Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za a samu fata mai haske

Yadda za a samu fata mai haske

Yadda za a samu fata mai haske

Mata da dama na sha’awar samun fata mai haske kuma mai sheki. Gaskiyar magana ita ce, ba zai yiwu mace ta dada haske a cikin kwana daya ba. Amma akwai abubuwan da za ta yi domin samun irin wannan launin fatar da take so. Don haka ne a yau na kawo muku irin abubuwan da za a yi domin samun fata mai haske kuma mai sheki daga dakin girkin uwargida ba sai an je kasuwa ko manyan shagunan sayar da kayan kwalliya ba.

==> Kurkum: yana dauke da sinadaran haskaka fata da kuma warkar da tabon fuska. Yana da kyau a kasance tare da shi. A samo zuma cokali biyu sannan a kwaba da garin kurkum sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna talatin a kullum kafin a shiga wanka. Yana dada wa fatar jiki haske.


==> Timatur: yana dauke da sinadarin ‘lycopene’ wanda ke taimakawa wajen haskaka fata. Idan har ana so a dada haske a sati daya, sai a markada timatur sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a shafa a fuska da wuya a kullum na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.

==> Ruwan ‘rose’: idan ana son amfani da wannan hanyar don dada hasken fuska, sai a rika diga shi a cikin man shafawa, yana sanya fata laushi da kuma haske. Ko kuma a samu garin alkama sannan a kwaba da ruwan ‘rose’ sannan a shafa a fuska da wuya na tsawon mintuna 20 kafin a wanke.


==> Zuma da lemun tsami: wadannan ababen na saurin sanya fata yin haske da kuma sheki. A samu zuma da lemun tsami sannan a kwaba su a rika shafawa a fatar fuska da jiki sannan a barshi na tsawon mintuna 30 sannan a wanke kamar sau biyu a rana safe da yamma.
==> Kurkum da madara: a kwaba garin kurkum da madara sannan a shafa a fuska a kwana da shi. Washegari a wanke. Yana sanya fuska haske da kuma sheki.

==> Fiya da gurji: a markada fiya da gurji sannan a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna 30 a kullum kafin a wanke. Yana sanya haske da kuma shekin fata.

Masu karatu su gane cewa a cikin ababen da na lissafo, guda daya yakamata mutum ya yi amfani da shi domin samun sakamako mai kyau. Amfani da su duka a lokaci daya na haifar da kurajen fuska.

Tura Zuwa:

Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna


Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna
A kowani waye wan gari sababbain dabaru na fasaha ake kirkira daga kwararru a bangare daban daban dake fadin duniya A wannan zamani da muka tsinci kanmu, wanda za’a iya samun dukkanin wani bayani da ake bukata a yanar gizo, yanar gizo yana girma fiye da yanda muke tsanmani idan muka kai duba izuwa ga tura sako zamanin baya kafin ka tura ma mutuum sako sai ka biya wani ya kai ko kuma kaje da kanka amma yanzu da zuwar yanar gizo zaka iya turama mutum sako cikin yan dakikai a kuma a farashin da bai taka kara ya karya ba, a lokutanmu na yanzu in zaka tura sako daya shafi bangaren rubutu yana da kyau ya kasance kana da abu wanda ake kira da suna “Email”.
Sannan Akwai abubuwa da dama da ba za’a iya cin moriyarsu ba idan babu Email. Misali yanzu Kama daga rajistan makaranta, neman aiki, rajista a wani shafin yanar gizo domin samun bayanai kai tsaye, ko rajista a kafafan sada zumunta, babu abun da za’a iya yi a yau idan babu Email. Kai ko wayarka ta android na bukatar Gmail domin ta yi maka aiki yadda ya kamata. A takaice dai rashin Email ga mutum a wannan zamani mummunan hatsari ne. Amma abun mamaki shine, da yawa a cikin hausawa har yanzu ba su rungumi wannan dama ba wacce intanet ta kawo mana. Wadanda ke da Email din ma tuni sun manta da number sirrinsu ‘password’ domin ba sa amfani da shi.
A dan haka ne aka bar mu a baya sosai kuma ci gabanmu ke ta yar hawainiya idan aka kwatanta ta da ci gaban da sauran duniya ke samu. Lokaci ya yi da ya kamata mu sauya hakan. Abun dadin shine; bude Email yana da matukar sauki kuma ba’a bukatar sisinka:

GA BAYANI DALLA DALLA

Email dai wani na’urane da aka kirkiresa dan taimakawa mutane wajen tafiyar da al’amuransu na yau da kullum akwai email kala kala ma’ana akwai kamfanoni dayewa wayen da suka bude nasu amma dai duk aiki daya suke sunansu kadai ya banbanta. Akwai Yahoo mail, akwai Gmail, Akwai rocket mail akwai Hotmail akwai Naij mail da sauransu gabadayansu sunansu email amma kamar yanda na liissafa wasu ko wani kamfani da Sunanda suke aiki dashi duk kuma aiki daya sukeyi. Amma gaskiya bisa fahimta ta a cikinsu dukka Gmail yafi su sauki yafisu girma yafi su tsaro saboda mallakar babban kamfanin nan ne wato Google kuma sun mamaye ko ina. Abunda yasa nace yafiso tsaro duk lokacin da aka bude kanfani ana samun tsagerun da suke lalata kayan na’ura ta hanyar canza musu tunani  ko kuma cire ko goge kayan mutane a yanar gizo amma tun kafuwar kamfanin nan na Google har izuwa yau da nake Magana ba’a taba goge ko cire kayan da google ya kirkira ba ba’a ma haifi wanda zai taba kayansu ba a takaice kenan.


 Sannan amfanin Gmail ya zo ya kere sauran ‘yan uwansa da nisa. Misali idan kana da Gmail, za ka iya ajiye dukkanin hotunanka da bidiyo da wakokin a yanar gizo yadda ba za su taba bata ba har abada. Bayan haka, gmail ka ke bukata ka yi rajista a Youtube kuma ka samu damar shiga Google play store na wayar ka ta Android dan saukar da application, da dai sauransu. Saboda haka na yanke shawaran nuna muku yanda ake bude Email Da Gmail in dai ka gane wannan zaka iya bude na kowani kamfani:

Matakai
=>Bude browser din ka ta OPera mini, UC browser ko Chrome ko FireFox ka rubuta www.gmail.com a akwatin rubutu kamar haka
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

=> Za ka ziyarci wannan shafin a kasa. zaka ga inda aka rubuta “create new account” kamar yadda kwarin ya nuna sai ka danna kai din.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

=>Daga nan zai kai ka shafin da za’a tambayeka number wayar ka sai ka sa wanda kake amfani dashi kada kasa number da baya kusa da kai saboda za,a turo ma sako kai tsaye, 

Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna


bayan kasa zaka samu sako ta akwatin wayarka wato sms wanda zaka ga an rubuta “Goto https://g.co” da wasu tarkacen sai ka danna kai din zai kaika izuwa ga wani shafi.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

==> za,a tambayeka ta cika wani form kafin ka wuce gaba sai kayi hakan ta hanyar shigar da abunda ake nema daidai kamar haka

=> Inda aka rubuta ‘First Name’, rubuta sunan ka/ki cikakke. Inda aka rubuta ‘last Name’, rubuta sunan mahaifinka sai Ka sauko kasa inda aka rubuta ‘Date of Birth’ ka zabi watan haihuwar ka sannan ranar da aka haifeka sai shekaran haihuwar ka dukka ta hanyar rubuta su da lambar Idan ba’a san ranar haihuwa ba, za’a iya rubuta koma me. Amma shekarun su zama daidai. Idan shekarun ma ba’a sani ba, a kiyasta dai dai misali. sai kuma nagaba shine ‘Gender’ ma’anarsa jinsi in kai na miji ne sai ka zabi ‘Male’ in kuma ke na mace ce sai ki zabi ‘Female’ daga nan sai a danna in da aka rubuta ‘Next’  
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

 zai kai ka izuwa ga wani shafi inda za’a umurce ka da ka zabi ‘Username’ ka rubuta lakani, duk abin da ka rubuta a nan shi zai zama Email Din ka. Misali idan ka rubuta afreen, Email dinka zai zama [email protected] sai a latsa ma bullin “Select” in dai kaga ya rubuta wata alama mai dauke da jan cala toh wannan bazzyi ba sai ka sake sa wani, ba lallai ne sunan da ka sa da fari yayi ba zayyu wani ya taba dudewa dashi in har hakan ya kasance sai ka sake zaban wani ko kuma ta hanyar sa masa wasu lambobi a gaban ko bayan misali [email protected] Ya  kamata gaskiya mutum ya yi amfani da sunan shi gaba daya ko kuma a kiyasce. Idan an rigaya an dauki sunan ka, zaka ga sun baka zabi dauke da sunan an kara lambobi a karshe.
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna
 
==> in har ka samu wanda yake aiki bayan ka danna ma bullin ‘select’ zai kai ka izuwa ga wani shafi inda za’a umurce ka sa lambar tsaro wato “password” sai kayi hakan tare da maimaita abunda ka sa da fari a akwati na biyu inda a rubuce “Confirm Your password” a nan sai a zabi password mai kyau wanda ba za’a yi saurin mantawa ba. A tabbata abu ne da za’a iya tunawa duk daren dadewa. sannan sai ka danna inda aka rubuta “Finish”. 
Yadda Ake Bude Email: Bayani Dalla Dalla Dauke Da Hotuna

Shikenan an gama. Yanzu idan ka ziyarci adireshin www.gmail.com, zai bude maka wannan akwati

Sai ka rubuta Email din da ka zaba, da password, ka danna dan akwatin nan har sai ka ga wannan dan alamar ta ‘good’ sai ka danna inda aka rubuta ‘sign in’. Duk wanda ka baiwa Email dinka ya turo sako, to zaka ganshi a nan, haka zalika zaka iya samun sako daga shafunan yanar gizo idan ka yi rajista da su. Bayan haka, kaima kuma za ka iya tura sako ga wasu Email din. Idan da wata tambaya, za’a iya rubutawa a kasa.
Tura Zuwa:

Hanyoyin kula da jiki


Hanyoyin kula da jiki

Hanyoyin kula da jiki

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku daga mujallar Duniyar fasaha, insha Allahu yau zamu yi baya nine a kan Hanyoyin kula da jiki, Gangar jikinmu abu ne da yakamata mu rika kula da shi domin kare lafiya da kuma jin dadinmu.. In ba haka ba za a iya haduwa da cututtuka da dama. Mata musamman wadanda suka haihu yakamata su san yadda za su rika kula da jikinsu haka kuma idan suna da sabon ciki akwai abubuwan da za su yi domin rage harar da duk abin da suka ci. Wasu na da yawan gumi, wasu kuma warin jiki, bushewar lebe, zanen ciki, kodewar fata saboda rana da su da dai sauransu. A yau mun kawo muku hanyoyin da za a bi domin magance wadannan matsalolin.

==> Yawan gumi: a samu ruwan amfuna da zuma a zuba a ruwa a kasance ana sha a kullum domin rage yawan gumi. Ko kuma a hada garin ‘baking soda’ da man zaitun da ruwa a kwaba sannan a rika shafawa a inda gumin ke yawan fita. Yawan shan bakin shayi da lemun tsami da man kwakwa na rage fitowar gumi a jiki.

==> Warin jiki: idan ka kasance mai warin jiki za a iya hada garin ‘baking soda’ da ruwan lemun tsami a kwaba sannan a shafa a hammata da wuraren da ke yawan wari a jiki na tsawon mintuna biyar sannan a yi wanka.

==> Mace mai juna biyu: gari na wayewa ta sha ruwa kofi daya kafin komai. Ta samu citta ta markadata sannan ta zuba ruwa ta dora a wuta ya tafasa na tsawon mintuna goma sannan tat ace a zuba zuma ta sha a kalla kofi biyu kullum da safe.

==> Kodewar fata saboda rana: za a iya samo ganyen ‘aloe bera’ a matse ruwan a inda kunar ta shafa na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke. Ko kuma a samu madarar gari da zuma a kwaba a shafa a wajen kunar na tsawon awanni biyu kafin a shiga wanka.


==> Zanen ciki (Stretch marks): wannan irin zane na bayyana ne a jikin mace sakamakon cikin da ta dauka. Bayan ta haihu wasu ba su san yadda za su magance wadannan matsaloli ba. A samu ruwan kwai sannan a shafa a zanen daya bayanan, a rika shafawa a ciki da cinya da sauransu. A jira ruwan kwan ya bushe kafin a wanke. Za a rika yin haka ne a kullum.

==> Yawan bushewar lebe: a samu man ‘glycerin’ da lemun tsami sannan a kwaba sannan a shafa a lebe kullum da dare kafin a kwanta barci. Yin hakan zai sa a samu lebe ya yi santsi da kuma laushi.
Tura Zuwa:

Amfanin kwai wajen magance kurajen fuska

Amfanin kwai wajen magance kurajen fuska

Amfanin kwai wajen magance kurajen fuska

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu insha Allah yau zaku koyi yanda ake amfani da kwai wajen magance kurajen fuska, a hakikanin gaskiya kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuska. Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.


Ababen da za a bukata:

Kwanuka biyu
kwai daya
Takardar ‘tissue’ daya

Amfanin kwai ga fuska:
·        Ruwan kwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma ‘minerals’
·        Yana kare fuska daga kuraje.
·        Yana kuma rage tsufar fuska.
·        kara wa fuska haske.
·        Rage kumburin ido.

A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.

Hadi:
A fasa kwai sai a cire gwaiduwar. A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.  Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.

A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu.  A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan? Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska. Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar. Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.
Tura Zuwa:

Soyayyen dankali da nama da kabeji

Soyayyen dankali da nama da kabeji

Soyayyen dankali da nama da kabeji
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Allah Ya fiddamu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka soyayyen dankalin turawa da nama da kabeji domin samun abun karyawa. Akwai ababe da dama wadanda za’a iya karyawa dasu. Yana da kyau a rika sauya girki daban-daban domin kada ya ginshi mutanen gidan. Shi dai wannan girkin ba daurasu akan wuta gaba daya ake ba. Daban ake yinsu sannan a sanyasu a wuri daya domin su kara dadi a lokacin karyawa.


Abubuwan da ake bukata

·        Dankalin turawa
·        Nama
·        kwai
·        Tumatir
·        Kabeji
·        Bama
·        Magi
·        Garin tafarnuwa
·        Man gyada
Hadi

A samu dankalin turawa sannan a fere shi ba tare da daddatsa shi ba sannan a wanke a ajiye a gefe. A tafasa dankalin da ruwa da gishiri kadan sannan a tsame. A fasa kwai kamar uku sannan a zuba magi da yankakkiyar albasa kanana sosai da garin kori da na tafarnuwa domin cire karnin kwan. A daura tukunya a zuba man gyada har sai tayi zafi sannan a dauko dankali ana tsomawa a kwai ana jefawa a mangyada. Haka za a rika yi har sai sun soyu. Sannan a kwashe a zuba a rufe a kwano mai murfi.

 A tafasa nama da magi da gishiri da garin tafarnuwa da na kori sannan a yayyanka mishi albasa har sai yayi laushi sosai ruwan ya kusa tsotsewa sannan a sake yayyanka albasa da timatir a zuba da man gyada kadan ayi ta gaurayawa akan wuta har sai albasar da timatir din sun nuna. Sai a kwashe a ajiye a gefe. A samu kabeji a yayyanka shi kanana sannan a tafasa kwai kamar uku a yayyanka da dan girma a ciki sannan a sami bama da magi kadan a zuba a gauraya. A samu kwano a zuba soyayyen dankalin a gefe, hadin nama a wani gefen sannan hadin kabeji a wani gefen. Za’a iya hada wannan kayan karyawan da bakin shayi ko kuma mai kauri. A ci dadi lafiya!
Tura Zuwa:

Yadda ake yin mashe- Girke Girke


Yadda ake yin mashe- Girke Girke

Assalamu Alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau mun kawo muku yadda ake yin mashe. Mashe abinci ne mai kama da masa amma ya fi masar kankanta sannan abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa shi daban yake da na masa ko waina. An fi cin wannan irin abincin ne a kasar Hausawa domin karyawa da safe. Sannan mafi yawanci sun fi son cin sa da yajin kuli-kuli ko kuma yajin barkono. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da ake bukata


Ø  Garin gero
Ø  Man gyada
Ø  Magi
Ø  Yis
Ø  Flawa
Ø  Gishiri
Ø  kuli/yaji

Hadi

A samu gero sannan a wanke a cire tsakuwa a busar sannan a kai a nika ba tare da an saka kayan kamshi ba ko kayan yaji. Bayan haka, sai a tankade wannan garin sannan a sa a roba sai a samu garin flawa a zuba a ciki a gauraya su gaurayu sosai. A duma ruwa sannan a zuba yis a ciki idan ya dan tashi, sai a zuba a cikin hadin garin gero da flawa. A samu ruwa ana zubawa ana kwaba hadin har sai ya yi kauri kadan. Hadin ya kasance ba mai kauri sosai ba sannan a rufe a sanya a rana har sai kullun ya tashi.

Sannan a dora tukunyar tuya a wuta a zuba man gyada da albasa su soyu. Sai a dauko kullun ana yankawa da ludayi ko cokali daidai girman da ake so ana soyawa kamar yadda ake tuyar fanke sannan a kwashe. A samu yajin kuli mai dauke da magi a ci da shi ko kuma yaji mai dauke da magi ana dangwalawa ana ci.

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive