Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

SABUWAR HANYAR DA ZAKA HANA MTN SACEMA KUDI

SABUWAR HANYAR DA ZAKA HANA MTN SACEMA KUDI

[MTN] SABUWAR HANYAR DA ZAKA HANA MTN SACEMA KUDI

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu insha Allah yau zan nuna muku hanyan da zaka bi wajen hana kanfanin MTN sace ma kudi a layinka, shin ana dauke maka kudi batare da wani daliliba? ina wadanda kudinsu baya kwana acikin layin Da zarar ka bar dan kobon ka kafin wayewar gari sai ka tarar da 0.0, ina wadanda kullum mtn saisun cire 5 ko 10 a layukansu ba tare da wani kwakwaran dalili ba.

To Alhamdulillah idan kana fama da daya daga cikin matsalar satan kudin MTN to insha Allah daga yau ka rabu da wannan mummunar aqidansu, kawai ga yadda zakayi matakai ne masu sauki, da farko kawai ka danna:- *123*5*1# zasu nuno maka wasu surutai kawai kayi Replay da 2 zasu sake rubuto maka wasu abubuwa  kar ka damu da karantawa kawai kayi reply da 8 nan take zakaga jerin sunayen abubuwan da kake ciki wanda sune silar daukar maka kudi, abunda zaka yi gaba shine kawai kayi Replay da number plan din da ka gani, zakaga Unsubscribe kawai saika danna, shikkenan kayi maganin wannan matsalar sannan zasu aiko maka da sakon message a kan wayarku na cewar ka fita daga cikin wannan tsarin, Allah ya bada sa,a.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive