Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.

Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.
Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.

Assalamu Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga nan mujallar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zan tattauna ne game da abunda ake kira da “Google Adsense” ma’anarsa da kuma amfaninsa.

Me ake nufi da Google Adsense?

Google Adsense wani campanine wanda yake guda karkashin babban kuma sannanne kamfaninan wato Google, shi Google Adsense an kirkiresa ne saboda masu rubutun kansu a yanar gizo ko wanda suke amfani da shafukan yaran gizo a ayukan yau da kullum, shi Google Adsense yana amfani ne ta hanyar nuna tallan kaya ta bangare daban daban yakan iya fito wa a siffar rubutu, hoto ko kuma hoto mai mosti wanda aka fi sani da video.

Menene Amfanin Google Adsense

Shi wannan kamfanin kamar yanda na ambata a baya yana aiki ne ta hanyar nuna talla a sifar hoto, rubutu ko kuma hoto mai mosti (video) wannan shafin yana daya daga cikin manya kuma sanannun shafuka wanda suke taimaka wa mutane masu rubutun kansu a yanar gizo samun kudi na asali. Wasu zasuyi mamakin abunda na fada eh gaskiya ne mutum yakan samu kudi na asali a yanar gizo ta hanyoyi daban daban wanda zanyi bayanin su a yan kwanaki masu zuwa, sai dai duk hanyoyin ba su zuwa cikin sauki suna bukatar aiki tukuru kamar dai komai a rayuwa bazaka zauna jiran kudi yazo neman ka ba sai dai ka fita ka nemi aiki dan samun kudin kashewa haka zalika aiki a yanar gizo.

A gaskiya wannan ba sabuwar hanya bace an jima ana samun kudi a yanar gizo sai dai mune hausawa bamu san dashi ba amma wasu shafukan suna amfani dashi misali Duniyan Fasaha, bbc hausa, aminiyata, alumata da dai sauransu, a koda yaushe in muna bukatar abu da ya shafi nema a yanar gizo mukanyi yunkuri dubawa a Google Search wajen neman sa musamman idan ya shafi harkar boko, idan muka nemi abu misali “yanda za’a rage zubar gashin kai” in har da harshen turanci zamu duba wannan Kalmar a yanar gizo zamuyi la’akarin cewa shafuka sama da dari ne suka rubuta mafitar wannan matsalar amma shin ka/kin taba tambayar kaka/kanki maisa ba shafi daya kawai ya kamata a samu wannan amsar ba? Maisa shafuka da dama suka rubuta hanyoyin magance wannan matsalar? sannan kuma maisa kowa yayi nasa bisa fahimtarsa? Shin ka taba bawa kan ka/ki wannan tamabayar ko amsa a matsayin ka/kin a dan/yar boko? To a hakikanin gaskiya zan iya fadan cewa yawanci shafukan da ake rubuta su da harshen turanci ana yinsu sabonda kudi kuma Alhamdullilah suna samu shine gaskiyar maganan.

Yanda ake samun kudi ta hanyar amfani da Google Adsense   
   
Yana daya daga cikin manyan hanyoyi da ake bi wajen samun kudi a yanar gizo, za,a samu kudi ne ta hanyar sanyasa a shafin rubutun kai (blog/website), za ka/ki iya zaban nauo’I daban daban na girma wanda ya dace da shafinka sannan ka samar da wani code wanda zaka sa a shafinka dan nuna tallace tallace. Zaka samu yan wasu canji ne ta hanyar amfani da google adsense kawai in har mutum ya danna wannan tallace tallace da akeyi a shafinka. Google Adsense suna amfani da saka kaine (roboot) wanda sukan karanta abunda kake rubutawa a shafinka koda wani yarene, sannan zasu samar da talla wanda ya dace da abunda kake rubuta wa sai su saka ba lallai bane su sa abunda ranka ke so sai dai baza su nuna kayan tsiraici, batsa ko abu makamancin haka.

Yaya zanyi na samu kudina Cikin ajihu?   

Google de kamfanine da suka wuce tsanmaninka saboda suna da ma’aikata sama da 50 a kowace kasa a fadin duniyan nan dan haka samun kudinka ba abun damuwa bane kawai dai bisa dokar su dole sai kudinka ya kai dala 100 wato $100 wanda ya kama naira dubu talatin da shida N 3600 a yanda canji dala yake a yau ba lallai ya zauna a haka ba zai iya fin haka ko kuma ya zama kasa da haka saboda ya danga nane da canjin dala. Google Adsense suna tura kudi a bisa hanyoyi guda biyu a nan Nigeria na farko shine ta hanyar cheque wanda suke turawa ta hanyar sako, za,a ba mutum ya kawo maka har gida in dai kana cikin gari a kowace jiha a cikin fadin duniyannan kuma yana zuwa ne a siffarsa na dalla wanda zaka kaiwa zuwa banki sannan a canza maka zuwa kudin kasarka wanda zai iya daukan yan wasu kwanaki. Sai na biyu wanda shine banki, sukan iya turama kai tsaye zuwa account naka dake banki in dai ka/ki cika sharrudansu wanda zamuyi bayanin su a kwanaki masu zuwa.

Wace matsalece zan iya fuskanta wajen fara aiki da adsense?


Eh toh babban kalubalen da zan iya cewa zaka/ki fuskanta da fari shine wajen amincewa da shafinka a hakikanin gaskiya a yanzu Google Adsense basu karban shafukan da ake rubuta su da harshen hausa ba ma hausa kadai ba tare da wasu harshunan, suna karban harshuna guda sha daya ne kacall duk fadin duniyan nan wanda ya hada da turanci amma wannan ba mastala bane in dai ka iya rubuta abu mai ma’ana da harshen turanci zasu iya karbanka In har kuma ka samu karbuwa a wancan shafin naka na turanci zaka iya amfani dashi a kowani irin tsafine koda kuwa yana dauke da wani yarene wanda basu amince ba sai dai kawai karka sa abunda suka tsana misali kayan batsa, iskanci, yanda ake sace kayan wani ko wata, yanda ake hacking da dai sauran wasu kayan almundaha wanda basu dace ba.  
Tura Zuwa:

DON ME KAIMA BA ZAKA HADA SHAFIN RUBUTU NA KANKA BA?

DON ME KAIMA BA ZAKA HADA SHAFIN RUBUTU NA KANKA BA?

Dan Uwa mai ka/ki ke jirane da haryanzu ba ka/ki bude shafin ka/ki na rubutun kai a yanar gizo ba? Ko kasan cewa wannan abu ne mai matukar sauki wanda baya bukatar sai ka zama wani kwararre ta fannin kwamfuta kafin ka yi shi? Ina gayyatarka da kuma ke ‘yar uwa da ku shigo daga ciki. Idan ba’a manta ba munyi sharhi akan yadda matasanmu na yanzu ke yawan bata lokutansu a saman internet ba tare da sunyi wani abu wanda zai amfanesu ba kuma bazai amfani kowa ba. Sannan kuma mun kawo mu hanyoyin da za’a iya bi domin amfani da wannan lokutan da muke batawa a yin chatting ko kuma wani abu mai kama da hakan a saman Internet wanda baya tsinana mana komai sai asaran kudi. Insha Allahu yau zamuyi bayanine akan shafin rubutun kai a yanar gizo tare da amfaninsa.

Shi dai “Web Designing” wanda kalmane a turance wanda ke nufin hanya da ake bi wajen hada ko kuma gina shafin yanar gizo wato Website. Harkar gina Website ta samo asali ne tun daga lokacin da aka kir-kiri yanar gizo ita kanta -wato shekaru da dama da suka gabata. A wancan lokacin gina website abune ne musamman saboda sai masana da kuma kwararru ta fannin ilimin kwamfuta ne kadai ke iya yinsa, saboda komai ana yinshi ne da yaren da kwanfuta ke fahimta wanda aka fi sani da Programming a turance wanda kuma ba kowa ne ya iya ba ko a cikin masana kwamfutar. To yau gashi ci gaban zamani ya kawo mu, gina website ya zama wani abu mai matukar sauki, saboda a yau zaka sami wanda bai da ilimi akan kwamfuta zai iya hada website nashi na kanshi cikin yan wasu dakikai.

A wancan lokaci duk wani abu da kake so a matsayin suran shafin ka (website) to dole ne ka rubuta sa bisa fahimtar kwanfuta wanda aka fi sani da “Code” a turanche (programming). Amma a yanzu komai an riga anyi maka sai dai kawai ka dauka ka dora inda kake bukata ba tare da bukatar rubuta komai ba na programming. Wannan tsarin da zaka iya gina abu ba tare da kayi Coding ba shi ake kira da Drag-And-Drop a turance.

Akwai abubuwa da dama da muke bata lokutanmu akan saman Internet alhalin kuma zamu iya amfana daga garesu domin samun abin yi. Mafi yawanci wadannan abubuwan sun hada da:



1. Sharhi akan al’amuran Yau da kullum

Akwai mutane da dama wadanda sanannu ne ta bangaren bayyana ra’ayoyinsu akan harkokin yau da kullum da kuma fannuka daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. Hanya mafi sauki wadda wadannan mutane zasu iya sanar da al’umma matsayarsu akan wani lamari da ya kunno kai shine ta hanyar amfani da shafin yanar gizo, a inda cikin kankanen lokaci zasu janyo hankullan mutane da dama bayyana ra’ayinsu akan wannan lamari da ya taso, tare da fadakar da su akan abin da suke tunanin ya dace. Akwai da dama daga cikin matasannmu wadanda kwararru ne ta wannna fanni, to don ba zaka hada website dinka ba a mai-makon ko da yaushe kana a saman Facebook wanda babu ta inda kake karuwa da hakan.

2. Tallata Hajarka

Wani abu wanda ba kasafaye mutanenmu suka gane alfanunshi ba shine hada ma kamfaninsu ko kuma sana’arsu website da kuma tallata hajojinsu a shafinsu na yanar gizo. A mai-makon ka kashe makudan kudi wajen kai talla a kafafen yada labarai, wacce ba ma kowa ke sauraronta ba, hanya mafi sauki shine ka kir-kiri shafinka na yanar gizo inda zaka tallata hajarka ga dubban mutane ba tare da ka kashe sisin kobo ba. Dama daga cikin mutane masu sana’a suna daukar yin chatting a matsayin wani abu wanda zai debe musu kewa idan sunje kasuwa, musamman ma idan babu ciniki. Shin don mi ba zakayi amfani da wannnan dama ba wajen tallata ma mutane irin hajarka a saman Internet din?
Duk wasu manya-manyan kamfanunnuka da ka sani kamar su Konga , Dealdey , Dangote, da dai saurnasu, zaka ga cewa duknansu suna da website inda suke tallar kayansu a lokaci guda kuma suna mu’amala da kwastomominsu. Shiga Kasuwa

3. Ilimantarwa

Akwai mutane da dama da suka sadaukar da lokutansu domin ilimantar da sauran mutane a addinance ko kuma a zamanance. A mai-makon ka dogara da kafar Facebook kadai, kaima zaka iya yin website dinka don fadakar da mutane. Akwai malamai da kuma masana fannoni daban-daban da kan bude shafinsu a yanar gizo domin ilimantar da mutane akan fannoni da dama. Akwai malaman addini kamar Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, da makamantansa, da ke da website inda ko dai su rika amsa tambayoyin al’umma ko kuma su rika sanya wasu tafsirai da suka gabatar. Akwai kuma masana da dama da kanbude shafin su a Internet don su sanar da mutane wani ilimi na musamman kamar yadda ake hada wasu abubuwa da dai sauransu.

4. Nishadantarwa

Akwai mutanen da su kuma abinda suke da sha’awa akanshi shine abubuwan nishadantarwa kamar wasana kwaikwayo, fina-finai, da dai sauransu. Wasu mutumen kuma zaka ga su dama can Allah ya halitta su mutune ne masu ban dariya da kuma sanya mutane raha. A lokuta da dama wadansu daga cikin wadannan mutanen sukan hada website dinsu domin nuna ire-iren wasannin barkwancinsu wanda zai baiwa mutane dariya, a yayin da a gefe guda kuma suke samun makudan kudade ta hanyar mutanen da ke ziyarar wannan shafin nasu. Misalin wadannan mutane sune Mark Angel da kuma Basket Mouth.

5. Labaran Wasanni

Zaka ga da dama matasanmu suna maida hankali sosai a bangaren harkokin da suka shafi wasanni. Wasu daga cikin wadannan matasa masu hikima sukan yi amfani da wannan dama su kir-kiri website domin mabiya wani club kamar Arsenal, Manchester, Real Madrid, Barcelona, Bayern Munich da dai sauransu. Ta hanyar mutanen da zasu rika tururuwa zawa wannan shafi, shi wannan matashi mai hikima zai iya samun makudan kudi na gaske. Muna yin abubuwa da dama wadanda ya kamata ace muna amfani da kafar internet domin gabatar dasu. Dalilan da zasu iya sanya ka ko kuma su sanya ki gina website basa da iyaka. Duk wani abu da kake tunanin zai iya janyo hankullan jama’a to abu mafi sauki da zaka iya janyo mutanen nan shine ta hanyar amfani da Website. A inda kai kuma zaka samu alheri mai yawan gaske ta hanyar tara wadannan mutane.

A post namu ta gaba, in Allah yaso, zamu kawo muku alfanun ko kuma amfanin hada website naku na kanku da kuma yanda zaku amfana daga gareshi. Ku kasance tare damu. Ga duk mai wata tambaya sai yayi comment da tambayarsa a nan kasa. Ga dukkan mai bukatar samun darasinmu kuma ta hanyar Whatsapp shima sai yayi comment da Lambar sa.

Tura Zuwa:

Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook

Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook 
Wannan lamari na barin account da mutumin da ya rasu a social network yana baiwa mutane da dama haushi da takaici, musamman waɗanda suke kusa da wanda ya mutu. A wani lokaci za ka ga mutane suna jingina (tagging) hotunan banza ko na batsa ga shi wannan mamaci, haka za ka samu duk shekara mutane su yi ta mai murnar cika shekara (birthday) amma alhali shi yana lahira, wasu waɗanda suka saba wasa da shi, idan suka yi magana da shi bai amsa ba su yi fushi ko zagi da dai makamantan su.
Muna yawan samun ƙorafe-ƙorafe a wurin jama’a musamman waɗanda suka damu da makomar ‘yan uwansu waɗanda suke da account a Facebook ko Twitter ga shi kuma Allah Ya yi musu mutuwa dangane da ya za ayi su iya goge wannan account domin yadda hankalinsu yake tashi duk lokacin da suka ga hotonshi ko kuma wani abu makamanci haka.
Wannan dalilin ne ya sa muka yi bincike muka gano ashe tun tsawon wancan lokacin da muke ganin haka tuni kamfanin Facebook suka fito da wani fom wanda shi ne kawai abin da kake buƙata domin goge irin wannan account ɗin.

A GYARA HALI KAFIN A MUTU.

Yana da kyau duk wanda yake karanta wannan takarda ya sani wata rana shi ne wanda mutuwa zata riske shi, kuma bai san wani lokaci ba ne, kuma bai san a wani hali ba ne. Yana da kyau mu riƙa tsaftace abubuwan da muke sakawa social networks domin duk abin da ka saka yana nan kuma wani ya killace shi. Kuma dani da ku duk mun san watan wata rana za a tambaye mu, kuma sai mun bayar da bahasi a kai.
Mutane da dama basa la’akari da cewar duk abin da na rubuta ko na saka a social network Allah zai tambaye ni, idan na saka wata magana ta karya wani ya yaɗa to zunubin yana kaina, haka idan na yaɗa abin da yake na alkairi ladan yana kaina. Mu guji yiwa mutane ƙazafi, saka hotunan da basu dace ba, da kuma yaɗa jita-jita da zarge-zarge domin waɗannan abubuwan suna da wahalar tuba kuma suna da wahalar kankarewa.

INA ZAN SAMI FOM DA ZAN CIKE

Shi wannan fom da za ka cike, yana da waɗansu ƙa’idodi da ya kamata mutum ya sani, kuma akwai abu mai muhimmanci da koya ya kamata ya kiyaye.
Kamfanin Facebook basa la’akari da garinka ko kuma addinin ka, suna la’akari da addininsu da kuma al’adunsu, saboda haka abin da suke buƙata wurin cike fom ɗin shi ne takardar shaidar cewar wannan mutumin ya mutu wacce kotu ko Asibiti suke bayarwa. Saboda haka kafin ka fara cike wannan fom sai ka je ka karɓi takardar shaidar cewar wane ya mutu, sannan kayi scanning sai ka fara cike fom ɗin.
Za a iya buɗe wannan fom ɗin ta bin wannan link kamar haka https://www.Facebook.com/help/contact/228813257197480
Fom ɗin wanda da Turanci aka rubuta shi yana buƙatar ka amsa tambayoyi guda takwas (8) kafin ka aika shi wanda su kamfanin Facebook za su duba su gani sannan daga baya su goge shi wannan account ɗin.

TAMBAYOYI DA AKA AMSA

1.    Cikakken Suna: A wannan ɓangare ana son kai da za ka cike wannan fom ɗin ka saka sunanka cikakke misalin Muhammad Hassan

2.    Sunan wanda ya mutu: shi kuma rami na biyu sai ka rubuta cikakken sunan wanda kake son a goge account ɗinshi, namiji ne ko mace.

3.    Email ɗin mamaci: a na son ka saka imel ɗin da kake tunanin cewar da shi wannan mamacin ya buɗe account, kodayake wannan email ba dole ne ka san shi ba, kuma idan ma baka cike wannan ramin ba saboda rashin sani babu matsala, amma saka email ɗin zai baiwa kamfanin sauƙi zaƙulo account ɗin kuma su goge shi.

4.    Link ɗin mamaci na Facebook: duk mutumin da ya buɗe Facebook, suna bashi wani link (hanya ko rariyar liƙau) da ita ce hanyar shiga shafin ka kai tsaye, kuma wannan hanya babu mai ita a Facebook sai kai. Misali nawa shine https://Facebook.com/muhammadabbaganakolo duk mutumin da ya rubuta wannan link a jikin browser to zai kaishi shafi na na Facebook kai tsaye. To idan baka san na wanda ya mutu ba, abin da za ka yi shi ne ka nemo shi a cikin abokanenka, sai ka taɓa sunan shi, zai kai ka kai tsaye cikin shafin sa, sai kayi amfani da browser ka kwafe link ɗin da ka gani sai ka saka a wannan ramin.

5.    Dangantar ka da mamaci: lallai Facebook suna buƙatar su san dangantakar da wannan mamaci kafin su cire wannan shafi a gidansu. Saboda haka za ka zaɓi dangantakar ka, a cikin kashi uku da suke da shi.
1.    Iyalai mafi kusa: kai ɗan uwansa ne, ko baban sa, ko matar sa ko kuma yayan sa da dai makamanta su.

2.    Dangantakar jini: kamar kaka, goggo, baffa, da kawu da dai makusanta na jini

3.    Abokantaka: idan wanda ya rasu, abokinsa ne ko kuna aiki wuri guda ne ko kuma aji ɗaya kuka yi, ko kuma ma dai ka san cewar ya mutu ne, sai ka zaɓi nan.

6.    Me kake son Facebook su yi da account ɗin: a nan Facebook suna son ka faɗa musu abin da kake son ayi maka da account ɗin domin ba goge shi kaɗai za su iya yi ba, a nan akwai abu guda hudu (4) da za ka iya basu dama su yi.

1.    A faɗawa abokansa ya mutu: wannan zabi ne da za ka ba Facebook na su saka a cikin shafin sa cewar wane fa yanzu ba shi, ya mutu, kuma su saka alamar da kowa zai iya ganewa cewar yanzu da gaske babu shi.

2.    A goge account ɗin sa: wannan shi ne ɓangaren da ya fi kyau ayi amfani da shi, domin zai ba Facebook dama su share dukkan abin da wannan mamacin ya saka a cikin Facebook, tun daga rubutunsa, likes da comments da sharing da hotuna da video da yasa a Facebook, yadda ba shi suna ba su.

3.    Ina da buƙata ta musamman: idan kuwa akwai wani abu da kake buƙatar Facebook su yi maka ba sharewa ba to sai ka zaɓi wannan ɓangare.

4.    Ina da tambaya: wannan kuma idan kana da tambaya da kake son kayi wa Facebook sai ka zaɓi wannan ɓangare.

7.    Yaushe mamacin ya rasu?: a wannan ɓangare suna son ka zaɓi rana da wata da shekarar da ya mutu ka saka musu.

8.    Takardar shaidai mutuwarsa: a wannan wurin shi ne za ka sakawa Facebooktakardar shaida daga kotu ko asibitin da mutum ya mutu cewar wannan mutumin ya mutu, ko shaida da mutane gidansu cewar su suka baka izini cewar Facebook su cire shafinsa.

9.    Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu da wannan fom domin su duba su gani sannan su yi abin da ka ce kana so.

Ba kamar yadda mutane suka tsammani ba, zai ɗan ɗauki lokaci kafin kamfanin Facebook su waiwayi takardar, domin kamfanin da yake da mutane sama da biliyan daya da rabi yana buƙatar lokaci kafin ya aiwatar da wani abu. Kai dai tunda ka aiki sai ka jira.
Kuma babu laifi idan mutane mabanbanta suka aika, misali a sami mutane da yawa su aika domin hakan zai sa Facebook su gane cewar wannan bawan Allah da gaske ne cewar ya mutu.
Muna rokon Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu mutuwa da imani, Ya kyautata ƙarshenmu ya yafe mana kurakuranmu, ya amintar da mu baki ɗaya. Amin

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Ko Kun San Ba Yawan Shan Zaki Ne Ke Kawo Cutar Siga Ba (Diabetes)

Ko Kun San Ba Yawan Shan Zaki Ne Ke Kawo Cutar Siga Ba (Diabetes) 

A duk ranar 14 ga watan Nuwamba ne aka kebe a matsayin ranar masu ciwon Siga “Diabetes na duniya. Kwararrun likitoci a fanin ilimin ciwon Siga sun bayyana cewa ba yawan shan zaki ke jawo cutar Siga ba. Wani malami a jami’ar Legas dake koyarwa a sashen koyar da aikin likita, Ifedayo Odeniyi, yace cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.” Ya kuma kara da cewa rashin aikin sa ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga. Bayan haka kuma ya yi kira ga mutane da su yi watsi da camfin da ake yi wai shan zaki ne ke kawo cutar siga.

Ya ce hakan ba gaskiya bane.

” Likita ya ce saboda irin wannan camfe-camfe ne ya sa mutane ke hana kansu cin abinda ya kamata don samun kuzarin da suke bukata a jikin su.” Ya ce tabas yana da mahimmanci idan mai dauke da cutar siga na kiyaye sharuddan da ya shafi irin abincin da ya kamata ya ci, amma haka ba yana nufin kada mutum ya hana kan sa cin abincin da ke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ saboda samun kuzari a jikin su.

Likita Odeniyi ya ce cutar siga yakasu kashi kashi; Akwai wanda shi Insulin baya aiki kwata kwata a jikin mutum wanda ake kira da ‘Type 1 diabetes’ sannan akwai wanda shi insulin din yana aiki amma ba yadda ya kamata ba wanda ake kira ‘Type 2 diabetes’ shine mafi yawan ‘yan Nijeriya ke fama da shi.


Ya ce alamomin cutar su hada da yawan jin yunwa, yawan yin fitsari da sauransu. Bayan haka Oladimeji Agbolade ma’aikacin kamfanin sarrafa magunguna dake kasar Faransa ‘Sanofi ’ya ce kula da masu dauke da cutar siga na da matukar wuya ganin yadda magungunan cutar ke da tsadar gaske.
Tura Zuwa:

Halaye 10 Da Ke Tsufar Da Mutum Da Wuri

Halaye 10 Da Ke Tsufar Da Mutum Da Wuri

Duk da cewa tsufa wani abu ne da babu wanda zai iya gujewa, za a fuskanci cewa wasu na tsufa da wuri fiye da wasu. Akwai wasu halaye da mutane ke yi da ke haifar da hakan, kuma kowannen su binciken kimiyya ya tabbatar da haka. Ga guda 10 a cikin su:

==> Shan taba sigari
==> Riko ko kuma Rike mutane a zuciya da kin yafiya
==> Shan giya
==> Yawan shiga rana
==> Rashin isasshen barci
==> Cin kayan zaki
==> Yawan gajiya
==> Rashin kula da fata yadda ya kamata
==> Yawan zama guri daya
==> Cin abinci wadanda ba sa gina jiki

Da fatan za a kiyaye domin a ci moriyar yarinta yadda ya kamata.


Tura Zuwa:

Miyar karkashi da kubewa

Miyar karkashi da kubewa

Assalamu alaikum Uwargida. Yaya iyali? Tare da fatan a na lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa danya. Wannan miyar dai bata cika son yawan kayan hadi ba sannan kowace mace da yadda take tata miyar karkashin. Wata karkashin zallah kawai take girkawa. Amma idan har ana son aci miyar tayi dadi sosai kyawunta a hadata da kubewa danya domin jin ainihin gardin miyar da kuma dadinta. Don haka na kawo muku yadda ake miyar karkashi hade da kubewa danya domin sanya kunnen maigida motsi. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da ake bukata
          ==> Ganyen karkashi
          ==> Kubewa danya
          ==>Tokar miya ko kanwa
          ==> Attarugu
          ==> Bandar kifi
          ==> Nama
          ==>Albasa
          ==> Danyar tafarnuwa
          ==> Garin citta
          ==> Magi

Hadi

A kankabe ganyen karkashin tsaf sannan a yayyanka shi kanana sosai. A samu kubewa danya a yayyankata sannan a saka a turmi a daka ta tayi laushi sosai. In kuma da kanwa za’ayi miyar sai a daka tare da kanwa kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. A daka attarugu da tafarnuwa sannan a kwashe. A wanke bandan kifi da ruwan dumi a cire kayoyin sannan a yayyanka albasa kanana.


A daura ruwa a tukunya sannan a tafasa nama har sai yayi laushi. Sai a kara ruwa kadan akan romon naman sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagaggen attarugu da garin citta da bandan kifi har sai sun tafasa sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har sai ta fara nuna sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a buga sannan a cigaba da juyawa. Idan har ba’a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin yakamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke a zuba sai a cigaba da gaurayawa har sai dandanon ya fito sannan a sauke. Za’a iya cin wannan miyar da tuwon semo.
Tura Zuwa:

Kwalliya A Lokacin Zafi

Kwalliya A Lokacin Zafi

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa. Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:

==> Hoda: Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.

==> Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.

==> Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.

==> A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.


==> Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.
Tura Zuwa:

KARIN NI’IMA GA MA'AURATA

KARIN NI’IMA GA MA'AURATA

GARIN RIDIZa a kasa kankana kashu uku, za’a dauki kasha daya daga cikin ukkun, sai a hada su guda a zuba a cikin blander a markade, sai a zuba garin ridi a ciki, a zuba madara da zuma ki zuba wa angonki cikin kofi kisha ya sha. Wannan hadin yana kara ni’ima da maniyi, yana hana karnin dake fitowa,   HADIN RIDIAnso miji da mata su ringa amfani da wannan hadin domin Karin ni’ima yana kuma sa koda yaushe ta dinka bukatar mijinta kusa da ita.1-    Ruwan kwakwa
2-    Madara peak
3-    Zuma
4-    Ridi
zaki hade su wuri guda ki ringa sha yana kara ni’ima sosai da sosai.

WANI HADIN RIDI(Karin ni’ima da kuzari) anso miji da mata su ringa sha domin motsa sha’awa1-    Kanunfari
2-    Zuma
3-    Garin ridi
4-    Nonon shanu mara tsami
Ki dafa kanunfari da ruwan zafi idan ya dauko nuna (dahuwa) sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu mara tsami, ki hade guri daya ki gauraye. Ki saka a firiji ko ki saka kankara idan yayi sanyi sai ki sha. Wannan hadin idan kinyi sai kuma bayan mako daya za,a kuma yi. HADIN KAYAN ITATUWA(Karin ruwan gaba) wannan hadin yana kara ruwa kuma mace da mijinta duk zasu iya sha.1-    Kankana
2-    Kokumba
3-    Tumatur
4-    Mazarkwaila
5-    Madaran peak
6-    Dabino
A yanka kankana duka harda yayanta, itama kukumba dukkanta za a yanka harda bayan, kada a cire yayan, a yanka tumatur shima kada a matse ruwan cikin sa sai kid aka kanunfari ki jika dabino ki cire kwalayen ki hade su guri guda, ki markada a blander sai ki juye ki saka mazarkwaila ta narke ki zuba zuma sai ki juye madara peak gwangani daya, ki ringa sha safe da yamma zaki sha mamaki.

HADIN KANUNFARIKarin ni’ima da motso sha’awaKijika kanunfari shi kadai ki rinka sha ki kuma kama ruwa da shi (tsarki) shima wani nau’in Karin ni’ima ne. (kanufari)

HADIN ZUMAKarin ni’ima damotso sha’awa zaki sami zuma mai kyau ki zuba garin habbatus-sauda da man zaitun ki juye su guri guda sai ki dinga sha babban cokali biyu da safe da kuma yamma.

1-    Zuma
2-    Garin habbatus-sauda
3-    Man zaitun

HADIN DANYAN KWAIYana karawa mace kuzari ba tareda ta gajiya ba wajen jima’I kuma yana karawa mace ni’ima da sha’awa.1-    Lipton
2-    Danyan kwai
3-    Zuma
Ajika lipton da ruwa kadan har sai yayi baki, sai ki fasa kwai ki hada shi, sai ki zuba cikin ruwan lipton kina iya zuba madara peak sai ki zuba zuma ki dinga sha.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *