Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda ake harkallar saye da sayar da mutane a Libya

Yadda ake harkallar saye da sayar da mutane a Libya

Hukomomi a kasar Libya sun ce suna gudanar da bincike kan yadda ake harkallar saya da sayar da ‘yan kasashen Afirka da suke gudun hijra ko kuma fataken da ke bi ta kasar da zimmar shiga kasashen turai a kasar.
Kamar yadda rahotanni ke nunawa, masu harkallar suna farautar dubban mutane ne wadanda suka shigo kasar da niyyar shiga yankin Turai, a wata irin tafiya mai cike da hadari da ban tsoro.

kasar Libya ita ce ta fi sauki ga mutane masu tafiya yankin Turai ta ruwa, domin ana samun sama da mutum 150,000 da suke shiga Turai ta wannan hanyar duk shekara a shekaru uku da suka gabata kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
“Mutanen sun zo ne daga kasashen Afirka daban daban, kuma suna cewa ne sun gudo ne saboda yaki, tsananin talauci, da rashin aikin yi da ya yi wa kasashensu katutu. Sun yi tafiya mai wahala ta cikin sahara, kuma sun biya wasu ‘yan fasa kauri wasu kudade kafin su shigo kasar Libya domin su yanke su shiga yankin Turai. Kuma saboda yanayin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a kasar Libya. Harkallar saya da sayar da mutane da harkallar miyagun kwayoyi ya yi mana kamari a nan,” inji Mahmoud Abdelwaheed, wanda ya ruwaito hakan daga inda ake a tsare mutane a babban birnin Tripoli.
Wani sabon salon harkallar saya da sayar da mutane a kasashen duniya da kasar Libya bai zama daban ba. Amma abin ban mamaki shi ne yadda ake harkallar a bainar jama’a, inda mutane ke zuwa su duba wanda suke so, su yi cinki, sannan su biya kudi su mallaki dan Adam.
Babu wani ingantaccen ragista domin shigowa kasar Libya.
Kamar yadda rahoto ke nunawa, wajen da ake tsare mutane da aka kama ba sa samun lura yadda ya kamata a kasar Libya, kuma ana samun labarin cewa ana cin mutunci mutanen da ke wajen, ana musu fyade, kuma ana sa su aikin wahala na dole.
Idan inda ake ajiye mutanen suka ciki, ana zargin cewa daga nan ne ake rika sayar da mutane kamar abin sayarwa a bainar jama’a a cikin kasuwanni. Wadanda suka tsira sun shaida wa Hukumar Kula da masu hijira ta Majalisar dinkin Duniya cewa suna amfani ne da wayoyin salula na zamani su nemo wadanda za su shigar da su kasar Libya, daga nan kawai sai a sayar da su, a rike su, sannan a tursasa su su rika yin aikin wahala da karfi da yaji, da kuma karuwanci.


Hukumar Kula Da ‘Masu Hijra ta Duniya ta ce harkallar saya da sayar da mutane ya zama wani abu da aka saba da shi, ta yadda har ya kai ga ana sayar da mutane a bainar jama’a da arha, wani lokacin har akan sayar da mutane a kudin da bai taka kara ya karya ba kamar ace dala 400 (Kimanin Naira dubu 144,000 ke nan).
“Duk da cewa abin akwai daure kai a ciki, amma gaskiya ana yi,” inji Leornard Doyle na Hukumar Kula Da Masu Hijra ta Duniya kamar yadda ya sanar da Counting the cost.
Ya kara da cewa “Dalilin shi ne, harkallar saya da sayar da mutanen yana faruwa kuma babu wata doka ta musamman a kasar Libya. Libya babbar kasa ce kamar Faransa, mai fadin kasa. Mutane da yawa suna shigowa kasar. Suna tunanin cewa za su samu sabon rayuwa idan suka shiga yanar gizo musamman a Facebook suka yadda ake rayuwa a yankin Turai, sai suga cewa su ma ya kamata su je a dama da su.”
Hakanan kuma ya kara da cewa a lokacin da mutanen suka sauka a kasar Libya, “Da sun sauka a motar da ta kawo su, sai a saka su a wani irin waje. Sai a kwace duk abin da suka zo da shi. Sai a tursasu, a ci musu mutunci, sai a sayar da su. Amma babban abin mamakin shi ne yadda ake sayar da su a bainar jama’a, inda ake tallar su a kan: Masu aikin wahala Dala 400, sannan kuma watakila mata su fi haka tsada, domin za a iya sa su a harkar karuwanci. Wannan shi ne ka faruwa a kasar.”

Doyle ya nanata cewa irin wannan lamarin ya nuna cewa ya kamata duniya ta sa ido a kana bun da ke faruwa a kasar Libya bayan mulkin Gaddafi
“Ya kamata duniya ta sa ido. Amma abin maraba ne yadda duniya ke magana a kan wannan matsalar,” inji Doyle.
“Wannan sabon salon harkallar saya da sayar da mutanen a zagaye duniya, ba wai Libya ba kadai. Yana faruwa a manyan kasashen duniya, da kuma kasashen da ke tasuwa. Amma abin takaici shi ne yadda ake harkallar a bainar jama’a.”mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive