Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Za’a Magance Rashin Tashiwar Kwanfuta A Kan Lokaci

Yadda Za’a Magance Rashin Tashiwar Kwanfuta A Kan Lokaci


Assalamu Alaikum barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wadda ke zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha. Zaiyu kana daya daga cikin wayanda suke fuskanta kalu bale wajen rashin tashiwar kwanfuta a kan lokacin daya kamata wadda ake masa lakani da slow booting a turanche.

Tura Zuwa:

Soyayyar Taliya Da kaza

Soyayyar Taliya Da kaza


Uwar Gida idan babu ke babu cikkane gida haka zalika rashinki tamkar rashin wani bangarene na jiki, Assalamu Alaikum barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa daku A cikin shirin namu na Girke-Girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha.
Tura Zuwa:

Sirrin Da Ke Tattare Da Shan Kankana

Sirrin Da Ke Tattare Da Shan Kankana

Kankana yana daya daga cikin kayan marmari da muke sha a yawancin lokuta, duk da cewar bamu san me amfaninta ga lafiyar jikin mu ba, watakila saboda arharta da ganinta da mu ke yi banza-banza sakamakon yawanta a gonaki, lambuna, kasuwanninmu sannan kuma ko wani lubgu zuwa sakon cikin gari , a hakikanin gaskiya kankana na daya daga cikin manyan abincin da za mu iya masa lakani da “MAGANI A GONAR YARO”. Yana da kyau mu fahimci cewar ba duk abinda Allah ya ba mu shi a wadace ba ne ya ke da karancin amfani ko muhimmanci a garemu.

Tura Zuwa:

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019


Muhammad Abba Gana


Mutane da dama sukanyi tambaya shin da gaske ne an sake Sakamakon Jarabawara NECO Na Shekaran 2019? Kwarai kuwa da gaskene. Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sanarwar cewa ta sake sakamakon jarabawar dalibai na dubu biyu da sha tara (2019) ta kara da cewar kashi saba’in da daya (71%) bisa dari na daliban da suka rubuta sun sami credit a harshen turanci (English) da kuma lissafi (Mathematics).    

Tura Zuwa:

Wasu Daga Cikin Amfanonin Zogale Ga Lafiyar Jiki

Wasu Daga Cikin Amfanonin Zogale Ga Lafiyar Jiki

Muhammad Abba Gana


Wasu lokutan mukan ci wasu abubuwa saboda marmari, ra’ayi, dadi ko kuma kwadayi ba tare da sanin wani irin amfani zai kawo mana ga lafiyar jiki ba ko kuma illa ba. Wasu abinci ko kayan marmari na dauke da kwayoyi da dama da ke taimakawa lafiyar jiki wajen ginata wasun kuma suna dauke da kwayoyin sinadari wadda zai iya taimakawa wajen kawo wa lafiyar jikin illa. Bisa la’akari da mujallar Dunyan Fasaha tayi, yau zamu tattaunane game da amfani zogale ga lafiyar jiki.

Tura Zuwa:

Illar Sanya Mahajar (Application) Launcher Akan Wayar Salula

Illar Sanya Mahajar (Application) Launcher Akan Wayar Salula


Lokaci zuwa lokaci mukanyi ababe da dama, a ranmu mukan ji daidai ne wadda kuma a hakikanin gaskiya ba daidai bane wasu lokacin son raine wasu lokutan kuma rashin sani ne. A mafi yawancin lokutan mukan biyewa ra’ayinmu ne ko kuma ita zuciyarmu wadda hakan kan zama mana matsala a nan gaba ko kuma ta sanya mu cikin kunchi da la haula.

Tura Zuwa:

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sabon sanarwar cewa ta bude sabon shafinta wadda zai taimaka wa dalibai na kasa baki daya wajen duba sakamakonsu na karshen zango. Wannan sabon shafin ya sha babban da wadda ya gabata, a shekarun baya idan mutum yana bukatan yaga sakamakonsa na jarabawar NECO to fa dole lallai sai ya siya katin gogewa wadda aka fi sani da scratch card a turanche.   

Tura Zuwa:

MIYAR ZOGALE

MIYAR ZOGALE 
Kamar yadda mukayi bayani a baya zogale na taimakawa lafiyar jiki matuka ta hanyoyi daban daban ta hanyar shan sa ko kuma ta hanyar cin miyarsa. Insha Allahu yau kuma Duniyan Fasaha ta kawo muku bayani ne akan yadda ke tsara miyan zogale cikin sauki wadda zai so sa kunne mai gida sannan kuma ya sa yara santi. A sha karatu lafiya.

Tura Zuwa:

Cikkanen Bayani Game Da Amfanin gurji a fatan Dan Adam

Cikkanen Bayani Game Da Amfanin gurji a fatan Dan Adam

Gurji ba abunci kadai bane, Gurji ba abun abinci bane ko kuma abun marmari kadai ba shi gurji masana kimiyya sunce gurji yana dauke da sinadaran magance gautsin fata sannan yana taimakawa wajen sanya fata sheki da laushi cikin sauki sannan kuma a yan kankanin lokaci.

Tura Zuwa:

Abinci Kala 6 Da Ke Tsayar Da Gudawa Cikin kankanin Lokaci

Abinci Kala 6 Da Ke Tsayar Da Gudawa Cikin kankanin Lokaci

Kowa da kallar cikinsa sannan kuma da abunda shi cikin nasan yake so, abincin wani yakan zama gubar wani. A mafin yawanci lokuta mukan sami matsaloli da dama ta bangaren shi ciki yakan kasance munci ko munsha wani abu wadda cikinmu bayaso hakan shi yake jawo mana matsala wani lokutan sai kaga mutum ya sami barkewar ciki in kuma hakan ya auku ba wani abunda mutum zayyi tayi face gudawa in kuma yazo da rashin sa’a sai abun ya hade harda amai.

Tura Zuwa:

Yadda Ake Sa Hoto A Post A Shafin Blogger

Yadda Ake Sa Hoto A Post A Shafin Blogger

Muhammad Abba Gana

Shafin blogger yana daya daga cikin sanannun kuma manyan shafuka a yanar gizo wadda suke taimakawa wajen rubutun ra’ayin kai, shafin blogger yana bayar da damar isar da sakonni ta hanyar rubutu, hoto ko kuma hoto mai motsi wadda aka fi sani da video a turance. A makonni da suka gabata munyi jawabi a bangarori daban daban daya kama da:

Tura Zuwa:

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA


Muhammad Abba Gana

Kowani ciwo yana da magani hakan take; mata da dama sukan koka wajen yadda maran su ke ciwo lokacin al’ada, hakan yana faruwane bisa wasu dalilai. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku wata hanya da zaku bi wadda da izinin Allah za’a dace.

Karanta: Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala


1. ==> A samu Tsohuwar Tsamiya a jika aruwa tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan tun kwana biyu kafin zuwa haila, har lokacin da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da dama sun jarraba kuma sun dace.

2. ==> MAN ZAITUN: A sami man zaitun sai a Karanta ayoyin Alqur'ani acikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta.

Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al'aurarta saboda ayoyin da aka tofa). Shima wannan idan anyi shi za'a dace. Koda Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke sanya mata ciwon jikin to zata samu waraka.

3. ==> KUSTUL HINDI: Idan an jikashi a ruwa ana shansa safe da yamma shima yakan Magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al'ada. Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Da fatan Allah shi amshi dukkan abinda muke roka ma junanmu. Allah yasa mu dace. Ameen!

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Muhammad Abba Gana

Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu yau zamuyi jawabine akan yadda ake duba sakamakon jarabawar Jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019).

Mutane da dama sun kosa matuka wajen son suga sakamakon jarabawar jamb na shekaran dubu biyu da sha tara (2019), musamman ma iyaye da kuma dalibai. Wasu daliban suna cikin tsaka mai wuya saboda labarai da ke fitowa yan wasu makonni da suka shude cewar dalibai da dama baza suga sakamakon jarabawansu ba sabili da sun jefa kansu cikin haramcecciyar hanya wato sata. Haka zalika wasu daga ciki za’a rage addadin abinda suka samu a cikin jarabawar.


Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa wato (JAMB), ta bayyana cewa jarabawar JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) ta fito a Asabar data gabata. Sannan kuma hukumar ta ce babu ruwan dalibi da zuwa cibiyoyin rubuta jarabawa domin ganin sakamako.    

“Daga yau har zuwa ranar Litinin, wannan ce kadai hanyar da za’a iya ganin sakamakon jarabawa.” Ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin hana ‘yan damfara su damfari mutane batun ganin sakamakon jarabawa. Sannan kuma an fito da wannan dabara ce domin duk wanda bai ga sakamakon sa ba, to ya na daga cikin wayanda aka rike sakamakon su.

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito


Sannan ya ce hakan ya na nufin an daina zuwa ana yin cunkoso a wurin duba jarabawa, inda wadanda ba su ga ta su ba ke yin dafifi a wuraren duba jarabawa ana haddasa cinkoso.

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB 2019


Wannan wata hanyace mafi sauki ga wadanda suka rubuta jarabawar shiga makarantun jami’a ta JAMB na shekaran dubu biyu da sha tara (2019) da zasu iya duba sakamakonsu.

Babu bukatar sai mutum yaje cibiyar CBT ko kuma inda ake aiki da yanar gizo wato CYBER CAFE domin duba sakamako.

Oloyede ya kara da cewa muddin ka tura sakon RESULT zuwa ga 55019 ta hanyar amfani da lambar wayar da akayi rajista da ita., to idan sakamakon ka ya fito, za ka ga an turo maka amsa cewar:

“Zuwa Gare ka, ga sakamakon jarabawarka kamar haka….”

Idan kuma an rike maka sakamako ne, to za a turo maka sakon: “RESULT WITHHELD”, wato “AN RIKE SAKAMAKON KA.”

Idan ka yi rajista amma ba ka rubuta jarabawa ba, za a turo maka sakon “CANDIDATE ABSENT”, wato “BA KA RUBUTA JARABAWA BA.”

Idan kuma an rike sakamakon ka, har zuwa lokacin da za a kammala wani bincike, to za a tura maka sakon: “AN RIKE SAKAMAKON KA sai an gama bincike a turo maka.”

Da fatan wannan rubutun ya taimaka sosai, zaku iya tuntubanmu ta wayannan hanyoyin idan kuna bukatar taimakon gaggawa ko kuma Karin bayani:

Kira: 09039016969
Whatsapp: 09039016969
Tura Zuwa:

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala

Cikakken bayani yadda kayan kwalliyan zamani ke haifarwa fata mummunan matsala 

Babu shakka kayan kwalliya na taimakawa matuka wajen bunkasawa da kuma kara fito da kyanki. Kai kayan kwalliya irin na zamani ba kayata kyau ba ma har kawar da muni suke yi. Zan iya cewa irin kayan kwalliyan da ake da shi yanzu da wadanda ake kirkira a kullum, amshin addua ne ga masoya kwalliya a duk fadin duniya.

KARANTA: "ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"


Sai dai akwai matsala. Sau daya yadda muke amfani da kayan kwalliyan kan iya haifarwa fatarmu matsalar da kayan kwalliyan ko dubu nawa ba za su iya rufewa ba. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda uku (3) da ake amfani da kayan kwalliya wadanda fata da ace tana da baki da ta koka:

1.==> Kwana da kwalliya a fuska: A lokacin da muke barci ne jikinmu ke aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin da sassan jikinmu ke fuskanta, ba’a bar fata a baya ba. A yayin da muka kwanta barci da kwalliya, hakan baya samuwa domin kuwa kayan kwalliya na yin kane kane a cikin kofofin fata su hana ruwa gudu. A dan haka sinadaran da zasu karawa fatarmu inganci, kyawu da sheki ko dai daga wani mai da muka shafa akan fatar ko kuma wanda jikinmu ya sarrafa daga abinci ba zasu iya yin amfaninsu ba yadda ya kamata.

Karanta: Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi


Idan mutum mai saurin samun kuraje ne, hakan yakan kawo su da gaggawa, idan ma ba kya yin kuraje to tabbas za ki tashi daga barci kiga fatarki ta rasa shekinta da kyawunta. Ci gaba da yin hakan zai tabbatar da lalacewar fatarki a nan gaba. Ki tabbatar kin wanke kayan kwalliya tsaf daga fatarki, daga su har kamu kamunsu kafin ki yi barci da daddare dukkuwa irin gajiyar da kika yi.

2.==> Amfani da kayan kwaliyan da irinsu bai dace da irin fata ba: Idan fatarki tana da maiko, ki ka je kika sayi kayan kwalliya masu tushe mai maiko, toh kinyi amfani da kudinki kin jibgawa kanki aiki, gani da yadda suke da matukar tsada ma a yanzu ya sa ya cancanta ayi maki jaje. Dalili kuwa shine maimakon ki kara kyau, da kin shafa sai fuska ta cika da maiko.

Banda toshe kofofin fata da kayan kwalliyan sukayi, ga kuma maiko ya zo ya kara na shi akai. Hakan yana haifar dawa fata matsala matuka.

Haka kuma idan kina da busasshiyar fata kika fara amfani da kayan kwalliya marasa maiko, nanma fa akwai matsala domin kuwa fatarki zata yi ta bushewa har ta fara yamushewa ta zama kamar ta tsohuwa. Banda hakan ma, wani lokaci irin sinadaran da ke cikin kayan kwalliya masu hatsari ne ga lafiyar fata, shi yasa za gi ga yawanci an rubuta cewa ki dan gwada kadan a matse matsin gwiwar hannunki na tsahon awanni kafin ki fara amfani da shi. Amma da yawanmu bama yin hakan. Sai an gama shan kyau, fata kuma ta zo ta zama kamar taswirar Nijeriya, a zo ana cewa an samu ‘skin reaction’ da ba’a san dalilin sa ba.

3.==> Amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa: Brushes din da ake amfani da su wajen yin kwalliya da bakin kayan kwalliya na matsawa irin su foundation gurin taruwar kwayoyin cuta suke zama. Shi yasa aka shawarci ma’abota kwalliya da su tabbatar cewa ko da yaushe sun ajiyesu a guri mai tsabta, sun kuma tabbatar da ba’a hada amfani da su da kowa ba.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Ban da haka ana so a daina amfani da mascara guda daya bayan wata 3, shi kuma foundation bayan shekara daya. Idan basu kare ba kawai zubar da su ake. Brushes kuma za’a iya wanke su a cikin ruwan zafi domin kashe kwayoyin cutar lokaci lokaci. Ajiye kayan kwalliyan nan a cikin jaka daya su hada datti su hada datti ba alkahairi bane ga fatarki, wani lokacin ma har kaisu baki ake yi wanda anan ma zasu iya kwaso matsala daga yawun baki. Ya kamata dai a kiyaye, domin ni fa na fi son naga kowa tsaf tsaf, fata na sheki kamar wancan abun da na manta sunashi.
Tura Zuwa:

Amfanin Cin Namijin Goro

Amfanin Cin Namijin Goro


Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha, insha Allahu maudu’inmu a yau zamu tattaunane akan wani abu mai muhimmanci wadda sau da dama mutane sukanyi tambaya akan sa; Ana ce masa ‘Garcinia kola’ amma a sauƙaƙe anfi kiransa da Namijin Goro kuma tushensa da tsirransu sun fito ne daga Afrika ta tsakiya. Wanda hakan ke nuna irin mahimmancin da nahiyar ta Afirka ke da shi a fannin tsirrai. Namijin Goro yana samar mana da ɗimbin hanyoyin warkar da cututtuka na mamaki. Yana daga cikin dangin tsirrai na Fulawa yana kuma fita da launin ruwan ƙasa.


AMFANIN GA HUHU: Yana magance Huhu da wasu sassa na jikin mutum sannan suna taimakawa wajen gudanar manyan ayyuka a cikin jikin mutum. yana taimaka mana wajen yin numfashi.

Cin irin sa yadda ya dace, yana taimakawa Huhu wajen gudanar da aiki yadda ya kamata kuma ya bada kariya a cikin jikin mutum. Yana kuma taimakawa hanyoyin Jini haka yana magance sanyi na zuciya. Saboda haka, ga mutane masu zuƙar Taba Sigari, namijin goro na iya zame musu magani.

MAGANIN CUTAR CIZON SAURO: Irin Namijin Goro ana taimakwa wajen warkar da cutar cizon Sauro. Ba mamaki da masu magungunan gargajiya suka bada shawara a riƙa yin amfani dashi. Ba a bayyana wata illa da Namijin Goro keyi wa mutum a jikin sa ba saboda yin amfani dashi.

Amma a wasu lokutan, cin Namijin Goron yana janyo wasu illoli a jiki. DAIDAITA BUGUN ZUCIYA YADDA YA KAMATA: Wasu sassan na jikin mutum sukan nuna ƙyama wajen cinsu ɗin wasu itatuwan, inda cinsu ke janyowa jikinsu wani irin yanayi. A irin wannan yanayin yana da kyau mutum ya tuntuɓi Likitansa ya kuma daina yin amfani dashi.

Karanta: Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace


A yanzu mun riga mun san cewar Namijin Goron, ba wai lallai ɗaci kawai yake dashi ba, yana kuma da ɓangare na zaƙi wanda kuma yana taimakawa wajen ƙara lafiyar jiki a gare mu.
Tura Zuwa:

Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki

 A zamanin da muka tsinchi kanmu a yanzu, wayar salula ya zama wani bangarene a cikin rayuwanmu sabili da bazamu iya numfasa wa ba tare da shiba balle a zo ta bangaren zamantakewa. Wadda yawan amfani dashine ke haddasa mana wasu matsaloli da dama ta bangaren wayar salulan haka zalika a wasu lokutan yakan shafi ita rayuwar mu.

A kowani wayewar gari matsaloli kara habbaka suke haka zalika hanyoyin da za’a magance matsalar na karuwa, na kasance ina amfani da wayar salulan android kusan shekara bakwai Kenan amma karo na farko Kenan dana fuskanci wata babbar matsala.

Wayata na nuna alamar shigowar kira ta hanyar yin kara tare da nuna flash light a baya wadda ke tabbatar min da cewar lallai kira ya shigo amma danayi yunkurin dauka kiran sai ga abun mamaki screen din ba alamar wajen daukawa; da fari na dau wayar ne ya gigice hakan yasa nayi saurin kashe wayar na chire battery tare da mayarwa, haka zalika banyi kasa a gwiwa ba wajen sake kunnata.

Bayan wasu yan mintuna abinda ya faru a baya ya sake aukuwa. Ga alamar shigowar kira amma kuma ba wajen dazan dauka balle nasan wadda yake kira, hakan yasa na yanke shawarar rubuta yadda za’a magance matsalar wadda a hakikanin gaskiya nasan akwai mutane da dama dake fuskartar matsala data auku dani.

Magance matsalar nada matukar sauki sai dai dole sai an bi wasu yan matakai wadda zanyi jawabi a gaba, matakan basu bukatar wani abu daya hada da yanar gizo, kudi, wani mahaja kokuma wani wayar salulan.    

Yadda za’a magance matsalar cikin sauki

1.==> Da fari za’a ziyarchi “Settings” na waya.

Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki


2.==> Sai a dubi “Applications” ko kuma “Apps & Notifications” sai a danna.


Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki


3.==> Sai a zabi “System Application” a wasu wayoyin kuma za’a ga “See All Apps”. 


Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki

Sannan a duba mahaja mai suna “Phone”.


Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki


4.==> Za’a ga “Clear Data” ko kuma “Clear Cache” a rubuce a sama ta bangaren hannun dama, 


Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki


sai a  danna daya daga ciki daga nan wani sako zai fito sai a latsa “Ok” domin tabbatarwa amma a mafi yawancin lokacin baya fitowa.

A wasu wayoyin kuwa ba lallai bane a same su a chan sama wajen hannun dama da zaran an shiga shi majahar na “Phone” wato mataki na uku sai a zabi “storage” za’a ga “Clear Data” ko kuma “Clear Cache” a rubuce a sama ta bangaren hannun dama, sai a danna daya daga ciki daga nan wani sako zai fito sai a latsa “Ok” domin tabbatarwa; haka zalika mafi yawancin lokacin baya fitowa.       

Shikenan an maganace matsalar cikin sauki. Shin kina/kana da wata hanya da ki/ka ke ganin zai taimaka matuka wajan magance wannan matsalar da ban ambata ba cikin wannan kasidar ba? Za’a iya turo mana dan dad’awa wanda zai taimaka wa masu ziyara nan gaba.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan 
Tura Zuwa:

Dalilin da ke sa waya taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta sauka da wuri


Dalilin da ke sa waya taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta sauka da wuri

Dalilin da ke sa waya taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta sauka da wuri

Assalamu Alikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu insha Allahu yau zanyi bayanine akan abubuwan dake sa wayar salula taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta na sauka da wuri bayan ta cika da charge a hakikakin gaskiya akwai matsaloli da dama wayanda suke sa waya taqi cika da wuri ko kuma tana qarewa da wuri amma zanyi jawbine a kan manyan umulhaba’isin daga cikinsu.

lokuta da dama zakaga mutum ya kai wa wani chajin wayarsa sai ka ga mutum ya dade da bayar da wayarsa chaji kuma ya tabbar an sa masa a wuta amma kuma kwata - kwata sai kaga dan percentage din daya shiga bai taka kara ya karya ba kuma abun mamaki shine kai zaka dinga tunanin ka dade da kai chajin naka amma kuma ba biyan bukata, ko kuma a,a kama samu chajin amma kuma sai kaga nan danan battery din naka yayi saurin sauka to menene dalilin dake haddasa wannan matsalar ?? dalilan nada dama ga wasu kamar haka,

Rashin kyan chaja: rashin kyau ko kuma rashin sanin chajan daya kamata asama waya yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa wannan matsalar, misali; kamar wayoyi irinsu samsung, lg, htc, da wasu kalar infinix, charger su yana zuwa dabanne da sauran wayoyi zakaga akwai wasu chajan da idan aka sa musu maimakon charge ya qaru sai kaga janyesa yakeyi.

Mutuwar Battery: mutuwar battery yana sa waya ya cika da wuri amma sai kaga ya sauka da wuri saboda lokacin da aka gayyace masa yakare ko kuma ya bacine saboda yawan sawa a wuta ko kuma yawan aiki dashi sosai.

  Hanyoyin magance matsalar

yana da kyau kasan ko ka nemi chajan da kasan tana cikamaka waya da wuri, ka dinga amfani da ita wajen yin chaji, domin kuwa idan ka dage da amfani da ire iren wadannan gurbatattun chajan hakan kan iya haddasa mutuwar battery din wayar naka amfani da waya yayin chaji: babban matsala ne kaga mutum na amfani da waya a lokacin da yake chajinta wasu ma sai kaga har kira sukeyi da wayar a yayin da ake chajinta, hakan ba karamin matsala bane domin kuwa zai haddasa maka mutuwar ko saurin kumbura battery din wayar naka, ire iren hakane sai kaga wayarka ta fara daukar zafi sosai, daganan kuma sai kaji ana cewa wayarka taci ic, ga wanda basu sani bama sai kaji ance wayarka taci battery, idan zaka iya yana da kyau kasa wayarka a flight mode waton alamar jirgi, saboda hakan kan taimaka sosai wajen saurin cikan battery din wayarka, amma sai dai kuma ba halin ka sami damar yin kira ko amsa kira ko kuma yin brawsing da ita  sannan ba ka da damar tura file ta hanyar wifi (flash share, xender) ko kuma ta hanyar blutooth, do nan da nan cikin dan kankanin lokaci wayar naka zata cika,
Tura Zuwa:

Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace

Matsalar Ciwon Sanyi Ga Mace

Wannan yana daya daga cikin manyan matsaloli da mata ke fuskanta ayau, mutane da dama sun bada gudumawar su ta bangaren yadda za’a magance wannan matsalar cikin sauki. 

Haka zalika ana gwada wasu na samun dace wasun kuma ana gwadawa amma har yau dai ba’a dace ba, wasun kuma basu nemi magani ba. Koma dai ta ina matsalar yake insha Allahu yau Duniyan Fasaha zata kawo muku hanya mafi sauki da za’a bi wajen magance wannan matsalar ta hanyar amfani da magungunan musulunci.

     Dalilin daya sa mafi yawancin lokutan muke kawo muku magunguna ta bangaren addinin musulunci ko kuma gargajiya shine sunfi inganci, tasiri da nagarta a kan shina asibiti sabilida wasu lokutan amfani da maganin asibiti mai makon neman lafiya sai kuma a tsokano wani abu Allah ya kiyaye.

Abubuwan da ake bukata

·        Tafarnuwa
·        Garin hulba
·        Bagaruwa
·        Man habbatussauda

* A samo tafarnuwa abare ta sai a dauki daya daga ciki ayi matsi da ita. Idan an wayi gari asamo garin HULBA a tafasata sai ki shiga ki zauna cikin ruwan idan ya dan huce. Ayi haka na tsawon kwana 7 amma shi na tafarnuwa za'a iya yi sau 2 ko 3 ya isa. 


* Dangane da magance ciwon sanyi asamu: hulba, Bagaruwa Da Man habbatussauda. za'a hada bagaruwa da hulba a tafasasu a barsa ya dan huce bayan ya dan huce sai ki zauna a ciki sannan sai ki shafa man habbatussauda. 
Tura Zuwa:

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Tare Da 

Muhammad Abba Gana

A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.

Mafi yawancin wadannan mune wato matasa yan uwana, mukan bata kusan dukkan lokutanmu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo, neman yan mata, karanta littatafan hausa na soyayya ko yaki, neman saurayi, karatun boko, kallon videon kwallo, wakar hausa ko misic da dai makamantansu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mu har ma ya sanya bamu kula da wasu manyan damammaki da zasu iya amfanemu domin samawa kanmu wasu ‘yan kudade na a kasha, wasu lokutan ma har yakan shagaltar damu wajen yin ibada.

A zamanin da muke ciki yanzu mutane sunfi sha’awar aikin gwamnati mutum yana so aji ana cewa ya tafi office ko kuma yana da hadadden office mai dauke da kayan sanyi na zamani sannan kuma a karshen wata yana da wani kayataccen albashi mai tsoka da wannan ake rudan wasu sannan a cusa musu sha’awar shigarta ta ko wacce hanya.

Idan kuma muka maida duba izuwa ga sana’ar hannu zamu ga cewar akwai wasu sana’oi da dama da mutum zayyi wanda zai iya tashi da dubu 5 koma fiye da haka wadda in an kwatanta za’a ga cewa abinda mutum zai samu a karshen wata zai nikka albashir mai aikin gwamnati har sau biyu ko fiye da hakan.

Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yi wani sana’a  kafin ya iya samun kudin da zai siya Data, amma kuma bai san ta yaya zai iya samin kudin a saman yanar gizo (Internet).ta hanyar amfani da datar daya siya. Insha Allahu a wannan makon, Duniyan Fasaha zata kawo muku wadansu cikakkun hanyoyin da za’a iya bi domin neman na kashewa a saman yanar gizo (Internet).

1.==> HADA SHAFUKAN YANAR GIZO: Shafukan yanar gizo abune mai matukar amfani sabili da yana taimakawa wajen bada cikakkiyar bayani game da kasuwanci cikin sauki, A hakikanin gaskiya adadin shafuka a yanar gizo yana ninkuwa a kowace waye war gari, haka kuma adadin masu bukata yana kara bunkasa.

Masana kimiyya sun nuna cewar duk wata kasuwanci da bata hadayya da yanar gizo to hakika ta na rasa wasu damammaki da zata iya samu wajen tafiyar da kasuwancin, haka zalika alamomi sun nuna cewar duk wani kasuwanci da bai da shafi na mussanman a yanar gizo nan da wasu shekaru masu zuwa dole sai ya samo.

            Hada shafin yanar gizo ba kowa zai iya yinta ba sai wadda yake da ilimi sannan kuma yake da basiran yin hakan, akwai mutane da dama wadda suka gwanance wanje suranta shafukan yanar gizo sannan kuma sun dauke ta a matsayin sana’a.

Hada shafi a yanar gizo ba wani abu mai matukar wahala bane sai dai ya zamana dole mutum ya koyi wasu yaruka wadda aka fi sani da ‘programming language’ a turance wadda ita kwanfuta ke fahimta; misali: php, python, JavaScript, ajax, java, Asp.net da dai sauransu.  ko kuma mutum ya koyi yadda ake amfani da wordpress, wix (wadda zanyi jawabin su a wasu makonin masu zuwa) ko kuma blogger wadda nayi jawabinsa a wasu makonni da suka gabata. Koyon daya daga ciki ababen da na lissafo zai bada damar samun makudan kudi a yanar gizo.  

2.==> JAGORA: Wannan wata halattacciyar hanyace da ake samun kudi da ita ta hanyar jawo wani yayi rajista bayan anyi sannan kuma an tabbatar da ingancinsa. A mafi yawanci sa’oi wannan damar yana aiki ne ga manya ko kuma sabobbin shafuka dan samun mabiya da zasu taimaka musu wajen gudanar da kasuwancinsu.

Yadda abun yake anan shine: Bayan anyi ragista da ita kamfani a mafi yawancin lokutan sukan saka wani adadin kudi da mutun zai samu yayin da ya gayyato wani yayi ragista dan taimaka musu wanjen tallar hajarsu. Sukan bawa kowa addireshi na musamman da zaiyi amfani dashi wajen gayyato mutune.

Duk sa’an da wani yayi rajista da wannan addireshin wadda ya basa zai samu ‘yan wasu changi. Inji bahaushe Iya kudinka iya shagalinka haka zalika ‘Yawan mutanen da ka jawo yawan kudin da zaka iya samu’. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada da Konga.com, alibabab.com, Jumia.com.ng, Be With Me Technology, EntireWeb, Renkutten, Yllix, dadai sauransu.

3.==> HADA MANHAJAR WAYA: Adadin mutane dake amfani da wayar salula ya zarce yadda ake tsanmani, sannan adadin yana ninkuwa a kowace wayewar gari.  Wayar salula yakan taimaka matuka wajen sa da zumunta ta hanyoyi daban daban haka zalika adadin mahajar da ake kirkira yana kara ninkuwa a kowace safiya bisa la’akari da yadda mutane ke sa’awar amfani da ita musamman android.

Mutum zai iya hada mahajar waya sannan ya siyar ko kuma za’a iya biyansa ya hada hajar sai dai wannan yana tafiyane hannu riga dana fari dole sai mutum ya koyi wasu yarukan kwanfuta dana ambata a baya kafin cin ma manufa. Amma Alhamdullilahi a yanzu akwai wasu shafukan yanar gizo dake bada damar hada mahajar ba tare da koyon daya daga cikin yarunkan dana ambata a baya ba irin su Androidmob da kuma Appgeyser. Sai dai matsalar wayan nan shafukan basu bada cikkakiyar damar amfani da ita sai an biya wasu kudade.

Lallai ba shakka mutum zai iya samun kudi na hakika da mahajar da ya kirkira ta hanyar saka tallace tallace a ciki, duk sa’ar da wani ya danna wannan tallan zai samu yan wasu changi haka zalika za’a iya biyan mutum makudan kudade dan tallata wata haja kamar yadda zamuyi bayani a gaba.       

4.==> SAKA HOTUNA MAI MOSTI (VIDEO) A YOUTUBE:  Wata hanya da ba kowa ne ya san da ita ba ko kuma yasan amfaninta ba a cikin mutanenmu shine yadda za’a iya samin kude daga YouTube.

Wannan hanya ce mai matukar sauki. Kawai abin da kake bukata shine ka mallaki google account (gmail). Za ran ka mallaki gmail zaka iya zuwa YouTube domin da bude channel.

A cikin wadannan channel din ne zaka rika dora bidiyoyinka. Domin samin kudi a duk lokacin da wani ya kalli wannan bidiyo sai ka tabbatar ka shiga wajen settings kayi checking ko kuma ka zabi monetize, wannan zaya baka damar da zaka sami kudi a duk lokacin da YouTube suka sanya talla a cikin bidiyonka.

5.==> TALLA: Shima wannan wata hanya ce da ake samun kudi a internet ta hanyar yin talla, Duk wani wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu. Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla.

Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafinn. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar da ya kamata.

Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.


Wadanna sune wasu daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su wajen samun kudi a internet, shin ka/ki na da wata hanya da ka/kika sani wanda ban ambata a cikin wannan kasidar ba? Za’a iya turo mana dan dad’awa wanda zai taimaka wa masu ziyara nan gaba. 
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive