Ina saye da sayar da man kadanya ne, duba da yanayin sanyi da aka fara, a yunkurin zama mai dogaro da kai Inji matashiya Maryam Muktar Abdullahi.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVoa a yau inda ta ke cewa mafi akasari tana gudanar da hajar ta ne ta shafukan sadarwa na yanar gizo, ta nan ne take tallata kayan nata.
Ta kara da cewa shafukan na taka muhimmiyar rawa wajen sama mata kwastamomi da inganta sana’ar ta ta, ta kuma kara da cewa baya ga wannan sana’ar, ta koyi sanar kwalliya ga mata inda ta koyi yadda ake kwalliyar ta hanyar daukar darussa da ake gudanarwa a shafukan Instagram da facebook.
Maryam, matashiya mai yi wa kasa hidima, ta ce shafukan sadarwa kadai ya ishe matasa tallata hajarsu tare da samun kasuwa da zama mai dogaro da akai a zamanance da dauke wa iyaye wasu matsalolin nasu na kansu.
Daga karshe kuma ta ja hankalin matasa da su jajirce wajen neman nasu na kansu tare da maida hankali wajen kafa sana’a domin dogaro da kai, maimakon mayar da hankali ga ayyukan gwamnati tare da amfani da damar wayoyin zamani wajen tallata sana’oinsu maimakon hirarraken da basu da amfani.
No comments:
Post a Comment