labarin manomi da karensa da kuma tambayar da makwabcinsa ya yi masa. Idan mun nazarci labarin nan a tsanake, za mu iya ganin darussa masu kyau da za mu iya koya a rayuwarmu ta yau da kullum. A rayuwarmu ta yau da kullum, akwai mutanen da suka yi kama da karen manomin nan, wadanda ke gudanar da rayuwarsu ba tare da sanin hakikanin inda suka sa gaba ba. Ma’ana, kamar yadda karen nan yake bin motoci da niyyar sai ya wuce su ko kuma sai ya kamo su, alhali babu wani abin da zai amfana daga haka, to haka ma wasu mutane ke yin wasu ayyuka na babu-gaira-babu dalili, ayyukan da ba za su amfane su ba a rayuwa. Ta haka za ka ga sun dauki wata hanya, wacce ba su ma san dalilin daukar ta ba, haka kuma ba su san ma inda suka nufa ba a rayuwa. Yin haka kuwa ba karamar asara ba ce, domin kuwa ga duk mai yin haka, babu abin da zai samu sai faduwa da asara.

Bari mu sake bibiyar maudu’in nan namu da misalai na zahiri, domin mu kara fahimtar abin da yake koyar da mu. dauki misalin dan makaranta, wanda a kullum ake bukatar ya rika zuwa makaranta domin daukar darasi. Shin me ya kamace shi ya yi? Kamata ya yi ya fahimta da cewa ya sa gabansa ne wajen neman ilimi. Ilimin da zai samu kuma zai zame masa mai amfani a duk tsawon rayuwarsa. Idan dalibin nan ya fahimta da cewa lallai ga inda ya sa gaba, to wannan za ta ba shi damar ya maida hankali ga zuwa makaranta a kan lokaci, ba fashi. Sannan kuma zai ba da kokari wajen yin karatu da nazari, domin ya samu nasarar cin jarabawa.

A daya bangaren kuma, idan dalibin nan ya zabi ya yi koyi da rayuwar karen manomin nan, to sai ya yi watsi da makaranta. A makwafinta sai ya dauki wani aiki marar tasiri da muhimmanci, ya rika gudanarwa. Misali, yana iya daukar tadar nan ta kallon kwallon Turawa. Kullum shi ne bata lokaci wajen kallo, dare da rana. Shi ne karance-karancen labarinsu da kokarin sanin abin da suke ciki. Za ka ga ya haddace sunayen ’yan kwallo na kungiyoyi da yawa, ya san yawan kudin da suke samu, ya san kudin da wata kungiya ta zuba, ta sayi dan wasa kaza, da sauransu. Ta haka dai za ka ga dukkan al’amuransa sun ta’allaka ga al’amuran wannan kwallo.

Idan zan tambaye ka, a matsayin wannan matashi na dalibin makaranta, me kallon kwallon Turawa zai tsinana masa? Ashe wannan aiki da ya tanadar wa kansa bai yi daidai da aikin da karen manomi ya diba wa kansa na bin mota ba? Yadda karen nan ba zai amfana da komai ba, haka shi ma dalibin nan ba zai samu komai ba a rayuwarsa. Iyaka abin da zai samu shi ne, dala miliyan kaza Rooney ke samu, kungiya kaza ta sayi Ronaldo kan dala miliyan kaza... illa iyaka.


Don haka, kada mu yi koyi da aikin karen manomi, mu rika yin aikin da zai amfane mu a rayuwa. Mu tabbatar mun san alkiblar da muka dosa tun kafin mu fara tafiya. Ta haka ne za mu samu nasarar al’amuranmu na rayuwa, domin kuwa ta haka ne za mu kauce wa abin nan da Hausawa ke kira ‘zuwan kare a karofi, ba rini ba matsa.’ Allah Ya taimake mu, Ameen.
Tura Zuwa:

Yadda za ki yi amfani da fiya da ayaba wajen gyaran jiki

Yadda za ki yi amfani da fiya da ayaba wajen gyaran jiki

Yadda za ki yi amfani da fiya da ayaba wajen gyaran jiki


Fiya da ayaba na matukar taimakawa wajen gyara fatar jiki, sukan sanya fata ta yi sheki da kuma laushi. Kayan hadi:

·     Ayaba
·     Fiya
·     Yogot
·     Man zaitun

Yadda za a hada:

1==> Daga farko ki samu ayaba, sai ki bare, ki yasar da bawon, daga nan sai ki samu fiya, ki bare ta, sai ki zubar da bawon. Bayan nan sai ki hada ayaba da fiya da kuma kwallon fiyar, sannan ki daka.

2==> Bayan kin gama dakawa, sai ki zuba yogot da kuma man zaitun. Za ki ci gaba da cakudawa har sai kin tabbata komai ya gaurayu.

3==> Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki har na tsawon minti 15.


4==> Bayan nan, sai ki wanke fuskarki ko sauran jikinki da ruwa mai dumi.
Tura Zuwa:

Yadda za ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi

Yadda za ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi

Yadda za ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi


Sau da yawa masu fama da kyesbi sukan ce kyesbin ba ya jin magani, har sukan yi masa kirari da ‘kyesbi; tsoho mai ran karfe’. Idan wannan ce matsalar sai mu ce ki sha kuruminki, domin mun taho miki da hanyoyin da za ki bi wajen magance kyesbi.

1==> A karon farko, ki samu man kade wanda ba a sanya masa wani abu ba. Misali, man kade da ba sanya turare ko aka hada shi da wani mai ba.

2==> Kafin ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi, yana da kyau ki shafa man a wani bangare na jikinki, misali, a kumatunki ko gefen kunnenki, kasancewar man kade na haifar da matsala ga wata fata. Idan bayan kin shafa man bai kuma haifar miki da matsala ba, sai ki yi amfani da shi wajen magance kyesbi.

3==> Ki samu ruwa mai dumi, sai ki debi man kade, sannan ki zuba kofin shan shayi daya na gishiri a cikin ruwan da za ki yi wanka. Bayan kin yi wanka sai ki tsane jikinki da tawul mai kyau da kuma tsabta.

4==> Daga nan sai ki shafa man kade a jikinki da kuma wurin da kyesbi ya fito miki, sannan ki rika yin tausa (massage) a wajen. Za ki iya yin hakan sai biyu a rana.

5==> Bayan kin shafa man kade, sai ki guji sanya tufafi mai kauri, ko kuma mai kaushi wanda zai rika sosa fatar jikinki.

Wadansu hanyoyin magance kyesbi:

1==> Daga farko ki wanke duk wurin da akwai kyesbi da ruwa mai dumi, daga nan sai ki goge wurin da tsumma mai tsabta. Bayan nan sai ki samu man E45, sai ki shafa a wurin. Yin hakan zai magance kyesbi.


2==> Amfani da man da ke dauke da sinadarin ‘hydrocortisone’ na magance kyesbi. Daga farko ki yi wanka da ruwa mai dumi. Bayan nan sai ki shafa man. Ire-iren wadannan man suna busar da kyesbi. Amma kafin a yi amfani da ire-iren wadannan man kamata ya yi a nemi shawarar likitoci.
Tura Zuwa:

Kwalliyar Sallah

Kwalliyar Sallah

Kwalliyar Sallah


Barkanmu da Sallah tare da fatan ana cikin koshin lafiya? Allah Ya karbi ibadunmu na alheri Ya kuma maimaita mana wannan rana. Ina so na janyo hankalin ’yan uwana mata musamman matan aure da su kasance masu yin ado ga mazajensu, kamar yadda aka yi mana nasiha a lokacin da muke amare. Don haka a dage wajen amfani da turaren wuta domin tsaftace muhallinmu da dakunanmu saboda jin dadin iyalanmu.

Ga kadan daga cikin hanyoyin da suka kamata uwargida ta bi don ganin an samu biyan bukata:

==> Uwargida ta tabbata ta dage wajen amfani da turaren wuta; a samu kaskon turare a zuba garwashi sannan a zuba turaren wuta a dora kabbasa a kai sannan a dauki zanin gado a rufa a don turara shi a duk lokacin da zaa shinfida a kan gado hade da labule da kuma kayan da za ta sanya a jikinta. Lallai wannan turare na dadewa sosai a jiki.

==> Kitso; uwargida ta dage da yin kitso a kalla sau biyu a wata musamman idan ta kasance mai yawan ‘ya’ya. Amma an fi so a duk sati maigida ya rika ganin matarsa da sabon kitso. Ta kasance tana shafa wa gashinta mai don hana fesowar amosanin ka da kuma rage tsinkewar gashi.

==> Lalle; jan lalle irin namu na gargajiya na da kyau sosai. Uwargida ta kasance wajen shafa wannan lalle a tafin kafarta a kodayaushe domin ban da adon da yake yi yana kuma bayar da kariya ga lafiyar mace. Idan ba za ta samu damar yin lallen a kodayaushe ba, to ta kasance tana shafawa a kalla atafukan hannayenta.

==> Dinki; kada uwargida ta ce za ta daina yi wa maigida kwalliya saboda ta manyanta. Ta dage wajen yin dinki irin na zamani don burge maigida a gida amma dai kada ta manta da sanya hijabi a duk lokacin da za ta fita zuwa unguwa.

==> Gyaran fuska; a kwai wata irin kwalliya wacce ’yan matan yanzu ke yi. Kamar sanya jan baki da gyaran gira. Sannan ina kira ga mata da su dage wajen yin kwalliya irin ta zamani, ko da sun manyanta ne, don haka na karfafa soyayya a tsakanin ma’aurata.

==> Daurin dan kwali; idan Uwargida tana gida ta kasance mai yin daurin dan kwali irin na zamani don jan hankalin maigida. Kada ta bari a bar ta a baya ta rika ganin wai ta tsufa. Za ta iya koyon irin wannan daurin dan kwali daga wajen ’ya’yanta mata ko kuma ’yan uwanta da kuma makwabta. Yana da kyau kowace mace komai tsufanta ta rika tafiya da zamani.


A yi sallah lafiya.
Tura Zuwa:

Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar take?

Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar take?

Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar take?


Abin bakin ciki da damuwa game da batun matasan kasata Najeriya.  A kullum mu ake ji  Kullum sai dada lalacewa muke yi da rashin sanin abin da muke yi. Ga rashin tabbas da rashin madogara.  Ko laifin wa ye? Iyaye ko ’ya’yan ko duka?

A tawa fahimtar, duk kuwa da cewa a wajen Huasawa karamin sani matsala ce, kuma kasancewa a kullum abin da babba ya hango, karami ko ya hau bishiya ne ba zai iya hangowa ba, amma dai a batun matasan nan musamman na kasata Najeriya, lallai akwai gyara da yawan gaske, kuma akwai kura-kurai da dama da suka yi sanadiyyar wannan matsala daga bangarorin ’ya’yan da kuma iyayen.

Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar take?Babbar matsalar tana wajen ’ya’yan ne, amma kuma tushen matsalar daga iyayen ne. Ya kamata mu fahimci bambanci tsakanin kamarin matsala da kuma tushensa. Hausawa suna cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun damar shiga. Ashe ke nan sai iyaye sun gaza ne yaro ke samun damar shiga wani hali, har ya fi karfin iyayen da ma al’umma baki daya. Allah Ya kiyaye.

Tushen lalacewar matasa a yanzu daga iyaye ne. Ina fada da babbar murna, saboda dalilai d azan zayyana.

Da farko dai wanda kuma shi ne babban dalilin lalacewar ’ya’ya shi ne yadda iyayen suka manta ko kuma suke jahilci baban dalilin da Allah Ya ba su ’ya’yan. Sun manta cewa Allah Ya ba su amana ne na ’ya’yan kuma zai tambayesu amanar da ya ba su. Yawancinsu sun dauka kawai su yi aure su hayayyafa shi kenan, har za ka ji suna cewa ai Manzon Allah ma ya ce mu yi aure mu hayayyafa. Wa ya fada Manzon Allah zai yi alfahari da sakarai ko barawo da dan iska? Manzon Allah zai yi alfahari ne da ’ya’ya masu albarka, wadanda da sauke nauyin da Allah Ya dora maka a kansu ta hanyar tarbiyantar da su bin hanya madaidaiciya.

Abin ban mamaki ga irin wadannan iyayen shi ne: Za ga gansu kullum tsaf tsaf abin ban sha’awa, za ka su yawanci suna dar dar da cin amana. Idan ka ba su amanar dukiya ko wani abun duniya, suna kokari su rikewa da kyau. Amma kash! Ba sa iya rike amanar Allah. Abin takaicin shi ne yadda suke tsoron abin da mutane za su fada a game da su, amma kuma ko kadan ba sa tsoron abin da Allah zai fada a idon dukan halittu ranar gobe kiyama a game da amanar da Ya ba su, sannan kuma duniya su gane cewa maciya amana ne, duk kuwa a duniya mutane suna musu kallon masu amana.

Don haka dole iyaye su gane cewa fa iyaye amana ne, kuma Allah zai tambayesu a game da amanar da Ya ba su. Kuma babbar amanar ita ce na ku kiyaye kanku da iyalanku daga shiga wuta. Maganar nema wa danka aziki wannan na Allah ne. Shi yake azirta wanda ya so. Don haka babban aikinka shi ne kiyaye iyalanka daga shiga wuta, duk abin da ya biyo baya kari ne.

Da yawan iyaye su suke fara la’antar ’ya’yansu. Zaka ga uba yana kiran dansa shege, duk kuwa da cewa shi ne ubansa. Za ka ji uba yana kiran dansa barawo ko dan iska ko kuma ire-iren wadannan kalaman na batanci. Wani lokacin ma za ka ji uba yana tsine wa dansa.

Shawarata a nan ita ce, idan har da gaske muna so mu magance wannan matsalar, dole iyaye su gane nauyin da Allah Ya dora musu. Na biyu kuma bayan tattaunawa da na yi da yawancin wadanda za ka ga sun shiga wani hali, yawancinsu sukan nuna min cewa iyayensu ne suka tsane su, suke kyamarsu. Don haka sai suka lura cewa kamar iyayen ba sa kaunarsu. Ke nan yadda iyayen suke nisantar ’ya’yansa ba karamar matsala ba ce.

Yawancin iyaye ba su matsalar ’ya’yansu ba. Kawai dai sun san sun ba ’ya’yan abinci da wajen kwana, amma wata matsalar ta wuce matsalar wajen kwana da abinci. Yaro yana so a saurare shi ne a ji abin da ya zo da shi, daga idan akwai gyara sai a gyara masa. Amma yawancin iyaye babu wata alaka tsakaninsu da iyayensu sai daura fuska da zagi da fada. To a nan nake sanar da ku iyaye: Idan ba ka jawo danka kusa da kai ba, duniya za ta jawo shi, kuma za ta masa riga da wando.

Za ka ga yaro yana cewa bai son ubansa koda kuwa bai fada a fili ba. Za ka yaro ya fi son uban da ya samu a wajen, wanda watakila uban abokinsa ne ko kuma kawai ya tsince ne a gararinsa. Da nake tattaunawa da wani yaro da aka kama ya yi sata, kuma mahaifinsa na da abin hannu, sai ya ce min mahaifinsa ba ya ba shi kudi, kuma mahaifin nasa ne ya ce ya bar masa gida. Koda ya bar gidan, sai ya koma gidan abokinsa da zama, kuma a cewarsa, mahaifin abokinsa ya fi mahaifinsa sau dari, domin ko ba komai mahaifin abokin yana tambayarsa abin da yake cikin zuciyarsa.

Wannan ko shakka babu, domin da damuwar zuciya gara damuwar jiki. Da ka sanya mutum cikin damuwa gara ka masa duka. Da yawan iyaye suna jefa ’ya’yansu cikin damuwa, amma ba su sani ba. Kuma idan ’ya’yan suka shiga wani hali, su ne suke fara yayata ’ya’yan a idon duniya. Za ka wani ya ga yaro mara ji, sai ya ce wane ga danka can, sai ka ji ya ce, wannan dan iskan ko wannan barawon. Idan ka ce masa barawo, ai ba laifi don wani ya ce masa barawo. Idan har uba ya kira dansa barawo, to lallai duniya ma za ta kira shi.

Sannan kuma akwai maganar auratayya. Iyaye sukan saka ’ya’yansu cikin matsalar da ta shafi zaman auratayya da ke tsakaninsu da matansu. Wannan shi ma babban kuskure ne. Wata yarinya take ce min ko kadan ba ta mahaifinta saboda bay a kaunar mahaifiyarta ko kadan. Da kyar muka mata bayani har ta dan yarda cewa yana son mahaifiyarta, amma ta dage cewa ita kawai tsakninta da mahaifinta sai dai gaisuwa kawai. Allah Ya kiyaye. Sannan kuma akwai matsalar kwadayi. Iyaye suna so ’ya’yansu su zama manya masu kudi, amma kuma ba sa sauraron ’ya’yansu ko wane irin karatu suke so ko kuma wane irin aiki suke so. Hakan ya sa suke karatu ko aikin da ba sa so kawai don ya zama dole su yi.

Don haka nake kira ga iyaye da sanya ido a kan ’ya’yansu ta hanyar sauraron abin da ke damun ’ya’yan. Ba wai ka sanya yaro a makaranta bane ka ba shi abinci da wajen kwana ba shi ke nan, sai ka ce ka sauke nauyin da Allah Ya dora maka. Dolen dole a gare ka tabbatar ka tseratar da iyalanka daga shiga wuta. Ko ta halin yaya ne. Allah Ya bada iko.

A bangaren matasa kuma, a matsayina na matashi, na san cewa duk matsalar ba ta wuce son abin duniya da gasa da abokai da kuma babban matsalar, wato rashin hikima.

Abin da ya sa na ce rashin basira shi ne kasancewar yanzu har da wadanda suke je makaranta sai ka ga sun lalace. To akwai bambanci tsakanin ilimi da hikima ko basira. Idan Allah Ya baka ilimi ba basira, to akwai matsala. Hikima da ilimi suke yi wa matashi jagora, amma ilimi kawai ba hikima yakan jefa mutum ga halaka.

Matasan yanzu muna son mu yi kudi cikin sauri, duk da cewa a nan ma akwai iyayen. Wannan ke sa wa mu ta yin gasa da ’ya’yan manya. Sannan kuma ’yan siyasa suke amfani da mu wajen bangar siyasa da karyar cewa idan sun yi nasara, za a dama da mu. Amma da son samu nasara saisu yi watsi da mu.
Don haka nake kira ga matasan, da mu dawo cikin hayyacinmu. Idan muka magana da babatun cewa a bamu ragamar mulki mu ja, to lallai ya kamata mu zama masu hankali da sanin ya kamata. Ya kamata mu rika amfani da hikima da basirar da Allah Ya bamu wajen lura dayin abin da ya dace.

Ita dai duniya budurwar wawa ce.
Tura Zuwa:

Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’

Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’

Hanyoyi 10 da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’


Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa daku cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha.. Na samu sakonni mata da yawa da suka nemi na yi bayanin yadda za su rabi da kurajen ‘pimples’. Duk da na ta taba gabatar da irin wannan bayanin, amma sakamakon neman da mutane suka yi na ga dacewar maimaitawa. Ga bayanin hanyoyin da za ki bi wajen rabuwa da kurajen ‘pimples’:

1 ==> Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki wato macline a turanche a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.

2 ==> Ki kasance mai yawan shan ruwa. Yana da kyau duk inda za ki je ki sanya ruwa a jikin jakarki ba wai dole sai kayan kwalliya ba. Yawanta shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.

3 ==> Ki rika amfani da abin shafawar da ake kira ‘Antiodident spray’, irin su Jane Iradale da Neutrogenia Rapid Clear da Acne Eliminating Spot Gel da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan ya yi yawa yakan haifar da kurajen fuska.

4 ==> Ki kasance mai amfani da man ‘Cornmeal’ a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne, Intagilo Clear Sal Cleanser. Sannan ki rika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; Phytomer Gommage da Luffa-0.

5 ==> Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun ‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to ki yi amfani da kayan kwalliyar da ba sa toshe kofofin fatar fuska.

6 ==> Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi, kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.

7 ==> Yi amfani da man ‘Tea Tree’ domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu da kuma kalarsu. Za ki sami ire-iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.

8 ==> Ki kasance mai yin taka tsan-tsan wajen amfani da ire-iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki, sai su haifar miki da matsala.

9 ==> Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki: Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi, sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.


10 ==> Ki guje yin amfani da hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive