Umma Ibrahim Adam, ta ce ta shafe shekaru kimanin 20 tana sana’ar sakar kayan sanyin yara, a wani yunkurin zama mai dogaro da kai tare da kawar da kananan bukatu tun tana kuruciya.
Umma ta bayyana cewa ta koyi harkar saka ne a wajen yayarta tun tana karama, daga bisani ta koma makaranta inda ta karanci harshen Arabic ta kuma sami takardarta ta Diploma.
Ta kara da cewa bayan kammala karatunta ta kuma sami aiki koda shike hakan bai sa ta hakura da sana’arta ta saka ba, a cewarta sana’ar na matukar rufa mata asiri inda take kula da marayun da mijinta ya barta da su.
Daga karshe ta bayyana cewa, bata bada bashi, don haka bata samun matsalolin karya jari ko makancin haka, kuma ta koyawa yara matasa da dama harkar saka duk a yunkurin dogaro da kai.
No comments:
Post a Comment