"Karatun 'Ya Mace hanyar dogaro da kai ne"
•Mrs Aisha Salisu Garba Kwangi
Aisha salisu garba kwangi daya ce daga cikin fitattun matan arewa diya ce ga tsohon Chairman' Na k'aramar hukumar jibia, Duk da kasancewarta budurwa amma ta kasance jaruma, Wadda ke kokarin ganin ba'a bar mata baya ba ta fannin karatu da Al'amuran rayuwa, a tattaunawarta da Zaidu Ibrahim Barmo a shirin "Matan Arewa" da shafin "Zauren Marubutan Hausa" ke daukar nauyin kawowa, ta fad'i tarihinta da Nasarorin data samu, har ma da shawarwari ga mata.
Ga dai yadda tattaunawar ta kasance,
•MrZaid:
Ni da dukkan masu karatu muna maki barka da zuwa a wannan fili.
Kamar yadda Ka'idar shirin take, Mu kan gayyato matan arewa, domin jin wainar da suke toyawa, da kuma Halin da 'yan uwansu mata suke ciki.
Bari mu fara da tarihin rayuwarki?
TARIHINA
Assalamu Alaikum Warahmatullah. Dafarko kamar yanda kafada Sunana Aisha Salisu Garba Kwangi. An haifeni a ranar Ashirin da hudu ga watan Nuwanban shekara alif Dubu daya da dari tara da casa'in da uku, a karamar hukumar Jibiya ta jahar Katsina. Nayi Nursery and Primary School dina a Katsina capital School, Sannan nayi karatun gaba da Primary wato Secondary School a makarantar kimiyya da ta gwamnati ta Sandamu wato GGSSS Sandamu Daura. Bayan nan najona Karatuna a Hassan Usman katsina Polytechnic inda nakaranci Nutrition and Dietetics wanda bayan kammalawata nasamu aiki a General Hospital Jibiya. Yanzu haka ina aiki anan Kuma ina saran cigaba da karatu bada dadewaba Insha Allah.
Inazuwa Madarasatul Tarbiyyatul islamiyya Jibiya.
NASARORIN DA TA SAMU?
To Alhamdulillah, da farko zan fara godiya ga Allah SWA bisa dukkanin ni'imominsa akaina, sannan ina godiya ga Mahaifana domin da taimakon Allah da taimakonsu nakai matsayin danake akai yanzu. Saboda jajircewarsu ganin sun bani ilimi na addini dana zamani dama tarbiyya baki daya. Duk wanda Allah ya azurta da ilimin addini dana Zamani dakuma tarbiyya hakika yasamu babbar nasara arayuwa. Domin kuwa karatunda natsaya na jajirce nayi shi yakaini amatsayin dake ayanzu wanda dayawa basu samu damar hakan ba.
KARATUN 'YA MACE A FAHIMTARKI?
A gaskiya karatun 'ya mace yanada matukar fa'ida sosai musamman a yanayin rayuwar da muke a ciki yanzu. Domin ni nagani akan kaina dama wasu daga cikin 'yan uwana da kawaye makusanta. Na farko hanyar dogaro dakai ne, zai taimaka mata gurin daukar nauyin ragamar rayuwarta koda tayi aure bazata dogara da sai abinda mijinta yayi mata ba. Kuma zata tallafawa mahaifanta dasauran 'yan uwanta. Sannan zai amfani abinda zata haifa. Malam bahaushe yace idan ka ilimantar da diya mace daya tamkar ka ilimantar da al'umma ne baki daya.

KUNGIYOYI
So a gaskiya K'ungiyoyi da yawa suna kawo mun takaddun gayyata, amma bana amsa musu saboda kasancewata marar son hayaniya da yawan tafiye tafiye zuwa tarurruka. Amma duk da haka ina cikin K'ungiyar JIBIA YOUTH FORUM A matsayin Mataimakiyar Shugabar Mata (Women Leader).
BURIN KAFA GIDAUNIYA?
Insha Allah, inada wannan kudurorin a raina. Duba da yanayin halin kunci da mata 'yan uwana da kananun yara suke shiga musamman a gidajen aurensu da asibitoci. Idan Allah yabani iko zan kafa gidauniya domin Tallafawa iyayenmu mata da 'yan mata da hanyoyin da zasu dogara da kansu da kananun sana'o'i domin samun abunda zasu rike yayansu. Sannan gidauniyar zata tanadi asusu domin bada taimakon gaggawa a asibitoci na karamar hukumata, domin kuwa ana rasa rayuka da dama saboda kudi kalilan na siyan magunguna.
BARI MU DAWO BAYA KADAN KIN BAYYANA KIN GAMA MAKANRANTAR KIMIYYA DA FASAHA DAKE KATSINA,POLYTECHNIC
Me kika karanta, Sannan nan gaba me kike son karanta?
•Aisha kwangi: Nutrition and Dietetics, kuma a kansa zan cigaba daga inda natsaya Insha Allah.
No comments:
Post a Comment