Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Amfanin Shan Rake Ga Lafiyar Jiki

Amfanin Shan Rake Ga Lafiyar Jiki 
A mafi yawancin lokuta muna shan rakene saboda zakinsa kadai ba tare da sanin amfani da kuma inganci da ke tattare dashi ba. A hakikanin gaskiya rake na da wasu sanadarai masu yawan gaske wadda ke taimakawa kwarai da gaske wajen inganta lafiyar jikin mu. Rake na kunshe da sanadarai kamar su carbohydrates, da amino acid, bitamin C, calcium da dai sauransu.

Ba shakka rake na kunshe da ruwa mai yawa, haka zalika rake yayi fice wajen zaki mai sanyaya rai da kuma sanya nishadi, hakan ne ya sanya Hausawa ke danganta maganar wadda ke shan rake a matsayin santi. Wasu daga cikin amfanonin rake sun hada da:

 

1.==> Yana kara ruwan Jiki da karfi musamman ga masu aikin karfi ko aiki cikin rana.

2.==> Yana taimakon Koda wajen fitar fitsari da kyau.

3.==> Yana karfafa garkuwan Jiki. Yana taimakawa wajen kamuwa da cutar sanyi mura da cutar daji.

4.==> Yana taimaka wa Hanta, Zuciya, Ciki, Ido, Kwakwalwa da Al’aura wajen yin aikinsu yadda ya kamata.

5.==> Yana gyara Fata ya kasance yadda ake bukata.

6.==> Gara ka sha Rake da ka sayi lemun kwalba don yafi su amfani ga lafiyar jiki

7.==> Yana wanke Hakora (amma yana da kyau a kuskure baki bayan ansha saboda kwayoyin cuta na iya samun zakin a matsayin abinci).

8.==> Yana maganin yunwa kuma baya da illa ga masu cutar ciwon sukari (masu fama da diabetes su kula kada su sha da yawa domin zai iya kasancewa guba a garesu).

9.==> Shan rake na inganta lafiyar hakora

10.==> Shan rake na samarwa jiki Karin ruwa domin yin aikinta yadda ake bukata

11.==> Yana rage amai ga mata masu dauke da juna biyu

12.== > Shan rake na maganin kumburi ga mata masu ciki

13.==> Yawan shan rake na kara inganta lafiyar kwakwalwa

14.==> Shan rake na kara inganta lafiyar idao da kara karfin gani

15.==> Rake na daidaita adadin sugan dake cikin jinni

16.==> Yawan shan rake na hana cushewar ciki

17.==> Shan rake na gayara fatan jiki

 

Wasu daga cikin amfanonin shan rake Kenan ga lafiyar jiki, yana da kyau mu kara adadin shan rake domin hakan zai taimaka wa lafiyar jikinmu sosai.

Tura Zuwa:

Yadda Za’a Magance Matsalar Sanko Cikin Sauki

Yadda Za’a Magance Matsalar Sanko Cikin Sauki

Sanko ya kasance wani cuta ne dake addaban wasu sa shi na mutane, wadda hakan na taba kyawun na miji ko mace. Bisa dalilin hakan mutane da dama basu sha’awar ganin sanko balle samunsa.

Tura Zuwa:

Illar Aikata Wasu Abubuwa Bayan Cin Abinci

Illar Aikata Wasu Abubuwa Bayan Cin Abinci

A hakikanin gaskiya akwai abubuwa bila adadin da muke aikatawa da zarar mun gama cin abinci wadda ke kawo matsala da illa ga lafiyar jikinmu. Wasu na sane da matsalolin dake tattare da hakan amma saboda ganganci suna cigaba da aikatawa, haka zalika wasu kuma suna yine bisa rashin sani.

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *