Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE 3

YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE
YANDA ZAKA SAUKAR DA HOTO MAI MOTSI WATO VIDEO DAGA YOUTUBE ZUWA WAYAN SALULANKA

vidmate yana daya daga cikin manyan application da ake amfani dashi a wayan salula wajen saukar da hoto mai motsi kai tsaye daga youtube, yana da saukin aiki sannan yana dauke da dukkan fasalin da kake bukata, wannan application din za’a iya samun sa kai tsaye wajen saukar da application wato google play store

MATAKAI

1- Saukar a cikin wayanka wato download and install na vidmate ta hanyan latsa nan sai ka bude, da zaran ya kawo zai kaika inzuwa ga gidansa wato home page

2- A sama zaka ga wani akwati inda aka sa wajen dubi wato search sai ka danna
YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE


3- A nan wajen zaka rubuta sunan hoto mai motsi da kake son saukarwa

4- In ka gama rubutawa sai ka latsa ma bullin enter

5- Ka na dannawa zai kaika izuwa ga youtube inda zaka ga hoto mai motsi wato video zaka gansa suran youtube din sai de shi yana dauke da mabullin saukarwa a gefensa wato download button a gefensa.
YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE
6- Sai ka danna ma bullin download wasu lokutan zai sake tambayar ka a wani irin girma kake so ka saukar, anan girman ya banbanta saboda akwai mp4 akwai 3gb akwai kuma mvk banbanci su annan shine shi 3gb bashi da nauyi saide in ka zo kallo zaka samesa bashida haske wanda bazakaji dadin kallo ba amma shi mp4 yafi 3gb ta wajen haske haka kuma ta bangaren nauyi sai de nauyin sa ba zuwa can bane ya dangana da nauyin video ne, shi kuma mvk yana da girma sosai yana da kuma haske sosai yawancinsa ana sawa ne a kaset wato plate na cd amma wanda yafi anan shine mp4 saboda haske wajen kallo.
YADDA AKE SAUKAR DA VIDEO DAGA YOUTUBE


7- Yana kammalawa zaka samesa kai tsaye cikin dakin nuna zane-zane wato gallery ka.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

3 comments:

  1. For newest informɑtion you have to visit web and on web I found this wеb site as a moѕt
    exceⅼlent site for most up-to-date updates.

    ReplyDelete
  2. Wow, that's extremely wonderful I actually have detected a brand new app download apk editor pro this app is nice and that I have started gazing it. Thanks for the assistance and for suggesting the matter I'll travel with it. Keep publication and writing a new article.

    ReplyDelete

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive