Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019


Muhammad Abba Gana


Mutane da dama sukanyi tambaya shin da gaske ne an sake Sakamakon Jarabawara NECO Na Shekaran 2019? Kwarai kuwa da gaskene. Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sanarwar cewa ta sake sakamakon jarabawar dalibai na dubu biyu da sha tara (2019) ta kara da cewar kashi saba’in da daya (71%) bisa dari na daliban da suka rubuta sun sami credit a harshen turanci (English) da kuma lissafi (Mathematics).    

Karanta: Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Sake sakamakon jarabawar NECO na shekaran dubu biyu da sha tara labarine mai dadi ga daliban da suke jira domin daurawa a account nasu na JAMB domin samun damar shiga makarantu na jami’a. yanzu mutum na da damar ganin sakamakon sa sannan kuma ya kan iya daurawa a account nasa na siradin duniya wato JAMB kafin su fara raba admission zuwa jami’a na shekaran dubu biyu da sha tara (2019).

Na samu sakonni daga mutane da dama akan cewar shin ta yaya za’a duba sakamakon jarabawar NECO ta hanyar amfani da katin gogewa (Scratch card) ko kuma ta hanyar amfani da numbobin sirri (Pin) wasu kuma sukanyi korafin cewar basu ga shekaran dubu biyu da sha tara (2019) a babban shafinta ba. A hakikanin gaskiya Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta chanza shafinta na duba sakamakon jarabawa haka zalika ta sauya mata kan duba sakamako. A yanzu Token (Numbobi Masu Zamar Kansu) ya maye gurbin shi Katin Gogewa (Scratch Card) da kuma Numbobin Sirri (Pin) bisa wasu dalilai.

Karanta: YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Yadda Za’a Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Mutum yana bukatan ya siya Numbobi Masu Zamar Kansu (Token) kafin ya samu damar duba sakamakonsa a yanar gizo na shekaran dubu biyu da sha tara (2019). Za’a iya karanta cikken bayani yadda ake siyan NumbobiMasu Zamar Kansu (Token) a nan. Bayan mutum ya bude account a shafin NECO sannan kuma ya siya Numbobi Masu Zamar Kansu wato (Token) nasa kamar yadda na zayyano ba tare da karya daya daga cikin dokokin su ba.

Matakan Da Ake Bi Wajen Duba Sakamakon Jarabawar Neco


Mataki Na Farko: Za’a ziyarchi babban shafin NECO wato https://result.neco.gov.ng/.

Mataki Na Biyu: Sannan za’a zabi shekaran jarabawa Misali: 2019.

Mataki Na Uku: Za’a zabi wani irin jarabawane Misali: SSCE Internal (JUN/JUL).

Mataki Na Hudu: Za’a saka “Registration Number” da kuma Numbobi Masu Zamar Kansu wato (Token) da aka siya a dai dai inda aka bukaci hakan.

Mataki Na Biyar (Karshe): Sai a latsa madannin “CHECK RESULT”  
Muddin anbi matakan dana zayyano daidai a baya mutum zaiga sakamakon jarabawarsa wula-wula na ko wani subject daya rubuta.

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019


Yadda Ake Fitar Da (Printing) Sakamakon Jarabawar NECO


Domin fitar da (Printing) sakamokon jarabawar NECO na shekaran Dubu Biyu Da Sha Tara (2019) dole sai mutum ya duba sakamakon sa da fari kamar yadda nayi jawabi a baya. Bayan mutum ya bude sakamakonsa a shafin NECO zai ga tambari na alamar firinta (Print Icon), sai a latsa kai ko kuma ta hanyar amfani da CTRL + P a kwanfuta.    

Shugaban Hukumar shirya jarabawar NECO na kasa Mal. Abubukar Gana yace cikin dalibai 1,151,016 da suka rubuta Jarawa a shekaran dubu biyu da sha tara (2019). dalibai 829,787 ne kadai suka samu nasarar samun credit a harshen turanci (English) da kuma lissafi (Mathematics) wadda dole ne sai mutum ya samu kafin ya fara shun shunan jami’a.

Karanta: Yanda Ake bude blog cikin sauki


Ya kara da cewar dalibai 40,630 ne suka tsinci kansu cikin haramcecciyar dabi’a ta hanyar yin sata a cikin Jarabawa wadda adadin ya ninka na shekaran data gabata wato shekaran dubu biyu da sha takwas (2018).

Shin ana fuskantan wani kalubale yayin duba sakamakon jarabawan NECO na shekaran dubu biyu da sha tara (2019)? za’a iya tuntubanmu kai tsaye ko kuma kamfanin Be With Me Technology domin samun taimakon agajin gaggawa a ko wani lokaci.           
Share:

Wasu Daga Cikin Amfanonin Zogale Ga Lafiyar Jiki

Wasu Daga Cikin Amfanonin Zogale Ga Lafiyar Jiki

Muhammad Abba Gana


Wasu lokutan mukan ci wasu abubuwa saboda marmari, ra’ayi, dadi ko kuma kwadayi ba tare da sanin wani irin amfani zai kawo mana ga lafiyar jiki ba ko kuma illa ba. Wasu abinci ko kayan marmari na dauke da kwayoyi da dama da ke taimakawa lafiyar jiki wajen ginata wasun kuma suna dauke da kwayoyin sinadari wadda zai iya taimakawa wajen kawo wa lafiyar jikin illa. Bisa la’akari da mujallar Dunyan Fasaha tayi, yau zamu tattaunane game da amfani zogale ga lafiyar jiki.

Karanta: Cikkanen Bayani Game Da Amfanin gurji a fatan Dan Adam


Zogale wadda aka fi sani da Moringa a turance ya kasance wani ganye ne dake dauke da sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam wadanda lafiyar jiki ke bukatarsu sosai wajen bukansa su…

Masana kimiyya sunyi nasarar bincike inda suka tabbatar da cewa ganyen zogale yana maganin sama da cututtuka dari uku (300). Daga cikin manyan cututtuka da yake magani sun hada da  manyan cututtuka irinsu ciwon hawan jini, ciwon sugar, cancer, gami da kashe tsutsotsin ciki da makaman cin haka..

Karanta: Amfanin Cin Namijin Goro


Manyan Masanan na duniya sun bada shawarar a rinka amfani da zogalen ta hanyar shanya shi ya bushe (amma fa ba acikin rana ba) sannan sai a daka shi a rinka shanshi a cikin ruwan tea (shayi) ko kuma a zuba shi a ruwa zafi haka zalika ba lallai sai abu mai zafi ba za’a iya sawa ko a cikin ruwan sanyi ne a sha amma lallai mutum ya tabbatar cewa zai iya sha kafin ya gwada domin ba lallai ne dadin ya masa yadda yake so ba ko kuma dadin yayi kamar miyar ba domain shi miya ana hadashi da wasu sinadaran duniyan masu sasa dandano, armashi da kuma kanshi. Wasu manyan magungunan da yakeyi a jikin dan adam sun hada da:
 • Yana maganin cutar zuciya da kwakwalwa
 • Yana taimakawa wajen lafar da wasu matakai da ke kaiwa ga haddasa bugun zuciya da kuma ciwon sugar.
 • Zogale na dauke da sinadarai da ke gyara fatar jikin mutuum cikin sauki.
 • Yana taimakawa wajen magance hatsarin kamuwa da ciwon cancer.
 • Zogale na kare mutum daga cututtuka da ke hana numfashi da kyau idan aka sa mu kumburi a huhu.
 • Yana dauke da Vitamin A, wanda kowa yasan amfanin vitamin A wajen kara lafiyar Ido da kuma kaifin Ido.
 • Zogale na maganin cutar nan ta Diabetes ta hanyar rage yawan sukarin jikin mutum. Idan har ana daka ganyen ana sha.
 • Zogale yakan taimaka wajen sarrafa abincin da mutum yaci cikin yan kankanin lokaci.
 • Akwai sinadarai da dama a jikin fure da ganyen Zogale sa gyara kare hanta.
 • Yana dauke da sinarin calcium wanda sinadari ne mai amfani sosai wajen kara kwarin kashi a manya, sannan kuma yana taimakawa yara wajen karin kwarin hakora.
 • Zogale na dauke da bitamin irin su E da C da suke taimakawa wajen gyara kwakwalwa su kuma kare cututtuka.  
 • Duk da cewar tsaro da kuma kariya daga Allah ne zogale yana taimakawa wajen tafiyar da al’amuran tsaro ko kuma kariya na jikin dan adam daga wasu cututtukan zamani.
 • Binciken da masana sukayi ya tabbatar da cewar shan ruwan zogale yana dakyau ga mata masu shayarwa, domin yana kara kaurin ruwan nono sannan kuma yana cika nonuwa. 
Wasu 13 kenan daga cikin abubuwan da shi ganyen zogale keyi ga lafiyar dan adam. Kammar yadda na fadi a fari zogale yana taimakawa lafiyar jiki sama da hanyoyi dari uku (300) amma wayannan sune manya daga cikinsu. Yana da kyau a kara adadin cin zogale domain taimakawa lafiyar jiki.

Karanta: Abinci Kala 6 Da Ke Tsayar Da Gudawa Cikin kankanin Lokaci


Shin akwai wata hanya da akeji zogale ke taimakawa sosai wadda basu kawo a cikin wannan kasidar ba za’a iya turo mana ta hanyar tuntubanmu ko kuma ta hanyar ajiye comment a kasan wannan post din. 
Share:

Illar Sanya Mahajar (Application) Launcher Akan Wayar Salula

Illar Sanya Mahajar (Application) Launcher Akan Wayar Salula


Lokaci zuwa lokaci mukanyi ababe da dama, a ranmu mukan ji daidai ne wadda kuma a hakikanin gaskiya ba daidai bane wasu lokacin son raine wasu lokutan kuma rashin sani ne. A mafi yawancin lokutan mukan biyewa ra’ayinmu ne ko kuma ita zuciyarmu wadda hakan kan zama mana matsala a nan gaba ko kuma ta sanya mu cikin kunchi da la haula.

A zamanin da muka tsinci kanmu a yanzu na Fasaha, mutane da dama musamman masu amfani da wayar taba ka latsa wadda aka fi sani da android a turance, za ka same su suna amfani da wata mahajar waya (Application) da ake kira da Launcher a turance.

Karanta: Waya na nuna alamar shigowar kira amma baya nuna wajen daukawa – Yadda za’a magance matsalar cikin sauki


Shi Wannan mahajar wadda aka fi sani da application a turance ana amfani ne da shi domin kayata cikin fuskar waya da kuma canza masa wasu daga cikin siffofin ko kuma sura da take fitowa da su misali: yanayin yadda hoton saman screen din wayar yake, kallar rubutu, surar mahajar waya, launi da dai sauransu.

Duk da cewar wadannan mahajar (applications) suna da amfani ta wani bangaren misali wajen kayata waya, akwai wasu illoli da dama tattare da shi wadda ke taba lafiyar waya irin su uwar wato kwakwalwa, wadda kuma ba kowa ne yasan da wadannan illolin ba wasu kuma sun sani amma saboda biyewa ra’ayi zuci suna kan amfani dashi.

A cikin wannan kasidar namu insha Allahu yau Duniyan Fasaha bisa la’akari da tayi zamu kai hangene ne izuwa ga illolin shi Launcher da kuma yadda yake taba lafiyar waya ta hanyar nuna wasu alamomi.

   1. Kwayar Cutar Na’ura (VIRUS): Sanin kowa ne akwai masu kawo barna a bangaren fasaha wadda aka fi sani da hackers a turanche wadanda kullum burinsu shine suga sun lalata abubuwan mutane ta hanyar yada virus cikin fasaha wacce zata ita haddasa matsala ga kwamfutoci, ATM, wayoyin salula, memory da dai sauran abubuwan fasaha na zamani.

     Karanta: Dalilin da ke sa waya taqi cika da wuri wajen charge ko kuma ta sauka da wuri


Sukanyi Nazari sosai sannan su zayyano abubuwan da mutane suka fi shagala akai ta hanyar yin download dinsa, sai su dauki manyan daga ciki sannan sai su gurbata shi da virus ko kuma trojan ta yadda duk wadda yayi download wannan abun ko kuma aka tura masa to shikenan wayarsa ko kwanfutarsa ta auri matsala wato wannan virus din. Sannin kowa ne akwai illoli da dama tattare da ita virus wadda ke haddsawa kama daga lalata wayar salula, chanza tunanin wayar salula, sanya masa muga yen dabi’u da makamantansu.

  2. Talla (Adverts): Duk sa’an da mutum ya saukar da wannan mahajar (application) ko kuma aka tura masa idan yazo da rashin sa’a mutum zai fahimci cewar daga lokaci zuwa lokaci akwai wasu talla da waya zai ringa nunawa mutum ya rasa ta ina wayannan abubuwan sukazo, a mafi yawancin lokutan yakan iya dakatar da mutum daga wasu ayyuka da yake son yi wanda hakan ya faru ne bisa dalilin saukar da wannan mahajar (application) yakan dauki lokaci mai tsaho kafin mutum ya magance wannan matsalar.

  3. Shan Chaji (Consuming Battery Life): Da yawa daga cikin mahajar (Application) launcher suna zuwa da nauyin tsiya wadda hakan yakan dauki lokaci kafin ya fara aiki dai dai, haka zalika idan ya fara aiki yana yi a kowani lokaci a kwakwalwar waya wadda aka fi sani da Running in Background a turance wadda hakan na bukatan wuta wajen gudanar dashi. Hakan ke sanyashi amfani da battery din waya ba tare da neman izinin mai shi ba.       

Wasu lokutan za’a ga cewar wayar na daukan zafi, duk da cewar akwai masu abubuwa dake sa waya zafi amma wannan na daya daga cikin manyan ababen dake sa ita wayar zafi sabili da yana aiki tukura a kan waya ba tare da numfasawa ba.

Karanta: YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID


    4. Tsayawa lokaci Zuwa Lokaci (Hooking): A duk lokacin da mutum ya dora mahajar Launcher sannan kuma nauyinsa ya kasance sama da wadda wayar salula ke zuwa dashi ko yazo dashi za’a ga alamar cewa a duk lokacin da mutum ya danna madannin home (na tsakiyar wayarka wanda ake minimizing da shi) za’a lura da cewar ya nuno duk wasu launchers din da ke cikin wayar sun fito domin mutum ya zabi wacce yake bukata.

A nan abin da ke faruwa shine, wayar zata rasa wane salo zata yi amfani dashi, domin ko wace mahajar launcher akwai yanayin yadda aka tsara shi. Wannan kan iya jaza wayar ta rikice ko kuma ta rasa ma hankalin gaba daya, sanadiyyar hakan sai ka ga waya tayi hooking, ma’ana ta tsaya cak, ta ki gaba ta ki komawa baya har zuwa wani lokaci.

Wani lokacin ma wayar ta kan dauke ne baki daya sai kuma ta kunna kanta ko kuma wasu lokutan sai an kunnata. Idan mutum nasa yazo da rashin sa’a zai tsaya ne chak sai mutuum ya cire battery ya kuma dawor da ita. Wannan kan iya sanya wani banagare na wayar ya sami babbar matsala bisa mutuwa ba tare da ka’ida ba.

Dukkan wayannan illoli guda hudu da mukayi jawabi akansu na tattare da amfani da mahajar Launcher wadda wasu lokutan kan iya  kawo babbar matsala ga lafiyar wayar salula, wadda hakan yakan iya kamawa lallai sai anyi wa wayar flashing domin komawa hayacinsa.

Karanta: Madannai uku na wayarka Android sun daina aiki? Ga cikakken bayani yanda zakayi aiki ba tare dasu ba


Babban Shawara anan shine, idan lallai ana bukatar yin amfani da mahajar Launcher, to a tabbatar da cewar bata wuce guda daya ba a cikin wayar salula, domin tara mahajar lauchers kamar kasuwan kifi a waya guda ba abin ado bane face ya janyowa mutum matsala babba. Idan kuma mutum ya kasance kamar kawu nane mai taran aradu da kai to babu shakka zai iya saka adadin son ransa.  Domin tabbatar da cewar Launcher bata dauke da Virus, ayi downloading dinsa kai tsaye daga Google Play Store.
Share:

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa ta fitar da sabon sanarwar cewa ta bude sabon shafinta wadda zai taimaka wa dalibai na kasa baki daya wajen duba sakamakonsu na karshen zango. Wannan sabon shafin ya sha babban da wadda ya gabata, a shekarun baya idan mutum yana bukatan yaga sakamakonsa na jarabawar NECO to fa dole lallai sai ya siya katin gogewa wadda aka fi sani da scratch card a turanche.   

Karanta: YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB NA SHEKARAN DUBU BIYU DA SHA TARA 2019


Amma da sabon shafin nan abinda mutum ke bukata shine token, token ya maye gurbin katin goggewa (scratch card) da kuma numbobin sirri (Pin). Hukumar ta kara da cewar tayi hakan ne domin kara inganci sannan kuma da sawwake wa dalibai wajen duba sakamakon su. Kama daga yanzu www.neco.gov.ng shine babban shafin hukumar shirya jarabawar neco sannan duk sakamakon jarabawa za’a iya samu a cikin shafin ta na kowani shekara.

Karanta: Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki


Kama daga yanzu za’a iya ganin sakamakon jarabawar NECO ta hanyar siyar token wadda za’a iya samu daga shafinta sannan kuma za’a iya rabawa dalibai, makarantu, ko kuma kamfanoni wayanda suke da niyar ganin sakamakon jarabawar dalibai.

Yadda Ake Siyan Token A Yanar Gizo


Matakin Farko: Mutum zai ziyarci shafin hukumar shirya jarabawar NECO ko kuma ta hanyar danna wannan addreshin https://result.neco.gov.ng/register

Mataki Na Biyu: Mutum zai saka cikakken sunan sa a shafi na farko, sannan number wayarsa a shafi na biyu, sai kuma email addreshin sa an uku, sai mutum ya zabi numbobin sirri da yake son sawa sannan ya maimaita a shafi na karshe. Bayan mutum ya tabbatar da abinda yasa daidaine kuma zai iya tunawa sai ya latsa madannin “Register”

Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Mataki Na Uku: Hukumar NECO zata turawa mutum sako a addreshinsa na email da yayi amfani dashi yayin rajister.  

Mataki Na Hudu: Mutum zai bude sakon sannan ya danna mabulin “Verify” domin jaddadawa.

Mataki Na Biyar: Mutum zai ziyarchi shafin NECO wajen shiga ko kuma ta hanyar latsa nan https://result.neco.gov.ng/login

Mataki Na Shida: Mutum zai saka email addreshinsa ko kuma numbern wayarsa a shafi na farko sannan kuma ya sanya numbobin sirrinsa daya zaba yayin rajister a shafi na biyu sannan ya latsa mabullin “Login”

Karanta: Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


Yadda Ake Siyan Token Domin Duba Sakamakon Jarabawar NECO


Mataki Na Bakwai: Mutum zai nema inda aka rubuta “Purchase Token” sannan ya latsa kai yin haka zai bawa mutum damar wucewa zuwa gaba. Abin Kula: za’a iya amfani da ko wani token a kan sakamako guda daya kacal sannan duk wani token akwai wasu adadi na amfani dashi.

Karanta: Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?


Mataki Na Takwas: Mutum zai zabi a dadin da yake son siya sannan ya danna mabullin “Pay Now” Abin kula: ko wani token guda naira dari biyar ne da kuma kudin sabis naira (50) wadda ya kama naira dari biyar da hamsin kenan (550).

Mataki Na tara (karshe): Mutum zai latsa ma bullin “Pay” domin biya ta dandalin Remita ta hanyar amfani da banki ko kuma katin banki.

Karanta: Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito


Wannan shine cikakken bayani ta yadda ake siyan token domin duba sakamakon jarabawar NECO ta hanyar amfani da sabon shafinsu. Shin ana fuskantan wani kalubale yayin siyan token na NECO? za’a iya tuntubanmu kai tsaye ko kuma kamfanin Be With Me Technology domin samun taimakon agajin gaggawa a ko wani lokaci.           


Karanta: Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar NECO Na Shekaran 2019

Share:

MIYAR ZOGALE

MIYAR ZOGALE 
Kamar yadda mukayi bayani a baya zogale na taimakawa lafiyar jiki matuka ta hanyoyi daban daban ta hanyar shan sa ko kuma ta hanyar cin miyarsa. Insha Allahu yau kuma Duniyan Fasaha ta kawo muku bayani ne akan yadda ke tsara miyan zogale cikin sauki wadda zai so sa kunne mai gida sannan kuma ya sa yara santi. A sha karatu lafiya.

Karanta: Yadda ake jus din gurji mai zobo


Abubuwan Da Ake Bukata


 • Tattasai
 • Attarugu
 • Albasa
 • Zogale
 • Maggie
 • Gishiri
 • Garlic thyme
 • Seasoning spices
 • Nama
 • Kifi busashshe
 • Man ja or man gyada
 • Gyada


Yadda Za’a Hada Miyar Zogale


Da fari zaki tafasa nama ki sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa saiki sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman.

Karanta: Yadda ake masa


Saiki zuba gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar mintuna goma (10) saiki zuba zogalen ki bayan kin gyarashi.

Abinda ya Gabata: Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’


Anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi a kalla kamar mintuna sha biyar (15) shikenan saiki sauke. Miyarki yayi dai dai kuma a shirye yake wajen ci.
Share:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *