Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Sa Hoto A Post A Shafin Blogger

Yadda Ake Sa Hoto A Post A Shafin Blogger

Muhammad Abba Gana

Shafin blogger yana daya daga cikin sanannun kuma manyan shafuka a yanar gizo wadda suke taimakawa wajen rubutun ra’ayin kai, shafin blogger yana bayar da damar isar da sakonni ta hanyar rubutu, hoto ko kuma hoto mai motsi wadda aka fi sani da video a turance. A makonni da suka gabata munyi jawabi a bangarori daban daban daya kama da:

Tura Zuwa:

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA


Muhammad Abba Gana

Kowani ciwo yana da magani hakan take; mata da dama sukan koka wajen yadda maran su ke ciwo lokacin al’ada, hakan yana faruwane bisa wasu dalilai. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku wata hanya da zaku bi wadda da izinin Allah za’a dace.

Karanta: Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala


1. ==> A samu Tsohuwar Tsamiya a jika aruwa tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan tun kwana biyu kafin zuwa haila, har lokacin da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da dama sun jarraba kuma sun dace.

2. ==> MAN ZAITUN: A sami man zaitun sai a Karanta ayoyin Alqur'ani acikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta.

Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al'aurarta saboda ayoyin da aka tofa). Shima wannan idan anyi shi za'a dace. Koda Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke sanya mata ciwon jikin to zata samu waraka.

3. ==> KUSTUL HINDI: Idan an jikashi a ruwa ana shansa safe da yamma shima yakan Magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al'ada. Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Da fatan Allah shi amshi dukkan abinda muke roka ma junanmu. Allah yasa mu dace. Ameen!

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Muhammad Abba Gana

Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu yau zamuyi jawabine akan yadda ake duba sakamakon jarabawar Jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019).

Mutane da dama sun kosa matuka wajen son suga sakamakon jarabawar jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019), musamman ma iyaye da kuma dalibai. Wasu daliban suna cikin tsaka mai wuya saboda labarai da ke fitowa yan wasu makonni da suka shude cewar dalibai da dama baza suga sakamakon jarabawansu ba sabili da sun jefa kansu cikin haramcecciyar hanya wato sata. Haka zalika wasu daga ciki za’a rage addadin abinda suka samu a cikin jarabawar.


Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa wato (JAMB), ta bayyana cewa jarabawar JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) ta fito a Asabar data gabata. Sannan kuma hukumar ta ce babu ruwan dalibi da zuwa cibiyoyin rubuta jarabawa domin ganin sakamako.    

“Daga yau har zuwa ranar Litinin, wannan ce kadai hanyar da za’a iya ganin sakamakon jarabawa.” Ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin hana ‘yan damfara su damfari mutane batun ganin sakamakon jarabawa. Sannan kuma an fito da wannan dabara ce domin duk wanda bai ga sakamakon sa ba, to ya na daga cikin wayanda aka rike sakamakon su.

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito


Sannan ya ce hakan ya na nufin an daina zuwa ana yin cunkoso a wurin duba jarabawa, inda wadanda ba su ga ta su ba ke yin dafifi a wuraren duba jarabawa ana haddasa cinkoso.

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB 2019


Wannan wata hanyace mafi sauki ga wadanda suka rubuta jarabawar shiga makarantun jami’a ta JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) da zasu iya duba sakamakonsu.

Babu bukatar sai mutum yaje cibiyar CBT ko kuma inda ake aiki da yanar gizo wato CYBER CAFE domin duba sakamako.

Oloyede ya kara da cewa muddin ka tura sakon RESULT zuwa ga 55019 ta hanyar amfani da lambar wayar da akayi rajista da ita., to idan sakamakon ka ya fito, za ka ga an turo maka amsa cewar:

“Zuwa Gare ka, ga sakamakon jarabawarka kamar haka….”

Idan kuma an rike maka sakamako ne, to za a turo maka sakon: “RESULT WITHHELD”, wato “AN RIKE SAKAMAKON KA.”

Idan ka yi rajista amma ba ka rubuta jarabawa ba, za a turo maka sakon “CANDIDATE ABSENT”, wato “BA KA RUBUTA JARABAWA BA.”

Idan kuma an rike sakamakon ka, har zuwa lokacin da za a kammala wani bincike, to za a tura maka sakon: “AN RIKE SAKAMAKON KA sai an gama bincike a turo maka.”

Da fatan wannan rubutun ya taimaka sosai, zaku iya tuntubanmu ta wayannan hanyoyin idan kuna bukatar taimakon gaggawa ko kuma Karin bayani:

Kira: 09039016969
Whatsapp: 09039016969
Tura Zuwa:

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala 

Babu shakka kayan kwalliya na taimakawa matuka wajen bunkasawa da kuma kara fito da kyanki. Kai kayan kwalliya irin na zamani ba kayata kyau ba ma har kawar da muni suke yi. Zan iya cewa irin kayan kwalliyan da ake da shi yanzu da wadanda ake kirkira a kullum, amshin addua ne ga masoya kwalliya a duk fadin duniya.

KARANTA: "ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"


Sai dai akwai matsala. Sau daya yadda muke amfani da kayan kwalliyan kan iya haifarwa fatarmu matsalar da kayan kwalliyan ko dubu nawa ba za su iya rufewa ba. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda uku (3) da ake amfani da kayan kwalliya wadanda fata da ace tana da baki da ta koka:

1.==> Kwana da kwalliya a fuska: A lokacin da muke barci ne jikinmu ke aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin da sassan jikinmu ke fuskanta, ba’a bar fata a baya ba. A yayin da muka kwanta barci da kwalliya, hakan baya samuwa domin kuwa kayan kwalliya na yin kane kane a cikin kofofin fata su hana ruwa gudu. A dan haka sinadaran da zasu karawa fatarmu inganci, kyawu da sheki ko dai daga wani mai da muka shafa akan fatar ko kuma wanda jikinmu ya sarrafa daga abinci ba zasu iya yin amfaninsu ba yadda ya kamata.

Karanta: Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi


Idan mutum mai saurin samun kuraje ne, hakan yakan kawo su da gaggawa, idan ma ba kya yin kuraje to tabbas za ki tashi daga barci kiga fatarki ta rasa shekinta da kyawunta. Ci gaba da yin hakan zai tabbatar da lalacewar fatarki a nan gaba. Ki tabbatar kin wanke kayan kwalliya tsaf daga fatarki, daga su har kamu kamunsu kafin ki yi barci da daddare dukkuwa irin gajiyar da kika yi.

2.==> Amfani da kayan kwaliyan da irinsu bai dace da irin fata ba: Idan fatarki tana da maiko, ki ka je kika sayi kayan kwalliya masu tushe mai maiko, toh kinyi amfani da kudinki kin jibgawa kanki aiki, gani da yadda suke da matukar tsada ma a yanzu ya sa ya cancanta ayi maki jaje. Dalili kuwa shine maimakon ki kara kyau, da kin shafa sai fuska ta cika da maiko.

Banda toshe kofofin fata da kayan kwalliyan sukayi, ga kuma maiko ya zo ya kara na shi akai. Hakan yana haifar dawa fata matsala matuka.

Haka kuma idan kina da busasshiyar fata kika fara amfani da kayan kwalliya marasa maiko, nanma fa akwai matsala domin kuwa fatarki zata yi ta bushewa har ta fara yamushewa ta zama kamar ta tsohuwa. Banda hakan ma, wani lokaci irin sinadaran da ke cikin kayan kwalliya masu hatsari ne ga lafiyar fata, shi yasa za gi ga yawanci an rubuta cewa ki dan gwada kadan a matse matsin gwiwar hannunki na tsahon awanni kafin ki fara amfani da shi. Amma da yawanmu bama yin hakan. Sai an gama shan kyau, fata kuma ta zo ta zama kamar taswirar Nijeriya, a zo ana cewa an samu ‘skin reaction’ da ba’a san dalilin sa ba.

3.==> Amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa: Brushes din da ake amfani da su wajen yin kwalliya da bakin kayan kwalliya na matsawa irin su foundation gurin taruwar kwayoyin cuta suke zama. Shi yasa aka shawarci ma’abota kwalliya da su tabbatar cewa ko da yaushe sun ajiyesu a guri mai tsabta, sun kuma tabbatar da ba’a hada amfani da su da kowa ba.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Ban da haka ana so a daina amfani da mascara guda daya bayan wata 3, shi kuma foundation bayan shekara daya. Idan basu kare ba kawai zubar da su ake. Brushes kuma za’a iya wanke su a cikin ruwan zafi domin kashe kwayoyin cutar lokaci lokaci. Ajiye kayan kwalliyan nan a cikin jaka daya su hada datti su hada datti ba alkahairi bane ga fatarki, wani lokacin ma har kaisu baki ake yi wanda anan ma zasu iya kwaso matsala daga yawun baki. Ya kamata dai a kiyaye, domin ni fa na fi son naga kowa tsaf tsaf, fata na sheki kamar wancan abun da na manta sunashi.
Tura Zuwa:

Amfanin Cin Namijin Goro

Amfanin Cin Namijin Goro


Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu maudu’inmu a yau zamu tattaunane akan wani abu mai muhimmanci wadda sau da dama mutane sukanyi tambaya akan sa; Ana ce masa ‘Garcinia kola’ amma a sauƙaƙe anfi kiransa da Namijin Goro kuma tushensa da tsirransu sun fito ne daga Afrika ta tsakiya. Wanda hakan ke nuna irin mahimmancin da nahiyar ta Afirka ke da shi a fannin tsirrai. Namijin Goro yana samar mana da ɗimbin hanyoyin warkar da cututtuka na mamaki. Yana daga cikin dangin tsirrai na Fulawa yana kuma fita da launin ruwan ƙasa.


AMFANIN GA HUHU: Yana magance Huhu da wasu sassa na jikin mutum sannan suna taimakawa wajen gudanar manyan ayyuka a cikin jikin mutum. yana taimaka mana wajen yin numfashi.

Cin irin sa yadda ya dace, yana taimakawa Huhu wajen gudanar da aiki yadda ya kamata kuma ya bada kariya a cikin jikin mutum. Yana kuma taimakawa hanyoyin Jini haka yana magance sanyi na zuciya. Saboda haka, ga mutane masu zuƙar Taba Sigari, namijin goro na iya zame musu magani.

MAGANIN CUTAR CIZON SAURO: Irin Namijin Goro ana taimakwa wajen warkar da cutar cizon Sauro. Ba mamaki da masu magungunan gargajiya suka bada shawara a riƙa yin amfani dashi. Ba a bayyana wata illa da Namijin Goro keyi wa mutum a jikin sa ba saboda yin amfani dashi.

Amma a wasu lokutan, cin Namijin Goron yana janyo wasu illoli a jiki. DAIDAITA BUGUN ZUCIYA YADDA YA KAMATA: Wasu sassan na jikin mutum sukan nuna ƙyama wajen cinsu ɗin wasu itatuwan, inda cinsu ke janyowa jikinsu wani irin yanayi. A irin wannan yanayin yana da kyau mutum ya tuntuɓi Likitansa ya kuma daina yin amfani dashi.

Karanta: Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace


A yanzu mun riga mun san cewar Namijin Goron, ba wai lallai ɗaci kawai yake dashi ba, yana kuma da ɓangare na zaƙi wanda kuma yana taimakawa wajen ƙara lafiyar jiki a gare mu.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *