Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za ki magance amosanin-ka

Yadda za ki magance amosanin-ka

Yadda za ki magance amosanin-ka
Mata da yawa suna fama da amosanin-ka, wanda hakan ta sanya suke shan fama wajen magance shi, a lokaci guda wadansu matan sun kashe makudan kudade wajen neman maganin amosanin-ka, amma duk da haka kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Sakamakon haka ne a wannan makon muku taho miki da hanyoyin uku da za ki bi wajen magance amosanin- ka:

1.      Amfani da ganyen bishiyar Yazawa ko kashu (Cashew):
Daga farko ki samu ganyen bishiyar yazawa mai kyau da kuma tsafta, sannan sai ki wanke da ruwa mai dumi. Bayan nan sai ki daka ganyen ta hanyar hada shi da ruwa kadan. Kada ki bari ya yi ruwa. Daga nan sai ki shafa a kofofin gashin kanki. Za ki bar shi a kanki har zuwa rabin awa. Bayan nan sai ki wanke. Za ki ci gaba da haka lokaci zuwa lokaci, har sai amosanin ya mutu ko ya warke. Za ki iya shafa wannan dakakken ganyen bishiyar yazawa kamar sau shida a tsakanin mako biyu. Za ki iya yi hadawa da yawa, wanda zai yi mako daya, sai dai kada ki bar shi a wajen da akwai zafi.



2.      Lemon tsami da ruwan kwakwa:
Ki samu lemon tsami guda biyu ko kuma yadda kike so, sai ki samu kwakwa, daga nan sai ki fasa kwakwar ki tsiyaye ruwanta a cikin kwano ko roba. Bayan nan sai ki gauraya ruwan kwakwar da na lemon tsami. Za ki iya gauraya ruwan kwakwar da kuma jus din lemon tsami (Lemon Juice). Idan kin gama hadawa sai ki shafa a kofofin gashin kanki har zuwa awa daya ko rabin awa, daga nan sai ki wanke da ruwa mai tsafta. Za ki ci gaba da yi har tsawon mako biyu. Idan kin yi hakan da yardar Allah kin rabu da amosani.

3.      ‘Ya’yan kwallon mangwaro:
Ki samu kwallon mangwaro, sai ki fasa shi, daga nan sai ki cire kwallon ciki. Idan kin yi hakan sai ki daka, sannan ki sanya a cikin roba, ki kuma rufe bakinta da leda ko murfi yadda iska ba za ta rika shiga ba. A duk lokacin da za ki yi amfani da shi, sai ki diba, sannan ki gauraya da madarar Butter Milk ko kuma ruwa kadan. Bayan nan sai ki shafa a kofofin gashi har tsawon wani lokaci, sannan ki wanke da ruwa mai dumi.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive