Akwai jerin wasu mata da ke ganin saka takalma masu tsini yana daga cikin ado musamman ga ya mace ba tare da sannin illoli dake tattare dashi ba.
Da akwai kuma jerin wasu mataye da ke ikirarin cewar duk ya mace da ba ta saka takalma masu tsini to fa lallai wannan yar bata cika goma ba.
Masana kimiya a fadin duniya sun dade suna gargadin iyayenmu mata game da manya manyan illolin da sanya takalma masu tsini ke haifarwa ga lafiya musamman kasusuwan jikin su da kuma jijiyoyi, amma da ya ke abu ne da ya jibanci gayu, sau dayawa sai dai a yi watsi da shi a cigaba da aiwatarwa.
Akwai wani bincike da aka gudanar shekaru da suka gabata a jami’ar Havard da ke kasar Amurka ya nuna cewar kari a tsahon takalmi ko da da inci biyu ne yana kara yiwuwar kamuwa da cututtukan kashi da kaso ashirin da uku (23) cikin dari da ake dasu a fadin duniya.
Haka zalika wani likita a asibitin Makurdi da ke jahar Benue anan kasa Nigeria, Dakta Martins Adejo ya shiga sahun likitoci masu gargadin, inda yace sanya takalma masu tsini na lahanta kashin bayan mutum da kuma jijiyoyi da suke taimakwa ita baya.
Ya kara da cewa takalma masu tsini na kawo matsala a gwiwowi da gabobi da tan kafa, sannan kuma yana raunata jijiyoyin da ke tayar da jini a jikin dan adam. Ba nan kadai ba yakan kuma iya ratsa wasu bangarori na jikin bil adam.
Lilkitan ya kuma ce, ba a fuskantar wadannan illoli yawanci sai a lokacin da tsufa ya zo wa mutum, al’amarin da ke hassasa yiwuwar kamuwa da cutar hawan jini da ciwon siga, ciwon baya da dai makamantansu.
No comments:
Post a Comment