Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

MOROCCANS TORTILLA

Girke Girke

Duniyan FAsaha

MOROCCANS TORTILLA

ingredients
Dankali 6
Kwai 4
Albasa
Parsley
Green bell pep
Spices
Seasoning
Mai
Kifin gwangwani

method
 Dafarko zaki fere dankalin ki dafa da Dan gishiri sai ki sauke ki tsane sai ki murjeshi ki ajje a gefe
Sai ki dauko kwano ki fasa kwanki ki zuba maggi,parsley, albasa,curry,onga,kifin gwangwani banda mai din sai ki dauko dankalin nan ki zuba cikin ruwan kwan sai ki juya ya juyu sai ki daura non stick dinki da mai idan yayi zafi sai ki zuba hadinnan ki sa low heat idan yayi sai ki kifa faranti Dan ya dahu ko ina sai ki juya dayan barin shima ya soyuDuniyan Fasaha
Islah tasiu Yau
Mrs jameel

+2349063541142


Tura Zuwa:

potato croquette

Girke Girke

Duniyan Fasaha

potato croquette

Ingredients.
Dankali
Kwai
Madara
Flour
Corn starch
Maggi
Onga
Mai

Method
da farko zaki dafa dankalinki idan ya nuna sai ki bare fatar ki ajje gefe sai ki dauko madara,maggi,thyme,da egg 1,da corn flour sai  ki motsa ki zuba a kan dankalin,idan kinga yayi ruwa zaki Iya qara corn flour, sai ki dinga diba a spoon ko ludayi  kina zubawa cikin ruwan  kwai daban, ki  kina  ajje wa cikin ruwan kwai sai ki saka a cikin corn flour sai ki soya a ruwan mai aci dadi lafi


taku har kullum Mrs jameel

Duniyan Fasaha
ISLAH TASIU YAU
MRS JAMEEL
+2349063541142

Tura Zuwa:

RICE BALL

Duniyan Fasaha


RICE BALL

 ABUBUWAN DA AKE BUKATA

Shinkafar dafawa
Gishiri
Kwai
Man gyada
Nama ja kona kaji
Tattasai
Albasa
Maggi

YADDA ZA A HADA

A wanke shinkafa a zuba cikin ruwan dake tafasa a tukunya. A zuba gishiri daidai, a bar shinkafar ta dahu sosai.

sai ki dauko naman ki,ki tafasa shi da kayan dandano idan ya dafu sai ki daka ki soya
A ajje shi gefe

Sannan a sauke a ajiye ta dan sha iska idan tasha iska  sai a dan bubbugata a fara debo ta da cokali a na sakawa a tafin hannu, a na fadada shi, sannan a na sa hadin nama a tsakiya, idan an saka sai a mulmule shi haka za’a yi ta yi har shinkafar ta kare.

Sannan sai a fasa kwai a cikin roba mai zurfi, a dora mai a kan wuta sai a rika saka dunkulen shinkafar a cikin kwan a motsa shi dan yaji sosai, sai a saka cikin man a soya har sai ya soyu.

 Note:in zakisha wahalar churawa to zaki Iya fasa kwai a ciki ki soya kamar kosai

Duniyan Fasaha
Islah tasiu yau
Mrs jameel luv

+2349063541142Tura Zuwa:

YADDA AKE YIN BINCIKE WATO SEARCH DA GOOGLE SEARCH


Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na Duniyan Fsaha. Insha Allah yau zamuyi bayanine a kan duba abu a google, Ba kawai zaka buɗe shafin google bane ka rubuta suna ko kuma wani abu da kake nema ba, shine kawai hanyar da zaka bi ka yi bincike. Google shine gidan da ya fi ko’ina shahara a internet kasancewar shi daya daga cikin gidajen da suke daukar dawainiyar fito da amsoshin abubuwan da mutane suke nema daga shafukan mutane. Google kamfanine da ya shahara a bakin duk wanda yake amfani da internet, mu samman wanda suke yawan bincike da neman bayanai, amma kuma google ba bincike kawai ake yi a cikin su ba, su na da ayyuka da dama da yake yi, wanda suka hada da kalanda, da akwatin ajiyar imel, dakin ajiyar takardu, youtube, video, biyan kudi wa masu aiki da blog, document, canza harshe, blogger, photos, shopping da dai makamantansu. Abu na farko bincike mai sauki, wanda ku san kowa shi yafi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shine zamu yi dan gyara a kai. Kashi na biyu kuwa zamu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai saukaka matuka da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shine na karshe shi kuma zamu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a duniya baki daya. kamar yadda mafi yawa daga cikin mu suka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son yayi bincike shine ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta www.google.com a wurin da ake rubuta adireshin shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar a cikin browser, da zarar ya rubuta zai bude mishi shafin farko. A dai dai lokacin da mutum ya rubuta abinda yake nema a google, misali ya rubuta Duniyan Fasaha to bayan ya rubuta tambayar shi sannan ya latsa search to ya sani google zai shiga cikin taskar da yake ajiye bayanai na dukkanin shafukan da suke cikin internet a fito da kalmar Fasaha da kuma kalmar Duniyan sannan kuma zai yi kokarin ya fito da in da ya same su a hade. Shi yasa idan mutum ya shiga internet domin yayi bincike kuma ya shiga dakunan bincike irin su google da zarar ya rubuta tambaya sai kawai yaga sakamako a kalla miliyan hamsin, wanda kai da kan ka mai karatu ka sani cewar ba yadda za ayi tambaya daya ace tana da amsa sama da miliyan daya koma ace dukkansu daidai suke. Shi yasa yana da kyau masu karatu su sani cewar ba dukkanin sakamakon da ka yi binciken ta a google ba ne yake zama cikakken amsa ba. Dukkanin wasu kalmomi da ka rubuta cikin dan ramin da google suka bayar a rubuta zai fito maka da amsoshin iya adadin kalman. Misali da mutum zai rubuta how can I write English” to abinda google zai maka shine duk inda aka rubuta kalmar how” a internet zai fito da ita. Haka kalmar can zai fito da dukkanin shafukan da aka rubuta wannan kalmar, haka zai ta fito da ko wane kalma daya bayan daya, sai ka samu amsa sama da miliyan goma amma kuma da wuya ka sani amsa tare da wannan cikakkiyar jumla kamar yadda ka rubuta ta. Da wannan dalili ne yasa su kansu kamfanin google suka fito da wasu hanyoyi da zasu saukakawa masu bincike a yanar gizo wajen samun gamsasshiyar amsa. Sabo da haka, zamu dauki wadannan hanyoyi daya bayan daya muyi bayanai akan su domin mu saukaka muku kuma wajen yin bincike a google.

BINCIKEN JUMLA WATO SENTENCE

Binciken kalma a google kamar yadda nayi bayani a baya kan iya fitowa da sakamako mai yawa wanda kuma basu da dangantaka da abinda ake nema. Amma kuma idan ya zo ta bangaren kasan me kake nema, to, akwai abubuwan da zaka kiyaye wajen binciken. Duk wanda ya san me ya ke nema kamar kana son ka nemi wata jumla a yanar gizo ko kuma wani shugaba yayi wani jawabi kuma ka haddace yadda ya fadi kalmar kuma kana son ka karanta sauran labarin to, google sun bayar da hanyoyin da zaka bi idan ka hada da kalmar da kake bincike zai bada amsarka daidai. Quotation Marks (Baka biyu) “ ” duk wanda zai yi bincike wani abu da yake son gani to sai ya saka shi a cikin baka biyu. Misali “Duniyan Fasaha” ko “Hankali ke gani ba ido ba” saka wadannan tambayoyi a cikin baka biyu zai dawo maka da amsar ka a duk shafukan internet ba tare da ya kakkatse zuwa kalmomin ba. Phrase Connector: sune hyphen ( – ) ko slashes ( / ) ko period ( . ) ko equal signs ( = ) da kuma apostrophes ( ! ) wadannan alamomi su ake kira da phrase connector suma kamar yadda aka yi amfani da baka domin samun ainihin amsa, suma haka ake amfani dasu misalin duniyan-Fasaha ko duniyan.Fasaha ko hankali=ke=gani=ba=ido=ba da sharadin ka da ka bada sarari a tsakanin kowa ne kalma.

AMFANI DA LOKACI

Idan mutum zai binciki wani abu a internet kuma wannan abun ya kunshi lokaci, to, zaka iya yin amfani da abinda ake kira Date Range shi kuwa Date Range ana saka shine a wajen binciken abubuwan da aka san lokacin faruwarsu da kuma ana kokwanton daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza ne abu kaza ya faru. Ko da yake shi amfani da wannan hanyar binciken tana da sharudda wanda sai an kiyaye su kafin a samu amsar da ake nema. Misali wanda yake son yayi binciken abinda ya shafi wani littafi wanda bashi da hakikanin lokacin da aka wallafa wannan littafi amma kuma yasan bai wuce daga shekarar 2014 ba zuwa 2016. To, da farko dole ya rubuta sunan littafin sannan ya rubuta shekarar da yake tunanin itace aka wallafa shi, sannan ya rubuta karshen shekara. Waye Sanadi daterange:2014-01-13..2016-01-13

AMFANI DA KALMOMIN CIKI (METADATA)

Wannan shi kuma tsari ne da kamfanin google suke baiwa masu binciken asalin kalma da ta ta’allaka ga shafu da suke da kalmomin ciki wato metadata, su metadata a takaice wadansu kalmomin da aka saka su a cikin shafukan internet domin saukakawa shi search engine saukin gano shafuka da abubuwan da shafukan suka kunsa. Misali duk lokacin da masu ilimin sanin yadda ake shirya shafukan yanar gizo “web designer” su ka kirkiri shafi to zai rubuta wadansu kalmomi da suke da alaka da wannan labarin da ke cikin wannan shafin. Kamar mutum ya rubuta labari game da computer kuma yayi magana akan abinda ya shafi Microsof Office, to, a wurin da ake rubuta shi metadata sai ya rubuta Kalmar Micrsoft, Windows, Office, Computer da dai wadansu ‘yan kalmomin da yasan mai bincike a internet zai iya rubutawa don neman sani. Wannan shine dailin da ya sa idan mai bincike ya shiga google domin yin bincike idan ya rubuta wata kalma sai yaga wani shafi ya bube amma kuma idan ya duba sama da kasan shafin zai ga babu wannan kalmar a ciki. To ita wannan Kalmar tana boyene a cikin kalmomin ciki “metadata”. To, wanda yake son ya binciki wani shafi amma kuma yana son shi shafin da ya ke binciken ya kasance a cikin sa ya kunshi kalmar kaza to zai iya yin amfani da tsarin metadata wajen yin binciken. Sannan wani Karin haske ma zai kuma iya kididdige lokacin da aka saka wannan bayani desertherald inmeta:modified:2006-01-01..2006-12-31 shima kamar yadda muke gani mun yi amfani da kalmar da muke nema, sai muka saka inmata wanda shi ya ke wakiltar google search engine, sannan kuma sai ka saka Kalmar modified wato lokacin da aka gyara ita waccan kalmar da kake nema, sannan ka saka kwanan wata. Wurin yin amfani da kwanan wata a wurin yin bincike a google mu kiyaye da yadda ake tsara date din, kwanan watan da zaka rubuta na farko dole ya fara da shekara sannan wata sannan rana kamar haka 2006-01-01.

AMFANI DA LAMBOBI:

Mutum na iya binciken abu a google ta hanyar amfani da lambobi wajen bincikensa. A misali mutum yana neman wani abu wanda kudinshi bai wuce kaza ba to zai iya amfani da wannan tsari wajen yin binciken. Phone $40..$90 idan ka rubuta haka to google zai fito maka da wayoyin hannu wanda kudinsu bai gaza dala arba’in ba kuma basu wuce dala casa’in ba.

TACE KALMOMI WAJEN BINCIKE

Wannan bangare kuwa shi zamu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyine da zai bi wajen neman kalma da kuma wata kalmar da ke da dangantaka da kalmar farko, ko kuma ya son yayi binciken kalma amma kuma baya son kalma kaza ta biyo baya, ko kuma ya na son yayi binciken kalma amma kuma ta zo da kalma kaza tare da ita, ko kuma ya binciki kalma kaza amma kuma idan ba a samu wancan kalmar ba to wata kalmar ta zo.
KALMA1 OR KALMA2 (KALMAR FARKO KO KALMA TA BIYU)

Idan mutun na son yayi binciken kalma sannan kuma idan wannan kalmar bata samu ba to a nemo wata kamla sai ka rubuta a cikin ramin google search engine duniya or lahira rubuta kalmar or a tsakanin kalmomin guda biyu shi ke fadawa google cewar a nemo mini kalma kaza ko kuma kalma kaza.


KALMA1 -KALMA2 (KALMAR FARKO BANDA KALMA TA BIYU)

Idan mutum yana son yayi binciken kalma amma kuma baya son ya zama binciken ya hada da kalma kaza to zai rubuta a cikin ramin google search engine misalin Wannan bangare kuwa shi zamu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyine da zai bi wajen duniya -lahira. Yin hakan ka fadawa google cewar ayi maka binciken shafukan da aka samu Kalmar duniya amma kuma kada a samu kalmar lahira a cikin shafin. Amma wurin rubuta wannan hanya mutum sai ya kiyaye kada ya raba lamar ragewa ( – ) da kalma ta biyu.

KALAM1+KALMA2 (KALMAR FARKO TARE DA KALMA TA BIYU)

Idan kuwa mutum na son yayi binciken kalmomi guda biyu lokaci guda, misalin yana son kalmar duniya amma kuma ya kasance an sami kalmar lahira a tare ko kuma a cikin shafi guda to sai ya rubuta kamar haka duniya +lahira wanda ya rubuta haka zai sami sakamakon shafin da aka samu kalmar duniya sannan kuma aka samu kalmar lahira a cikin shafin gaba daya. Shima kamar yadda na sama yake kada ka raba alamar hadawa ( + ) tare da kalmomin da kake bincike.

~KALMA (‘YAN UWAN KALMA)

Idan mutum na son yayi binciken kalma amma kuma yana son a nemo mishi kalmomin da suke da alaka da wannan kalmar to a nan zai saka alamar ( ~ ) a jikin ita kalmar. Misalin idan kana son wadansu kalmomi ne suke da alaka wajen ma’ana tare da kalmar education to sai ka rubuta kamar hama ~education yin hakan zai fito da dukkanin kalmomin da suke da alaka kalamar education wanda a turance ake kira da synonyms.

KALMA -KALMA (‘YAN UWAN KALMA TA FARKO AMMA BANDA KALMA TA BIYU)


Shi kuwa wannan binciken yayi kama da na samanshi, sai dai kuma banbanci tsakaninsu shine wannan kana bukatar a kawo maka kalmomin da suke da alaka da wannan Kalmar amma kuma baka son wanda suke da alaka da kalma ta biyu. Misalin ~examination - assignment wadannan kalmomi ne guda biyu masu alaka da junansu ta wajen ma’ana, to amma kuma idan ka saka irin wannan tambayar za a baka amsa da dukkanin kalmomin da examination yake da shi tare da alakanta kansa da shi, da kuma kin fito da kalmomin da suke da alaka da assignment. Wadannan sune a takaice abun da za mu iya baku wadanda suke shafi yin bincike tare da google search engine, Da fatar za a kasance tare da mu a darasi na gaba. Ga neman karin bayana ko tambaya zai iya aiko da ita kai tsaye zuwa ga: [email protected] ko kuma ta hanyan turo da tsako 09039016969.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Beans Buns

Duniyan FAsaha
Beans Buns
Ingredients

Wake
Kwai
Garin bread
Nikakken nama
Magi,gishiri
Curry
Albasa
Mai
Tafarnuwa

YADDA AKE
Ki samu waken ki me kyau mara kwari ki
gyarashi,sai ki surfashi ki wanke ki fidda
hanncinsa tas,sai ki dora ruwa a tukunya kisa
waken ki dafa shi, sai yayi laushi,amma ba
tubus ba,sai ki sauke,
dama kin tafasa namanki da albasa da magi
da tafarnuwa,kin dakashi,sai ki soyashi sama
sama,karki bari ya kandare,
sai ki dauko wannan waken ki tukeshi kamar
tuwo,kisa magi da gishiri a ciki idan kina
bukatar curry sai kisa a ciki ki cakuda,
sai ki dinga diba kina sa naman a tsakiya kina
curashi kamar ball kina barbadeshi da garin
bread kina ajewa har ki gama,
san nan ki fasa kwai kisa magi ki kada ki dinga
dauka kina soyawa a mai me zafi,
ki gwada yana da dadin ci kuma ga kamshi
daga nesa.

Wow baa bawa mai rowa
Matan gida muna jiran ganin pics

Duniyan Fasaha

ISLAH TASIU YAU
MRS JAMEEL
+2349063541142
Tura Zuwa:

HUSBAND GIFT

Duniyan Fasaha

HUSBAND GIFT

Ingredients
Fulawa
Albasa
Attarugu
Thyme
Nikakken Nama
Butter
Maggi & gishiri
Mai & Baking powder
Zaren dinki sabo

Method
Idan kika kwaba fulawarki da baking powdered
da butter, sai kiyi kwabin kamar na meat pie
daganan saiki dora nikakken naman ki da
albasa ki soyashi sama-sama sanna saiki
murza fulawa ki yankata a square for angle
size,saiki dauko wan an naman kisaka a
tsakiya kikamo gefe da gefe duka guri hudun
saikisa zare ki daure kisan acikin oven ki gasa
zakiga yayi kyau saman kullin zai bude . Aci lfy

Tura Zuwa:

SARKIN DADI

Duniyan Fasaha


SARKIN DADI

....................
Ingredients

Nama
Kwai
Fulawa
Dankali
Albasa,attaruhu
Tumatur
Tafarnuwa
Tsinken sakace
Maggi&Gishiri
Kara's
Mai

Method

zaki samu namanki mai kyau mara kitse ki
wanke ki yanka kanana ki jajjaga attaruhu ki
zuba akai sai ki zuba dakakkiyar tafarnuwa da
curry kisa magi da gishiri ki dora akan wuta
yayi ta dahuwa har ruwan ya kone san nan
kuma ya dahu.
ki dafa dankali ki yankashi shima a kwance da
dan tudu sai ki yanka tumatur shima a slice ki
yanka albasa,
sai ki dauko dankali ki soka a jikin tsinken
sakace yaje karshe sai ki saka nama shima sai
ki soka tumatur sai ki kuma soka nama ki sa
karas sai ki kuma saka nama sai ki aje,haka
zakiyi harki gama.
sai ki fasa kwai ki kadashi idan 4 ne sai ki zuba
fulawa cokali 3 kisa magi ki juya sosai,sai ki
dora mai akan wuta ki dauko wannan hadin da
kika jera a hankali ki saka a cikin kwan nan ki
juya ko ina ya samu sai ki soya ki barshi yayi ja
har ki gama.

Duniyan Fasaha
Islah tasiu Yau
Mrs jameel

+2349063541142
Tura Zuwa:

MUHIMMAN SHAWARWARI BAKWAI (7) GA MASU AMFANI DA BLOGAssalamu Alaikum, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. insha Allah yau zan bada wasu shawarwari wa masu rubutun ra'ayin kansu ta hanyan ranar gizo wato blog. zama daya daga cikin gwanayen rubutun ra'ayin ka ta hanyan yanar gizo wato blog ba karamin aiki bane, abu na farko mai dadi shine kasancewar kaine shugaba, wanda ke nufin ba zama daga safe zuwa dare ba, zakayi duk abun san ranka zaka kuma sa abun san ranka, son zama daya daga cikin jerin sunan masana kuma gwanaye wajen yanar gizo wanda ke dauke da wasu matsaloli da dama, musamman in kana tafiyar da komai da kanka na tsawon lokaci, yana da kyau ka fita dan ganawa da mutane, zaka iya hakan ne ta hanyan:-

1- Aiki a cafe
2- Halartan taron kara wa juna sani
3- Halartan taron sadarwa na kwanfuta koh na zamani

Ayan anan shine kada ka bari yancin rubutun ra'ayinka a yanar gizo ya zama maki yinka, insha Allah yau zan zayyano hanyoyin da na bi dan gujewa hawan jinin rubutun yanar gizo, yana da matukar amfani musamman a wannan zamanin namu na fasaha.

ABU NA FARKO

Daukan hutu a ayyukan yau da kullum
Daukan hutu a tsakin aiyuka yana da matukar amfani dan taimakawa ido daga hasken wutan kwanfuta koh na wayan salula, yana taimakawa wajen kore gajiyan kwakwalwa yana kuma taimawa wajen samar da karfin gwiwa dan karasa aiki daya rage misali daukan hutun minti hudu na tsawon aikin minti talatin. kada kayi kokarin cigaba da aiki sosai yana haifar da wasu matsaloli.

ABU NA BIYU

Yin aiki a wada taccen wutan lantarki

mafi yawancin masu rubutun ra'ayin kan su wato blog suna watsi da yanayin hasken wutan lantarki, wadun su sukanyi aiki a wurin da babu haske wanda hakan ba karamin illa yake kawo wa lafiyan idanunmu ba, hasken wutan kwanfuta koh wayan salula ba karamin illa yake kawo wa lafiyarmu ba, kayi kokarin daidai ta hasken wutan kwanfutanka dana dakinka sannan kayi kokarin bude tagogi dake cikin dakin.

ABU NA UKU

Kibta idanu

kayi kokarin yawai ta kibta idanu domin yawai ta aiki na tsawon awa goma 10 koh sama da haka yana kawo rashin ruwa a cikin idanu, yawan kibta su yana mayar dasu mazauninsu na da. masana sunyi ittikafin cewar yawai ta kibta idanu yana taimakawa ido sosai wajen aiki.

ABU NA HUDU

Zaban kayataccen wajen aiki

in kana aiki a offishi shine waje mafi inganci dan aiki saboda bazaka fuskanci wani matsala ba saboda an kayyadesa ne dan aiki. amma in kana aiki a gida yana da kyau ka kayyace wajen aiki, ka nisanci kanka daga yara kana’na da wasu ayyukan gida wanda zai na dauke ma tunani.

ABU NA BIYAR

Cire abun daukan hankali
kada ka hada ayyukan gida da na ayyukan yanar gizon ka sannan kayi kokarin cire duk wani abu da zai katse ka ko ya dauke maka tunaninka a yayin da kake aiki.

ABU NA SHIDA

Ka samar da allon rubutu
ka samar da allon rubutu a dakin ka dan zayyo shirin abubuwa da zakayi gaba, ka rubuta duk abubuwan da kake so kayi a cikin satin nan koma watan gaba daya, ka dage wajen lissafo abubuwan da zakacinma a cikin mako.
ABU NA BAKWAI WANDA SHINE NA KARSHE
KA NESANTA DA WAYAR SALULANKA

wannan yana daya daga cikin abu mafi muhimmanci a lokacin da kake yanayin rubutu, karan kiran waya koh alamar shigowar sako zai iya yanke ma tunani ko hankali abu mafi muhimmanci da nakeyi yayinda nake amfani dashi koh kuma amfani da kwanfuta shine katse layuka na, duk da cewar yana da amfani ya kasance a kunne amma kasancewar koda yaushe muna nan a kan chatting zai iya daukan hankali.


Wayannan sune wasu daga cikin shawarwari ga masu rubutun ra'yin kansu ta hanyar yanar gizo wato blog. Yanzu lokacinka ne, in kana so kayi kari a kan shawarwarin dana bayar zaka iya rubutawa a akwatin nuna ra'ayi wato comment box.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

SHORT BREADDuniyan Fasaha

 
SHORT BREAD

KAYAN HADI
Flour
Butter
Madara
Sugar
Vanilla flavour

METHOD

Firstly Zaki sa butter da suga kiyi mixing ki buga har
sai kin daina jin karar sugar sai kisa madarar ki
na gari sai flour kiyi mixing din su da dan karfi
sai kisa a fridge yayi 30 minute zuwa 1 hours
sai ki fitar kiyi shaping din shi kiyi  amfani da fork
kiyi ramikan sai ki gasa na 10 to 15 minute

Duniyan Fasaha
Islah tasiu yau
Mrs jameel luv
+2349063541142
Tura Zuwa:

kubewar Senegalese
kubewar Senegalese

Ingredients

kubewa danya me kyau
fry fish
meat na rago
gyada nikakkiya amma a soye
 kayan miyan ki tomato 2
galic da masoro
 manja ko na gyada
daddawa
Maggi da onga

Method
Zaki yanka kubewar ki round shape meaning kiyi slicing nata, ki dauko kayan miyanki ki jajjaga ki ajje gefe ki dauko nama ki wanke ki Dora a wuta ki zuba maggi da gishiri,albasa da dan ruwa kadan inyayi sai ki sauke ki zuba a kwano daban

Ki dauko tukunyar ki ki zuba mai ja ko fari ki zuba dakakkiyar albasa da tafarnuwa da citta in sun soyu ba konewa ba sai ki zuba kayam miyar ki ki soyu sosai sai ki zuba ruwan naman nan ki dauko daddawa ki zuba gyadar ki dai dai misali sai ki barta har warin gyadar ya futa sai ki dai daita ruwan miyan iya adadin yawan da kike so
Sai ki kawo spices naki ki zuba

Dama kin gyra kifinki kinsahi a ruwan zafi saboda datti kin wanke sai ki zuba
Sai ki zuba kubewar in ya tafasa da yar kanwa shikenan sai ki rufe ta danyi

note
Baa birge kubewar fa saboda shape nata ya futo


Taku har kullum mum amjad
aci dadi lafiya
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive