Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Gyaran gaba (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakeken gaba. (Matsi)

Ana so uwar gida ta kula da gabanta musamman ga wacce tayi sabon haihuwa. Barin gaba (farji) ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen mai gida, uwar gida kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi. Masana ilimin kiwon lafia da jima'i sun ce duk lokacin da aka yi jima’i da mace farjin ta yana kara fadi shi kuma azzakarin mai gida yana rage girma. To kinga nasa na rage girma na ki kuma yana kara fadi, rashin kula da kuma neman mafita a hakan yasa maza da dama suke ganin matayensu a matsayin tsofaffi ta bangaren jima'i. Haka kuma kema uwar-gida rashin kula daga wajen maigidan naki takansa kema ba kya jin gamsuwa sosai a duk lokacin da kuka gabatar da ibadan aure (jima'i) Don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin ya za ma rago. Kuma ba kowane namiji ba ne zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba hakama ba kowace mata bace zata iya gayawa maigidanta ba rashin gamsuwar ta ba. Don haka uwargida da maigida sai mu kula.
Ga wannan hadi ga uwar gidan:-
·        Farar albasa
·        Kanunfari
·        Citta
·        Balmo
·        Barkono
·        Rihatul hulbi.

Sai ki hada su waje daya ki mayar da su kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum. Insha Allahu Uwargida da maigida zakusha mamaki, domin kuwa gabanki zai cike yayi cif-cif kuma zaki dawo tamkar sabuwar budurwa ga maigidanki.

Bayan haka ma, za ki iya samun zogale mai kyau sosai, amma danyen ganyen, ki wanke sosai, ki sa a Blender, ki markade shi, har sai ya yi laushi, har ki ga yana yauki, sannan ki tace shi sosai. Bayan kin tace ruwan, sai kuma ki nemo madarar gwangwani na ruwa, misali irin madarar PEAK (na ruwa), ki juye a ciki, ki dan saka zuma, haka za ki rika sha a kai a kai. a kai a kai.
Maigida ma za ki iya masa hadi:-
·        Muruci
·        Saiwar haukufa
·        Namijin goro
·        Hanno
·        Rihatul hubbi
Sai ki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau ana sha. Sannan ku nemi dabino a daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.
Insha Allah za a samu biyan bukata. Allah ya taimake mu amin.




mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive