Home »
kwanfuta
» YADDA AKE DAWO DA KAYAN MEMORY KO FLASH BAYAN AN GOGE SU TA HANYAR AMFANI DA KWANFUTA
YADDA AKE DAWO DA KAYAN MEMORY KO FLASH BAYAN AN GOGE SU TA HANYAR AMFANI DA KWANFUTA
Assalamu Alaikum barkan mu da war haka barkanmu da sake saduwa a cikin sabon shirinmu, insha Allah yau zamu amsa Daya daga cikin manyan tambayoyin da jama’a suke yi a kowane lokaci shi ne ya mutum zai yi a lokacin da ya rasa kayan da ya ajiye a cikin memory SD Card na wayarsa Pen drive wato flash disk ko kuma disk, a sanadiyar kankare memory wato formatting)ko kuma an goge abin da ke ciki deleting bisa kuskure. Amma kafin in fadi yadda ake yin wannan aiki ko kuma abubuwanda da ake amfani dasu wato software a turance da ake bukata yana da kyau in sanar da jama’a yadda shi wannan memory yake da kuma yadda ake lura da shi. Memory yana daya daga cikin mazubi ne da aka yi shi domin ya ba mutum damar ya iya yin ajiyar kayan da aka yi su da wutar lantarki wato electronic data wanda ya hada da hotuna masu motsi wato videos da rubutu da surkulle da duk wani abu da ake iya adana shi a cikin kwanfuta. Wadannan memory koh flash yana da yanayi mabanbanta dangane da yadda ake yin sa da kuma tsarin yin sa, sai dai mafi shahara shine wanda ake yin amfani da shi a mafi yawan wayoyin tafi da gidanka na zamani wato android ko kuma smartphones. A baya, mafi yawan kanfanonin da suke kirkirar wayoyin hannu ko kamara kowa na yin irin nasa memory dinne, dangane da girma ko fadin sa, wanda ya sanya akwai matsala sosai yadda memorin wani kamfani baya aiki a wata na’ura da ba tasa ba. Amma bayan da waya kirar Android ta samu karbuwa sosai a fadin duniya sai ya zama na sun sami hadin kai wurin tabbatar da mazubin memory ya zama yana da rami iri daya wanda zai zama kowace waya ko tablet zata iya amfani da su. A baya wannan memory ya na da tsada matuka, ga shi kuma yana da wahalar samuwa a kasashen mu na africa, ga shi kuma ba shi da girman wurin kwasan bayanai, amma Alhamudu Lillahi a yanzu wannan ta kau domin ana samu memory wanda a kalla yana iya daukar Gig dubu shi daya. Daga cikin abin da yake damun jama’a da yawa shi ne yawan lalacewarsa mara dalili da kuma rashin sa’a wurin gogewar abin da ke cikin sa. Mutane sau da dama suna manta cewar Memory card shima kirkirannen kayan kwamfuta ne, kuma yana iya lalacewa kowani sa’i, musamman idan aka yi rashin sa’a wanda yake rike da shi bai iya lura da shi sosai ba. Wasu lokutan ba wai memorin ya lalace ba ne, a’a an sami matsala ne ta hanyar sanyashi.
Misali zai iya yuwa ka sami wayar da take daukar memory da yake da tsarin ajiyar bayanai na FAT wanda yake nufin File Allocated Table a turance to idan ka saka shi a cikin wata wayar da kwakwalwarta baya daukar wannan tsarin sai ka ji ta fada maka cewar wannan memorin yayi samu matsala, yayi dameji ko kuma yana bukatan formating. Ko kuma wani lokaci zaka ga duk abin da ke cikn memorin ya ki budewa ko kuma ya nuna alamar lalacewa wanda wannan shima ba yana nuna maka cewar memorin ya daina aiki ba ne ko kuma kayan cikinsa sun lalace gaba daya bane. Shima wannan yana da danganta ne da irin File Sysmem din da aka ajiye kayan tun farko. Wasu lokutan kuma zaka ga ka dauko kaya daga cikin kwamfuta ko wata wayar salula amma da zarar ka tashi budewa sai ka ji ya na fada maka cewar Unsupported format wato bai gane ba, wannan shima ba yana nufin cewar memorin ya lalace ba ne yana maganar cewar wayar bata da application din da zai iya budewa. To duk wadannan ba abin da za mu yi Magana ba ne a kai yau. Muna son muyi magana ne ga mutum da cikin rashin sani ko ma ganganci ya goge abu da ke cikin memory na wayarsa ko flash sai kuma bukatansa ya dawo yana son ya sake dawo da wannan kayan saboda yayi amfani dashi. A tsari irin na bature na tunaninsa da kuma yadda yayi kayan ajiya na kwamfuta wato storage devices aturance yana da kyau jama’a mu san da cewar duk abin da ya taba shiga cikin memory na kwamfuta ko waya ko flash har abada yana nan a cikinsa, koda kuma an goge shi ko an yi formatin lallai yana nan daram, kuma za a iya dawo da shi san da ake bukatansa. Sai dai inda gizo ke saka shi ne dame ya kamata in yi amfani wurin dawo da wadannan kayan nawan?? Akwai hanyoyi mabanbanta da jama’a suke yin amfani da su wurin dawo da kayan da suke cikin memory koh flash bayan an goge, kadan daga ciki shine ta yin amfani da shafukan intanet domin samun biyan bukata. Sai dai a nawa shawarar ban cika son jama’a suna yin amfani da wasu shafukan intanet wurin irin wannan aiki ba, kasancewar mafi yawan irin wadannan shafuka na yanzu yawancinsu yan yaudara ne da zamba da kuma zubawa mutane miyagun virus cikin wayarka ko kuma kwamfutar ka ba tare da ka ko kin sani ba. Amma akwai na kirki sai dai mafi yawansu sai ka biya kudi kafin ka samu naka. A wannan karatun zan nuna mana wadansu manhajojin wato softwares a turance na kwamfuta mai kyauta kuma garanti ga duk wanda yake son yayi amfani da su wurin dawo da kayan da suka bace a memorinsa ko ya gogesu ta hanyar rashin sani ko kuma san ransa. Idan memori yana cikin waya ne ko kuma cikin kamara kuma idan ka hada shi da kwamfuta baya nuna memorin to yana da kyau ka ciro memorin daga cikin inda ya ke da zama ka saka shi a cikin Card Reader domin fara yin wannan aiki. Abin kiyayewa shi ne, tunda da kwamfuta zaka yi wannan gyara to ka sani mafi yawan kwamfutar da muke amfani da ita a wannan kasa ta mu ta Africa kashi 60 suna dauke da virus mai cinye kayan kwanfuta na mayar da su shortcut, to, amfani da irin wannan kwamfutar akwai hatsari, saboda haka ka sami kwamfutar da ka san tana da anti-virus mai kyau kuma mai karfi, kuma ana updating dinsa kafin ka zura shi. Wani hanzari ba gudu ba, idan kasan akwai wadansu kaya a cikin memori din to yana da kyau ka kwashe su ka zuba su a cikin wani folder a kwanfutanka domin kada garin so ka dawo da baya ya zamana suma su zama da suna iri daya da wannan sai ya daura a kansa. Wadannan dai sune kadan daga cikin abin da zan iya jan hankali a kai kafin in nuna mana software da zamuyi aiki dashi. Amfani da wadannan applications koh softwares ba wani wahala suke da su ba wajen aiki, da farko dai dukkansu kyauta ne kuma suna yin aiki sai kamar yadda ya kamata duk da de ba wai zan fadi mataki bayan mataki bin kowane daya daga cikin su ba ne, sai dai zan fadi shi application koh software din da kuma amfanin sa wanda bazan tsawai taba.
1- Pandora Recovery wani application ne dake aiki a Windows ne kawai Pandora Recovery shi ma yana aiki mai kyauta wajen dawor da kayan da aka goge yana da girman 3.12MB, yana aiki a kwamfutar da aka sa mata Windows kuma wacce Operating System dinta ya fara da Windows XP zuwa sama. Shima yana aiki. wato za a ciro memorin a saka a cikin Card Reader sai a saka a cikin kwamfutar da aka yi Installing software Pandora Recovery. Sannan sai a zabi kodai yayi Quick Scan ko Deep Scan. Shi na Quick Scan ga wanda ya ke son ya dawo da abubuwan yayi deleting ne amma wanda yake son ya dawo da wadanda aka yi formatting shi zai amfani da Deep Scan banbancin shine shi quick scan yana yine cikin yan kankanin lokaci kuma shi duba wanda aka goge yakeyi amma shi deep scan yana tono wayanda aka goge da su wayanda akayi formatting din. Bayan ya gama scanning za ka iya zaba tsakanin kodai ka yi amfani da Pandora Recovery Wizard sai ka yi amfani da sharudda da zai rika fitowa kana zaba har ka gama, ko kuma ka yi
right click ka zabi abin da kake son ka dawo da su daga cikin sauran.
2- Recuva yana daya daga cikin kwararrun kuma wanda aka yarda dasu wajen dawor da kayan da aka goge shi Recuva Na aiki a Windows ne kawai Wannan application na Recuva (version 1.5) nauyin sa 4.02MB ne kuma kyauta ne ake samunsa, yana aiki a kwamfutar da take da operating system na Windows ana kuma iya saka shi a Windows 2000 zuwa sama. Idan kana son ka dawo da kayanka din ka dake cikin memory din ka. Zaka saka memorin a cikin Card Reader sannan ka zura shi a cikin kwamfutar da ka yi installing wannan application na Recuva din, sai ka tashe shi (recuva) sai ka zabi shi memori din a cikin jerin manyan kwakwalen da suke jikin kwamfutar. Sannan sai ka taba maballin Scan ma’anar sa duba. Zaka bashi yan lokaci don zai dawo da kayan da aka goge a cikin sannan zai baka maballin da aka rubuta Recover sai ka taba shi domin ya dawo maka da wanda kake so bayan k agama zabansu.
3- PhotoRec yana daya daga cikin kwararrun kuma wanda aka yarda dasu wajen dawor da kayan da aka goge cikin sauki shi Na aiki da DOS, Windows 9x zuwa Sama, Linux da OS X) Shi wannan manhajar ta PhotRec na kyata ne kuma hadin gwaiwar masana ne suka kirkire shi, shi yasa yake aiki a cikin kowace kwamfuta. Yana da girman 9.4MB. Yana zuwa tare da shi wannan PhotoRec wani application a cikinsa mai suna TestDisk wanda shi wannna TestDisk yana dawo da partition din da aka yi deleting. Shi yana bukatar kafin ka fara amfani da shi ka zabi wani tarin file ne memorin ya ke da shi misali ko FAT ko NTFS, sannan ka zabi shi memory din sannan ka ce yayi binciken wato Scan. Bayan ya gama dawo dasu wato recovery a turance din sai ka zabi wurin da kake son a jiye kayan da ya dawo maka.
4- Stellar Phoenix Mac Photo Recovery yana daga cikin kwararrun kuma wanda aka yarda dasu wajen dawor da kayan da aka goge sh yana Na aiki ne da OS X ne kawai Shi Stellar Phoenix Mac Photo Recovery (version 6.0) girman shi 13MB ne, kuma yana aiki ne a kwamfutar da take da Operating System na OS X 10.5 ko sama da haka. Ana bukatar wanda zai yi amfani da wannan softwares da ya yi amfani da Card Reader shi ma, sannan ya kunna wannan application. Za ka iya yin amfani da wannan manhajar domin dawo da hotuna ko bidiyo ko sauti ta hanyar zabar me kake ya dawo maka. Idan ka zaba sai cewa software ta yi bincike wato sanning ta hanyar taba Scan Now ko kuma latsa Advanced Scan domin yin bincike mai zurfi. Mutum zai iya zabar kayan da ya ke son ya dawo masa da su musamman wadanda deleting dinsu aka yi deleting dinsu, amma ga wanda yake son ya dawo da kayan da formating dinsu aka yi sai idan ya biya su kudi. Wannan software yanzu akwai irinta ga wanda ya ke da kwamfutar da take da manhajar Windows.
Wannan sune kadan daga cikin application da zan kawo muku wanda zasu taimaka maku wurin dawo da kayan da kuka goge ko kuma kuka rasa sakamakon an yi formating Memory.
YAYA ZANYI NA SAMU WAYAN NAN SOFTWARES DIN
Zaka samu wayan nan applications din ko softwares da nayi bayani a kansu ta hanyar searching a google sannan ka saukar dasu ana samun su kayuta ne ba tare da ka biya sisi ba.
mawallafi: Muhammad Abba Gana
Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.
Howdy! This is kind of off topic but I need some guidance from an established blog.
ReplyDeleteIs it very difficult to set up your own blog?
I'm not very techincal but I can figure things out pretty fast.
I'm thinking about making my own but I'm not sure where
to start. Do you have any ideas or suggestions?
With thanks
yes of course there are lot of problem and challenges you will face when managing a BLOG BUT ANY WAY CREATING IT IS NOT SO HARD as you think if you are ready you can simply contact me and i will help you out insha Allah
Delete