Jus don sanyaya rai a lokacin zafi
|
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa damu
a wannan filin namu na girke-girke uwargida wanda yake zuwa muku kai tsaye daga
mujallar Duniyan Fasaha. A yau na kawo muku jus din markadaddun ’ya’yan itace
ne don sanyaya ran maigida domin zafin da aka shiga na kwanan nan. Abubuwan da
za ki bukata ba ma su yawa ba ne. Ga arha, ga kuma biyan bukata.
Abubuwan
da za a bukata
·
Abarba
·
Lemun zaki
·
Gwaiba
·
Flaba
(wasu na kiransa da felebo)
·
Kanka na
·
Blanda
(nau’ra na markada yayan itatuwa)
·
Abin matse
lemu (orange skueeze/press)
Hadi
Idan uwargida ta sayo abubuwan da na lissafo
za ta ga lallai ba wani abu mai tsada ba ne duka bai fi ta kashe Naira 300 ba.
Ta bare abarba da gwaba da kuma kankana ta ajiyesu a gefe. Sannan sai ta samo
lemun zakinta ta yanka shi rabi da wuka kamin ta daura a abin matse lemun zaki
(orange press) idan ta samu ruwan lemu da dan dama, sai ta zuba ruwan a cikin
blanda da yankakkiyar abarba da kwaba da kuma kankana duk a cikin blanda sai ta
markadasu. Uwargida ba dole sai kinyi amfani da kayan zamani ba in har kina da
wata dabara ta yanda zaki iya markadawa ba tare da yayi yaji ba ko matse ruwan
lemun ba tare da wani dauda ba zaki iya yi.
Bayan ki markada, sai ki tace sannan ki zuba
flaba, domin dada wa jus din kamshi. Idan uwargida mai son sukari ce, sai ta
zuba siga. Amma babu sukari ya fi dadi. Sai a sanya a firiji domin ya yi sanyi
kafin a zuba wa maigida a kofin gilashi domin sanyaya masa zuciya!
No comments:
Post a Comment