HANYOYIN DA ZA'A MAGANCE TALLACE-TALLACE GA 'YAYA MATA?
Iyaye maza suji tsoron Allah su rika sauke nauyi tareda hakkokin da Allah SWA ya dora musu. Ma'ana Tarbiyyantarwa, Ilimantarwa, ciyarwa, shayarwa, Sutura da sauransu. Domin nafahimci dayawa rashin sauke nauyin da maza basayi akan iyalansu shiyake jaza wasu iyayen suke dora wa yaransu talla domin su samu abunda zasuciyar dasu, wanda idan ba Allah ya kare ba sai asamu gur6acewar tarbiyya.
YAWANCI A KARAMAR HUKUMAR JIBIA BABU KUNGIYOYIN MATA, SHIN ME KIKE GANIN YA KAWO WANNAN KOMA BAYAN, SANNAN KINA GANIN IN KIKA SAMU ANAN GABA ZAKI KAFA TAKI KUNGIYAR?
Gaskiya mafi yawanci kowa yana hidimar gabansa ne, kuma ba'a samu wanda suka share fili suka kafa kungiya ba balantana mu yan baya muyi koyi dasu. Insha Allahu idan har nasamu dama tareda tallafi da hadin kai daga shuwagabanni da masu mulki na karamar hukumu ta ba abinda zai hanani kafa kungiyar mata.
ZAMANI YAZO ZAKI GA MATASA MAZA DA MATA, SUN FADAWA HARKOKIN SHAYE-SHAYE, ME KIKE GANIN YANA KAWO HAKAN, SANNAN SAKACIN DAGA INA NE?
Allah shi yake shiryar da wanda yaso, amma kashi casa'in bisa dari zan danganta gur6acewar tarbiyyar yaya akan mahaifansu musamman uwa mace. Domin hakkintane takula da shige da ficen yayanta, dawa suke mu'amala, suwaye abokanensu, ina da ina suke zuwa idan sun fita. Saboda shi uba idan yasa kafa yafita tun safe wani baya dawowa sai dare. Wani na ba agarin yake harkokin sanaarsa. Idan har uwa zatasa isa ido wa rayuwar yaranta tareda taka tsan tsan gurin tarbiyyarsu da hanasu yawo da abokanen banza da zama majalissu na zaman hakan zaa samu saukin matsalar nan. Domin sai idan suna cudanya da abokan banzan zasu samun kayan mayen.
AURE
A yanzu dai kam banda aure, amma inada niyya nan kusa bada dadewa ba In Allah ya yarda.
KIN BAYYANA YAWANCIN LALACEWAR 'YA'YA DAGA SAKACIN IYAYE NE, SHIN MISALI SAI KI HADU DA 'YA MACE TANA SHAYE-SHAYE, WADANNE SHAWARWARI ZAKI BATA?
Ta yiwa kanta da yayan da zata haifa kiyamullaili ta daina, domin kima daraja da martabarta zasu zube a idon duniya. Sannan kayan mayen data kesha zai iya taba lafiyar wani sashe na jikinta.
ABINCI, DA SUTURA?
Ina sa kowane irin kaya amma nafison Arabian wears, irin jallabiyu haka.
Sannan nafison ganyayyaki da kayan rafi dakuma abinci marar nauyi.
ABINDA TAKE SON A DINGA TUNAWA DA'ITA
Kyawawan halayena, hallaci, tausayi, hakuri tare da kyautatawa.
BURINTA A RAYUWA
Nayi aure, Na haifi yara, kyautatawa mahaifana da yan uwa da dukkanin al'umma baki daya. Sannan inaso nasamu ilimi mai zurfi. Inaso mahaifana suyi alfaharin kasancewata diya A gurinsu, mijina yayi alfaharin kasancewa dani A Matsayin matarsa uwar yayansa. Al'ummar karamar hukumata suyi alfaharin samun mai kishinsu tare da kyautata musu ta kowace hanya.
DARUSSAN DANA KOYA A RAYUWA
Rayuwa tana dauke da kalubale daban-daban. Hakikanin gaskiya nakoyi darasi sosai akan halayen mutanen mu Na yanzu wanda suka hada da rashin halacci, cin amana, yaudara, karya, ha'inci, saurin manta alkhairi, rama alkhairi da sharri, Aibantawa, da kuma son zuciya.
SHAWARA GA IYAYE MATA
Su jajirce gurin bawa yaransu tarbiyya da ilimi. Sannan su tashi tsaye gurin neman Na kansu, su bar raina kananun sana'o'i domin kuwa duk wanda yayi zuru to lallai zai ga zuru.
IDAN BA ZAN TABA MANTAWA DASHI BA
Cin Amanata daga gurin wanda na yadda dashi kuma na amince dashi.
KYAUTAR DA AKAI MAN DA BAZAN MANTA BA
Kyauta ce tsakanina da dan uwana Abdullahi Salisu Garba Kwangee wanda yake karatu a Jamiar Al azhar ta kasar Misra. Ina alfahari da kasancewarsa yaya a gurina.
YA KIKE JI A RANKI, IDAN WANI KO WATA SUKA ZO NEMAN TAIMAKO WAJANKI?
Ina tsintar kaina acikin farin ciki idan har Allah ya bani ikon taimakawar, sannan na kan kasance cikin bakin ciki idan naga wani yana bukatar taimako amma ina ji ina gani abun ya gagareni ba yanda zanyi saboda banda abun taimakawar musamman a gurin aikina wato Asibiti.
SAKONA NA KARSHE GA 'YAN SOCIAL MEDIA DA KUNGIYOYI
Muji tsoron Allah mu kiyaye abubuwan da basu dace ba a social media, misali yanzu zaka ga matasa masu kananan shekaru sun zama yan bangar siyasa ana anfani dasu gurin zaki, suka tare da aibanta wani a social media. Mu tashi tsaye mu nemi na kanmu mu daina zuru tare da bin yan siyasa. Sannan idan ant ashi gina kungiya ar ika gina me amfani wacce zata amfani al'umma baki daya.
Home »
marubutanmu
» "Karatun 'Ya Mace hanyar dogaro da kai ne" 2
"Karatun 'Ya Mace hanyar dogaro da kai ne" 2
mawallafi: Muhammad Abba Gana
Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.
No comments:
Post a Comment