Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci jama’a su daina cewa wai PDP ba za ta sake mulkin Najeriya ba.
Idan ba a manta ba da, tsohon shugaban kasar dai ya yi murabus daga Jam’iyyar APC mai mulki, inda daga bisani ya sanar da cewa ya koma jam’iyyar PDP, inda ya baro a wani faifan bidiyo da ya saka a shafukan sada zumunta.
A cewar Atiku Abubakar, “Babu wanda ya san gobe sai Allah, balantana ya san abin da zai faru. Mutum bai da wannan ikon,” inji Atiku Abubakar.
No comments:
Post a Comment