fiddausi Yako, matashiya mai kimanin shekaru 12, yar asalin karamar hukumar Kiru, ta ce tana zuwa tun daga garin yako domin sayar da gyada a rashin samun damar cigaba da karatun sakandire.
Ta ce ta kammala firamare a Gazam, dake Yako, inda ta kammala aji shida tun daga nan da ta ga lokaci na neman kure mata sai ta fara talla, duk kuwa da cewar ta samu nasara a jarabawarta.
Ta ce tana matukar burin cigaba da karatu koda na sakandire ne domin samun cigaba a rayuwa, kuma ta kara da cewa tana da ra’ayin zama malamar makaranta, domin ko ba komai zata kara wasa kwakwalwarta ta hanyar koyarwa da kuma cudanya da dalibai.
Ko da yake ta ce iyayenta ne ke dora mata tallar gyada, tana yi domin ta sama musu kudi don kashe bukatun yau da kullum.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
No comments:
Post a Comment