Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Gudun Auren Dole, Yasani Shiga Duniya.

Gudun Auren Dole, Yasani Shiga Duniya.

Kakata ce ta kore ni daga gida, ba tare da dalili ba, hakan ya tilasta min barin gida da neman mafaka inji matashiya Bushira.
Wani labarin na nuni da cewar, mahaifin yarinyar Bushira yana son aurar da ita, amma Bushira bata son auren da ake son yi mata, hakan ne ma ya sa mahaifin nata ya dauketa ya kuma kai ta gidan kakarta.
Ta ce kwatsam wata rana kakar ta, ta hada mata kayayyakin ta inda ta koreta, bayan fitowarta daga gida ne ta hadu da wasu matasa, inda suka bata mafaka.
Wusa matasan da suka dauki wannan yariya, suke kuma aikata badala da ita, sun bayyana yadda akayi suka hadu da ita, inda kowannen ke bayyan halin da ya hadu da ita, daya daga cikin su dai na cewa ya hadu da ita ne a kasuwa, inda ta nemi ya bata lambar wayar shi
Shi kuwa dayan cewa yayi ta zo ta ce mishi ita daliba ce, kuma tana neman masauki. Samarin dai sun bayynar da irin alakar da ta shiga tsakanin su da yarinyar.
A bayanin shi kuma, mataimakin kwamadan Hisbah, akan ayyuka na mussaman Barister Nabahani Usman, yace muddin aka kama matasan da laifi lallai zasu fuskancin hukuma.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Fiddausi Lawal; Babu Nakasasshe Sai Kasasshe

Fiddausi Lawal; Babu Nakasasshe Sai Kasasshe

Masu iya Magana kan ce babu nakasasshe sai kasasshe, Fiddausi Lawal, wata mai bukata ta mussamam ta ce ta fara fuskantar matsalolin rayuwa tun tana makarantar firamare.
A sanadiyyar matsalar da take tattare da ita, Fiddausi bata samun damar lokacin hutun cin abinci da ake badawa a makaranta a okaci guda tare da na ragowar 'yan makaranta.
Hakan bai karya mata gwiwa wjan ci gaba da karatu ba, ta kara da cewa bayyan kammala karatun sakandire, ta jajirce akan ra'ayinta na ci gaba da karatu duk kuwa da cewa ta fuskanci matsaloli da dama inda wasu daga cikin malamanta ma, basa saurara mata baya ga dawainiyar da wasu daga cikin dalibai ke yi na jigila da ita.
Malama Fiddausi, ta kara da cewa a mafi yawan lokuta mutane hudu ne dawainiyar daukanta domin hawa da sauka daga bene a makaranta. A cewarta, yayin da take makaranta ba ta da wata hanya ta mussamam domin samun taimako irin na masu bukata ta mussamam.
Fiddausi ta ce duk da bukata ta mussamam da Allah ya nufe ta da ita, hakan bai hana mata karasa karatunta ba domin kuwa a yanzu tana da digirinta na biyu kuma a yanzu ma ta samu gurbin aiki a ofishin babban akanta na kasa baiki daya.
Tura Zuwa:

Jajircewa Da Mayar Da Hankali Wajan Aiki Na Kai Mutum Ga Wani Matsayi- Amina Dogonyaro

Jajircewa Da Mayar Da Hankali Wajan Aiki Na Kai Mutum Ga Wani Matsayi- Amina Dogonyaro
A shirinmu na wasu muhimman mata da suka taka rawa a al’ummarsu a wannan karon mun sami bakuncin Amina Dogonyaro, ma’aikaciya a NTA, wacce ta ce ta fara aiki ne a bangaren banki, bayan ta kammala yiwa kasa hidima, daga bisani ta koma ga aikin jarida.
Ta ce tun da fari dai ta so ta zama lauya ne inda ta sami gurbin aiki a wajen Kana imahaifiyarta ta ce lallai ba zata yi nisa da gida ba.
Amina dogonyaro, ta bayyana cewa da farko ta fuskanci kalubale da dama musamman ganin yadda ta sami kanta cikin aikin jarida, koda shike daga bisani ta lura cewar abinda kawai take bukata shine mayar da hanakli da jajricewa kuma tabbas hakanta ya cimma ruwa.
Daga karshe malama Amina ta bayyana cewa gidan Talabijin din data fara aiki ya fara sa wasu daga cikin shirye shiryen ta wadanda suka sami karbuwa irinsu In-baku-ba-gida da sauransu.
Tura Zuwa:

Sabuwar Manhaja Da Yara Zasu Iya Koyar Da Kansu, Batare Da Zuwa Makaranta Ba

Wai kuwa yara da basu taba zuwa makaranta ba, na iya koyar da kansu yadda ake rubutu da karatu, daga kawai sun samu na’urar kwamfuta? Wata tambaya da wata kungiya mai yunkurin ilmantar da duniya tayi ke nan.
Kungiyar ‘Global Learning XPRIZE’ ta ware makudan kudade da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan goma sha biyar $15M, don cinma wannan burin. Daya daga cikin daraktocin kungiyar Mr. Matt Keller, yake cewar, wannan kamar abu ne mai wuyar yuwuwa.
Kana shawarar na iya zama kamar hauka, domin kuwa ance yaro ya koyar da kanshi da kanshi, daga amfani da kwamfuta, an dai bama kungiyar kwantirakin fitowa da wata sabuwar manhaja, da yara wadanda basu samu damar zuwa makaranta ba, zasu iya amfani da ita wajen koyar da kansu da kansu.
A kididdigar tsangayar lissafi ta hukumar kula da kayan tarihi na majalisar dinkin duniya UNESCO, ta tabbatar da cewar, akwai kimanin yara sama da milliyyan dari biyu da sittin da uku, a duniya da basa zuwa makaranta.
Hakan yasa suke ganin akwai bukatar samar da wannan manhajar, don a ilmantar da kowa, ya zuwa yanzu dai an samu wasu kamfanoni da zasu gudanar da aikin, yanzu haka ma ana sa ran a watan Nuwamba za’a fara gwajin wannan manhajar.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Wajibi Ne Mata Su Nemi Ilimi Mazan Yanzu Basu Da Tabbas - Inji A'isha Mustapha

Wajibi Ne Mata Su Nemi Ilimi Mazan Yanzu Basu Da Tabbas - Inji A'isha Mustapha
A'isha Mustapha wata matashiya mai sana’ar saida man fetur a gidan mai ta ce tana sana’ar ne domin dogaro da kai tare da tara kudi domin samun damar shiga jami’a.
Ta ce ta kammala makarantar sakandire ne a shekara ta 2013, daga nan ne ta kama aiki kuma tana da burin karantar Mass Communication wato aikin jarida.
Aisha ta ce bata fuskantar wani kalubale domin kuwa tana samun abinda ta ke nema,kuma babban burinta ta sami mijin aure.
Kuma ta kara da cewa aure baya hana karatu, a cewarta ilimi ya zama wajibi domin mazan yanzu basu da tabbas, don hake ne ya zama wajibi mata su zamo masu dogaro da kai.
Tura Zuwa:

Neman Ilimi Baya Hana Sana'a - Inji A'isha Mai Karatun Lauya

Ina zuwa kasuwa domin sana’ar sayar da ganda a lokutan da bana zuwa makaranta ko lokacin da aka tafi yajin aiki a makaranta da zumar zama mai dogaro da kai
Matashiya A’isha Ma’aruf, ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da DandalinVOA, inda ta bayyana tana taimakawa mahifiyarta ne a wsu lokuta inda take zuwa kasuwar ‘yan ganda domin ta saro ganda.
Ta kuma ce tana kaiwa kasuwar sabon gari don sayarwa mata masu abincin gida ko na kasuwa , tana kuma yin sana’ar ne domin dogaro da kai kafin lokacin da zata kammala karatunta na lauya.
Aisha ta ce a halin yanzu basa samun riba sosai sakamakon tsada da gandar ta yi koda shike sukan sami ‘yar karamar riba a gandra rakumi.
Daga karshe ta kara da cewa sana’ar hannu wajibi ce ga diya mace da ma dukkan matasa masu tasowa.

Tura Zuwa:

Matasa A Daina Raina Sana'a Ko Jari - Inji Jamila Ahmad Yakasai

Ya kamata matasa su daina raina sana’a ko jarin da zasu fara sana’a da shi, domin kuwa da ruwan ciki ake jan na rijiya, kuma da kadan-kadan jari yake zama babba, inji wata matsashiya mai sana’ar hijabi da kayan gumama, Malama Jamila Ahmad Yakasai.
Da take zantawa da wakiliyar DandliVoa, Malama Jamila ta ce takan bude dilar gwanjo ta kayan yara a hannu guda kuma tana dinka hijabai na mata da kananan yara duk a yunkurin zama mai dogaro da kai.
Ta kuma kara da cewa duk kuwa da wannan sana’ar ta bata hana mata neman ilimi ba, kuma babu takurawa a harkokinta na gida misali wajen lura da mai gida da ‘ya’yanta.
Daga karshe Jamila, ta ce tana koyawa matasa yadda ake dinka hijabi ba tare da ta karbi ko kabonsu ba.
Tura Zuwa:

Gagarumar Shawara Ga Kowace 'Ya Mace - Inji Hauwa Suleman


Na hakura da aikin banki sakamakon daukar dogon lokaci da aikin yake yi wa ‘ya mace, hakan ne ya tilasta min hakura da wannan fannin inji malama Hauwa Suleman.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, inda ta bukaci matasa mata su maida hankali wajen neman ilimin zamani domin a dama da su kamar yadda zamani ke sauyawa.
Hauwa ta kara da cewa ta so ta karancin aikin jarida amma kamar yadda al’adar makarantu ta ke a Najeriya, ya sa ta sami gurbin karatu a fannin ilimin zamantakewar al’umma wato Sociology.
Kammalawarta ke da wuyu ta sami gurbin aiki a banki, wanda daga bisanai ta samu canjin aiki zuwa aikin gwamnati, ko da yake ta ce bata fuskanci gwagwarmayar rayuwa ba ko a fannin aiki da makamanta haka.
Daga karshe ta ce a lokacin da take karatu bata fuskanci wata matsala ba illa ta zirga-zirga daga gida zuwa makaranta, sai kuma nbangaren aiki inda ta ce takan fita aiki a wancan lokacin daga karfe bakwai na safe sai bakwai na dare wani lokacin ma har a wuce bakwai lamarin da ya tilasta mata hakura da aikin.
Tura Zuwa:

HANYOYIN DA ZA A BI DON RAGE KIBAR JIKI

Hanyoyin da za a bi don rage kibar jiki...
Assalamu alaikum matan gidan nan. A yau na kawo muku wata hanyar da za a bi domin inganta kwalliya. Babbar magana a nan ita ce rage kibar jikinmu, domin kiba ba karamar kara wa mace muni take yi ba. Ko da akwai hanci kibar sai ta shanye hancin. Idan har ana son a yi kyau, idan an yi kwalliya, sai an taimaki kai wajen rage wannan kibar. Ba a rana daya aka hada wannan kibar ba. Don haka sai an yi hakuri da juriya kafin a rage kiba. Ga kadan daga cikin hanyoyin da za a bi domin rage kiba don taimaka wa kwalliyarmu.

·        A dage wajen cin kayan lambu; kamrsu ganye da kabeji da sauransu, domin suna taimakawa wajen rage kibar jiki.
·        Ka da a bar ‘y a’yan itatauwa a baya; yawan shan ‘ya’yan itatuwa kamar su lemu da mangoro da ayaba da kankana da sauransu na taimakawa wajen rage kiba, har ma su inganta fata da kwalliya.
·        A rika shan ruwan lemun tsami da zuma a ruwan dumi idan gari ya waye kafin a ci komai.
·        Ka da a zauna da hada maiko, alhalin ba a motsa jiki, sannan sai a ce ana son rage kiba. Don haka sai a dage da motsa jiki ko da kuwa ‘yar gala-gala ce ake yi za ta taimaka.
·        Akwai wata ‘’yar na’ura ko damarar ‘tummy trimmer’ da mata ke amfani da ita domin rage kibar tumbi; idan an sanya wannan abu za a rage yawan ci, sannan a rage kibar tumbi.
·        Bayan an yi wadannan abubuwan da na lissafo, tabbas idan an yi kwalliya za a y i kyawun gani, a fito fes sosai. Kuma za a ga kowace irin kwalliya aka yi sai a ga an yi kyau tamkar an rage shekaru. An ce dai ‘in ana da kyau sai a hada da wanka.
Tura Zuwa:

YADDA ZA KI YI AMFANI DA FIYA DA MAN ZAITUN WAJEN GYARAN FUSKARKI

YADDA ZA KI YI AMFANI DA FIYA DA MAN ZAITUN WAJEN GYARAN FUSKARKI
YADDA ZA KI YI AMFANI DA FIYA DA MAN ZAITUN WAJEN GYARAN FUSKARKI

Sau da dama mutane sun dauka amfanin fiya shi ne a ci, ba tare da sun fahimci ana amafani da ita wajen gyaran jiki da fuska ba. Dalilin da ya sanya a wannan makon muka taho miki da matakan da za ki bi wajen amfani da fiya da kuma man zaitun wajen gyaran fuskarki ke nan. Kafin mu kai ga bayanin yadda za ki yi amfani da fiya da kuma man zaitun wajen gyaran fuskarki, za mu bayyana miki amfanin fiya ga jikin dan Adam Amfani fiya ga jiki:

·        Fiya tana dauke da sanadarin bitamin A da kuma Glutamine wadanda suke taimakawa wajen kawar da matattun kwayoyin halittar cikin fata.
·        Ana amfani da fiya ga busasshiyar fata don kawo danshin fata. Tana dauke da sinadarai masu yawa wadanda suka hada da bitamin K da C da Copper da Iron da sauransu.
·        Laushin fata: fata takan tsotse man da yake cikin fiya, wanda hakan yakan sanya man ya ratsa kofofin fata, inda fata kuma takan tatse sinadaran da suke dauke a cikin fiya, wannan sai ya sanya fata ta yi laushi da kuma dadin gani
·        Mayar da tsohuwa yarinya: Fiya tana dauke da sinadaran da suke kone kwayoyin cututtukan da suke kodar da fata, wanda hakan sai ya sanya fata ta rika sheki da kuma laushi, har a rika taken ta mayar da ke yarinya.
·        Hasken rana yana dauke da sinadaran da suke kodar da fata ko kuma su sanya saurin tsufa, amma sakamakon sinadarin da fiya take dauke da shi, sai ya zamanto ta kare fata daga haske rana.

Idan kika hada fiya da kuma man zaitun zai sanya fatarki laushi da damshi da kuma sheki. Fiya da man zaitun na amfani ga busasshiyar fata, musamman ma wajen kare fata daga bushewa ko zazzagewa.

Kayan hadi:

1.      Fiya
2.      Man zaitun
3.      Kukumba

Yadda aka hadawa:

Ki samu fiya babba daya, sai ki cire bayan fiyar, daga nan sai ki daka ta, bayan nan sai ki zuba man zaitun, sannan ki gauraya sosai, daga nan sai ki shafa a fuskarki.

Ki samu kukumba, sai ki daka ta, daga nan ki shafa a fuskarki. Za ki bari har tsawon minti 10. Daga nan sai ki wanke fuskarki da ruwa mai dumi, sannan ki yi amfani da tawul mai tsafta wajen goge fuskarki.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive